UKU-BALA'I 40

UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA ARBA'IN.
Sosai take kai kawo cikin dakin gabadaya ta kasa zaune ta kasa tsaye tunda Dr.Karami ya zo ya ajje ta a kofar gida ya juya ya tafi ba tare da ya dubeta ba balle yace da ita k'ala hakan ba karamin taba mata zuciya yayi ba duk da tana jin wani iri a game dashi na bacin rai duk da ta san dai fushin da take yi dashi ba ta san ya yake ba amma ta tabbata halin ko in kula da ya nuna mata a yau yayi matukar sanyata cikin wani irin yanayi na tashin hankali mai girman gaske sosai take jin zuciyarta da ruhinta suna faman kai kawo dauke da lamari mai matukar girma na tashin hankali.
Hannayenta ta daura bisa goshinta tana dafewa gabadaya take jin duniyar na sauyawa a gareta gabadaya take jin komai na kara cakuɗe mata sosai take jin lamarin da Baseera ta sanar mata ya samu gurbi mai girma a sassa na zuciyarta wanda sam ba kwanciyar hankali a cikin sa.
Numfashi take ja a hankali kafun ta ja jiki ta zauna bakin katifarta idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir kamar wacce aka zubawa barkono.
Bata san me zata yi ba, bata san mai ya dace tayi ba, ta tabbata lamarin nan zai iya narkar mata da zuciya har ma da gangar jiki sosai ta kasa gasgata abin da take ji a zuciyarta sosai take karyata kanta wanda bata san mai yasa haka ba ta tabbata zuwa yanzu ya kamata ta yarda da komai ta anshi komai a yarda ya zo sai dai kuma hanzarin da tayi ba gudu bane domin kuwa tana kallo kwaɗo yana shirin yi mata kafa kafar da take zaton in har yayi mata ita to komai ma ya rigaya ya gama faruwa.
Mikewa tayi cikin rashin kuzari tana faman sakin huci mai zafi da take jin sa tun daga kasar zuciyarta yake busowa bakin kofa ta tokare Umma da take kallo dake zaune tana gyarawa Mu'azzam riga gefe guda ta zauna tana mai duban su amma a badinance zuciyar ta can wani waje ta cilla ta mai nisan gaske tana gayyato abubuwa masu yawa tana ajje mata a filin zuciyar tata.
Umma ta lura da ita amma bata nuna ta ganta ba sosai take jin tausayin 'yarta ta a zuciyarta sosai yanayin da take ciki yake taɓa mata zuciya amma ta rasa ya za tayi ta rasa wani irin hali Mariya ta daukarwa kanta wanda ba a iya gane me ke faruwa da ita ba nisawa tayi bayan ta saki Mu'azzam yayi hanyar waje domin yin wasa ta dubi dakin su Goggo Marka kafun ta juya da hankalinta sosai kan Mariya da tayi tagumi da hannu daya idanuwanta akan Umma wanda sam ba ita kuma hankalin ta yake kai ba.
"Mariya".
Umma ta fadi murya a kasa cike da natsuwa da nuna rashin wasa kafun ta nisa ba tare da Mariya ta ansata ba.
"Ban san ya zan dubi lamarin ki ba, ban san a wani mizani zan ajje komai naki ba, amma sosai zuciyata ta cilla wani bigire mai girma akan yanayin ki. Kin boye abin da yake damunki kina kiɗin ki kina rawar ki ke da zuciyarki a tunanin ki hakan shine daidai ko?".
Girgiza kai tayi kafin ta nuna da hannu a lokacin Mariya ta dago idanuwanta ta na sauke su akan Umma kafin daga bisa ta kau da su.
"Ban san mai ya canza miki halin ki ba, ban san mai ya sauya miki rayuwa ba, nidai na san ba haka kike ba, ni dai na san ba wannan halin kika ta so dashi ba, amma lokaci guda kin sauya komai na ki ya canza kamar ba Mariya ba. Zuciyarki...ina Zargin Zuciyarki da kuma abin da ke cikinta don na tabbata akwai abin da ya shigar miki zuciya ya canza miki komai na ki na tabbatar da hakan a raina, amma ki kasa faɗi mani a matsayina na uwa gareki baki da wata shaƙiƙiya wacce ta dace ki kai wa kukan ki da neman mafita kamar ni baki da kowa ba ki da wanda zaki kai wa kukan ki kamar ni amma Mariya kin yi watsi da wannan damar wanda ita kadai ce hanya mafi dacewa dake a filin duniyarki".
Nisawa tayi kafin ta dubi in da take jin motsi a bayan ta Hafsat ce tsaye ta tokare bakin kofa ta zuba masu idanu kafin ta kau da kai gefe guda ita Umma nuna wa tayi kamar bata ganta ba Mariya dake zaune itama sun ga juna a tsakaninsu su zubdawa junansu kallo raini kafin Mariya ta kau da kai tana mai kokarin mikewa kan kafafuwanta.
Bata hanata b domin ta sani ganin Hafsat ne ya sakata mikewa ta shiga daki ita ma mikewa tayi ta bi bayanta.
Zuciyarta taji tana sanar da ita da ta fadi abin da ke cinta a rai amma tsoro da yarda Umma zata dauki lamarin ya hanata motsawa sai gyaɗa kai take yi kamar wata kadangaruwa Umma na binta da kallo.
"Ba zan takura miki ba domin bana son nima a takura min bana son takura ga kowa domin takurawa tana iya sawa kiyi mani karya ki fada min abin da bashi ne ba ni kuma ba zan so hakan ba na barki har zuwa lokacin da kikayi ra'ayi don kan ki".
"Ehem...Umma...".
Da sauri ta daga mata hannu ganin yarda ta fara kalato furucin da zatayi kamar wanda akayi wa dole ganin yanayin da Umma tayi ya sanya ta tsuke bakinta waje daya idanuwanta su tara kwalla kadan.
******
Kallonta yake yi da wani irin yanayi mai haifar masa da wani lamari mai girman gaske tun daga tushen zuciyarsa da ruhi yake jin yanayin gangar jikinsa da jijiyoyin jikinsa gami da ɓargo suna ansar wani sako mai girman gaske.
A hankali idanuwansa suka shiga lumshewa kamar wanda barci yaci karfinsa kafin ya sake buɗe su sosai akanta kafin ya kau da kai yana jan numfashi yana haɗiyeshi da kyar.
"Mariya...".
Kau da kai tayi daga kallon da take masa tun dazu mai cike da tuhuma da zargi kafin lokaci guda ta galla masa harara wacce ta sanya shi shanye abin da yayi niyar fadi.
Jikinta sosai ya ansa da yanayin muryar da yayi amfani da ita wajan ambaton ta amma bata bari hakan yayi tasiri a zahirin ta ba.
Juya tayi da zubar kowa gida zuciyarta da bugawa da yanayi na fargabar abin da zai je ya dawo ta san bata yiwa kanta adalci ba ita akaran kanta ta san haka amma bata san mai yasa komai take kasa saita shi ba ita da zuciyarta. Zuciyarta sosai take kara buɗewa da lamarin amma ita taki ba da kai bori ya hau numfashi take ja tana jin yarda kamshin turaren jikinsa ke bula ko wani sashi da lungu na cikin hancin ta yana haurawa cikinta yana hautsina mata kwanya da guntun tunanin da take ta kokawa dashi tun dazu.
Bata san shi ne ba da ba abin da zai sata fitowa har ta dubeshi har yayi kokarin kara rikita mata lissafi duk da tana kaunar sanyashi a idaniyarta amma kuma kuncin da take ji game dashi yafi garwashin wuta a gareta zafi.
" A tunani na ban yin tsammani na kai har haka a wajan laifi ba a wajan ki ko da yake ban yi mamaki ba tun da duniyarki ta kubuce ta daina tunanin wani mai kama dani komai sunana".
Numfashi taja gami da tsayawa daga takunta da take yi wanda take jin jikinta kamar yana narkewa yana watsewa a kasa juyawa tayi idanuwanta na sauka a nasa da wani irin yanayi wanda lokaci guda ya haifarwa da zuciyoyi biyu abu iri guda har ya kusan tona sirrin da yake a ko wani dayan su.
"kana kokarin daura min laifin da ban san dashi ba kana kokarin hukuntani akan abin da ban sani ba...".
"Ba magana bace wannan ya kamata ki daina yin ta kin ji ko!".
Ya fadi muryarsa da sauti a ciki yana takowa gareta sosai numfashin su yake dukan juna kafin Mariya ta kau da kai cikin kasalallan yanayi.
"Akan mi zaka ce ba magana bace kai ne dai kake raina ta amma ni abin da na fadi shine daidai!".
Ita ma ta fadi da zafi a muryarta kamar zata shako wuyarsa wani irin zafi da raɗaɗi take jin zuciyarta na haifarwa mai girman gaske. da mamaki yake dubanta jin yarda take masa magana murmushi yayi mai ciwo kafun ya kara kusanto ta.
"Mariya".
Ya kirata bata ansa shi ba illa dubansa da ta sake yi tana jan numfashi.
"Kace ban cancanta da na tsaya ina kula samari ba har su zama abokan rigima ta yanzu kai mai ya kawo ka nan har ka tsaya a nan kake magana dani har kake daga min murya kenan kai ma kana sahunsu?".
Runtse idanu yayi kafun ya buɗe su lokaci guda sun kaɗa sun yayi jajir.
Bai san ta wacce hanyar zai dubi Mariya ba bai san mai ya dace yayi mata ba da zata gane in da ya sanya gabansa take ganewa taki fahimtarshi shi kuma ya rasa gane ta ina zai bi domin fahimtar da ita komai bai koma ya sanar da ita bai san ta yaya zata fuskance shi ba yana tsoron abin da zai je ya dawo.
Takun da suka ji na takalmi ne duk ya dawo dasu daga dogon nazarin da su ka fada su duka dubanta suke yi da mamaki Baseera ce tsaye hannayenta sarke a juna fuskarta sanye da bakin glass No respect wanda ya hana tonuwar asirin yanayin da kwayar idanuwanta suke ciki amma daka kalleta zaka hango wani kwantaccen murmushi mai girman gaske a fuskarta ta a hankali ta shiga takowa har ta iso in da suke tsaye sai da tayi musu kallon tsaf! kafin tayi kasa da glass din tana duban Mariya wacce ita ma ita take kallon da wani yanayi wanda ba yabo ba fallasa.
Murmushi tayi mata kafun ta dubi Dr.Karami da yayi fakare yana kallonta kashe masa ido daya tayi wanda komai da tayi din akan idon Mariya ne hakan ya sanya ta juyar da idanunta jin yarda kirjinta ke ansa sautin bugu kamar zuciyarta zata faso kirji ta yo waje wani tukuki bakin ciki da takaici taji yana taso mata yana turkewa a makoshi numfashi ma daƙyar take jan sa idanuwanta lokaci guda sun kaɗa sun yayi jajir.
Motsa baki ta shiga yi kamar zata yi magana amma ina! ta kasa zuciyarta da take jin tayi nauyi kamar zata tarwatse ta hanata aiwatar da komai takun da taga Baseera nayi zuwa ga Dr.Karami yakara hargitse mata tunani da sauri ta fara ja da baya tana kokarin kwasa da gudu kuka ne take jin yana zuwa mata mai karfin gaske wanda ta tabbata in har ta cigaba da tsayuwa a wajan ba kuka kadai ne zata samu zarafin yi ba har zubewa akasa sumamiya sai tayi.
"Mariya".
Baseera tayi saurin kiranta ganin tana kokarin barin wajan ta juya tana takowa inda ta tsaya cak! fuskarta da murmushi kafaɗarta ta dafa kafun ta kure da idanu sosai.
"Uhmmm...".
Hannu ta daga mata a zafafe tana turen hannunta da ta daura mata kan kafada.
"Bana muraɗin jin komai daga gareki kin ji ko don Allah ki bar naji da abin dake damuna a zuciyata bana son karin wani Tension din a wannan lokaci...".
"ki daina fadin haka domin duk maganar da kikeyi karya ce kawai zalla a cikinta kuma bata kai zuciyarki ba ni nasan haka idanuwanki gashi nan kuma suna karya taki da kan su don haka Tell me the trut I don like joking Mariya in kuma ba zaki iya fadi ba ni zan fadi a yanzu nan ba sai kin bata min lokaci kin bata naki ba".
Gyaɗa kai Mariya ta shiga yi idanuwanta na kawo kwalla ji take yi kamar ta kurma ihu don takaici komai na Baseera haushi yake bata ta tsaneta tsana mai tsanani bata taba zaton zata tsani wani bawa a filin duniyar nan ba amma a yau ta tsani Baseera Babbar ƙawarta da take ji da ita a filin duniyar nan wanda bazata ce ga dalili ba.
"Of Couse in ba zaki iya fadi ba ni ina damar da zan iya fadi".
Juyawa tayi ta dubi Dr.Karami da ya gama shiga wani hali na ruɗani musamman yanayin da ya ga Baseera tayi masa ba karamin tayar masa da hankali yayi ba ya jefa zuciyarsa cikin tsanani ruɗani mai matukar firgita kwanya.
"Ta kasa fada maka abin dake damun zuciyarta, ta kasa fuskarta ka ta sanar da kai komai ko da yake kai ma da naka kunshin na sirrin zuciya a tsakaninku ban san waye ya dace na dora a mizanin masu cutar kai ba".
Baseera ta fadi fuskarta ba wasa tana kai komo a tsakaninsu sosai dukkannin su suka shiga ruɗani in maganarta wanda suka rasa in da ta dosa sosai zuciyoyinsu suka shiga harɓawa da lamari mai girma akan maganar sosai suka shilla duniyar nazari ko za su kwato kansu daga duhun da suka faɗa akan zancen nata amma sun kasa sai watsa mata idanu suke yi suna faman jan numfashi kwakwalansu na kara cakuɗewa da lamari mara sauki a zuciya da ruhi.
Taku tayi a hankali ta isa wajan Dr.Karami da ya saki baki da idanu yana kallon ikon mai duka shi dai aka ran kansa bai san ina ta dosa da maganarsa ba amma zuciyarsa nayi masa zargi akwai wani sirri da ta sani a tsakaninsu.
"Zuciyarka zata cuce ka in har baka yi wasa ba".
Ta fadi tana dubansa tsakar idanu kafun ta murmusa da wani irin yanayi.
"Kana sona Dr.Karami amma ka kasa sanar dani har ni akaran kaina na fahimta ya kamata ace baka yi wannan saken ba domin kuwa bana tsammanin zan soka domin ina da wanda nake so".
Runtse idanu yayi lokaci guda yaji wasu kibiyoyin tashin hankali sun cakar masa zuciya kafun lokaci guda yaji duk wani sashi na jinin jikinsa yana tsayawa cak! da gudana komai na jikinsa yaji yana narkewa da tashin hankali buɗe idanuwansa yayi lokaci guda ya sauke su wajan da Baseera take tsaye wacce a wannan lokacin ta rigaya ta juya ta doshi inda Mariya take tsaye tana kokarin mutuwa zuciyarta na ta faman kai kawo wasu kaifaffun wuƙaƙe taji suna soke mata kirji da zuciya da ruhinta take ji su na babbakewa lokaci guda.
Tsoro ne ya saukar masa lokaci guda ganin yarda Baseera ta doshi Mariya ya tabbatarwa kansa maganar da ta sanar dashi ita zata sanar mata tsoronsa daya taki fahimtarsa tsoronsa daya tayi masa fahimta ta baibai tare da yanke masa hukuncin akan wannan lamari ya tabbata komai kara kwaɓewa zai yi da hanzari ya fara kokarin takawa domin isa wajan domin sanin abin yi amma ina kafin yayi taku biyu ta isa wajanta har ta fara magana da ita mutuwar tsaye yayi lokaci guda zuciyarsa ta buga da wani tashin hankali gumi ya fara karyo masa mai dumin gaske komawa yayi da baya ya jingina da motarsa a daidai lokacin ya hango mota kirar Benz tayi Parking kuri yayi wa motar yana kallonta haka kawai yaji motar bata kwanta masa ba a zuciya har da mai ita karan kansa kafin ya gama guntun tunaninsa ya ga Dr.Aqeel ya bayyana ware idanu yayi sosai yana dubansa da mamaki wani kunci ne yaji ya zo masa wuya lokaci guda ya tsaya kafun zuciyarsa ta shiga bugawa da sauri-sauri kamar zata yo waje.
"Kin ka sa fahimta,na fada ki kina cikin yanayi na so amma kin ki yarda sai faman wahalar da zuciyar ki kikeyi na tabbata ba zaki taba samun WALWALAR ZUCIYA ba har sai ranar da kika gasgata na sani Dr.Aqeel kike so amma kin kasa sanar dashi hakan".
Wani irin duba Mariya tayi ma jikinta har rawa yake yi yana karkarwa bakinta ya shiga motsi ji take yi kamar ta shako wuyar Baseera ta turmushe ko ta samu sa'ida da wadannan banzayen lafuza da take fada mata bata san ya kayi ta san Dr.Aqeel take so ba bata san wa ya fada mata shi take so ba bata ya akayi har bakin Baseera ya iya tafka wannan saɓon mai girman gaske ba.
Numfashi ta ja mai tauri kafun ta dube ta sosai da idanuwanta rinannu.
"ya kamata kiyi saurin tuba ga Ubangiji tun kafin ya hukuntaki akan wannan saɓon da kikayi".
Ta fadi tana faman nishi numfashinta take ji yana fizga kamar zai rabu da gangar jikinta gabadaya duban Dr.Karami tayi lokaci guda taji zuciyarta ta sake bugawa kafun ta dubi Baseera da take faman kallonta fuskarta da murmushi.
"Karki sake zuciyata tayi gangancin fara ci miki mutunci karki ga laifina tun wuri ya kamata ki sauya maganar domin ba haka take ba".
Dafa kafaɗarta tayi tana faman sauke numfashi ita jarumtar ta fara rauni bata san ya zata sauke lamarin nan da ta dauko ba mai girman gaske kwakwalwarta ta fara kamawa da wuta batayi zaton abin ba zai zo mata da sauki har haka ba ta dauka lokaci guda komai zai sauya za su karbi muradan zuciyoyinsu ashe fatanta ba zai tabbata ba burinta zai nakasa a wannan matakin tun kafin aje ko ina kau da kai tayi wasu kwalla suka taru mata kafin ta mai da su daƙyar tana faman jan numfashi duban Mariya tayi sosai har yanzu tana kan bakarta taki yarda da burin zuciyarta.
Da dan hanzari Baseera ta juya ta koma inda Dr.Karami yake tsaye gabadaya abin duniya ya ishe shi tsoro yake yi yaji inda zance zai kwana shi da Mariya.
"BAR RAINA ALLURA...".
"...Domin kuwa karfe ce".
Kamar daga sama Baseera taji muryar ta sauke zancen da ta dauko da sauri ta juya Dr.Aqeel ne yake takowa a hankali fuskarsa da yanayi na ba yabo ba fallasa hannunsa da Key din motarsa ya faman kaɗawa sosai ya tunkaro su kallan kallo suka shiga yi shi da Dr.Karami kallo ne na wani irin hali mai kama da 'a cike nake da kai, kana son kawo mani tsaiko a lamari na.'
Harɗe hannayensa yayi a ƙirji lokacin da ya iso yana mai dubansu daya bayan daya kafin ya dire akan Mariya da tayi wujiga-wujiga da ita kamar wacce ta kwato kanta daƙyar daga bakin kura.
"Bana tunanin wannan tsayuwar da kukayi akwai mafita a cikin ta maganar gaskiya ya kamata ku sani ni Mariya take so domin duk abin da kuke zantawa da yarda ke Baseera kike yi na san so kike yi ki hada tsakaninsu amma kin kasa to ki sani Mariya bata da wani wanda yake son ta take sansa tamkar yani...".
"You don get Sense At All Dr.Aqeel ya kamata ka iya bakin ka tun kafin ya kai ka ga dana sani".
Cewar Dr.Karami yana faman hirji jin abin da Dr.Aqeel yake fadi gaba gaɗi cikin gadara da isa.
Murmushi ya saki yana mai watsa hannu sama kafun ya dubi Baseera.
"Bana zaton Mariya zata so Dr.Karami domin kuwa bai nuna son ba ni na fara nuna mata so don haka ni zata ansar wa so".
"Ba dole bane ka fara furta kalmar so ka yi tunanin kuma za a anshi naka son akan wanda ya so daga baya so ba ruwansa sai wanda ya burge zuciya ta aminta dashi zata so dadewa a so ba shi yake sanya a so mutun ba so a RANA DAYA yana iya samun gurbi sannan so yana iya wanzuwa zaman shekaru amma bai samun gurbi don haka ka sani GURBIN SO ba a ko wani waje ake samun sa ba sai inda ya dace".
Gabadayan su suka juya in da suke sauraron zantukan na fitowa Huzaif ne tsaye harɗe da hannu yana faman dariya mara sauti har da 'yar kwallarsa a idanu a hankali ya shiga takowa yana mai cigaba da cewa.
"Bana tunani don ka zo ka furta so kayi tunanin zaka samun GURBIN SO a zuciyar da ka furtawa so lokaci guda so daban yake sannan so sai inda ya ga ya dace zai shiga duk da dai shi kan shi so din ba ya lura da dacewa ko matsayi ko wata daukaka kafin ya farwa zuciya kana ganganci da kace so sai ya tsufa a in da ake furta shi yake samun gurbin zama ya kamata ka sauya tunaninka".
Ya fadi ya mai duban su kafun ya dubi Mariya da tayi firgai-firgai da ita kamar wacce take jira ace kes ta kurma da gudu bata san lokacin da hawaye suka fara zuba a idanuwanta ba dumin su kawai taji tunda Huzaif ya tunkaro ta take jin gabanta na tsananta faduwa da tashin hankali mai girma so take yi ta saki ihu ko zuciyarta ta daina tsalle tsalle da babbakewa da take yi zuciyarta ta take ji tana kumbura cikin kirjinta komai na jikin ta take jin yana daukar zafi kamar roba cikin wuta ji take yi tana narkewa da tashin hankali mai girma gaske bata san wani bala'i bane kuma yake kokarin samun gurbi a yanzu bata san wani irin tashin hankali bane zai sanyota gaba a wannan bigire ta shiga uku ita a duniyarta.
Saukar hannu taji a fuskarta ana dauke mata hawaye wani numfashi taja mai karfi kafin ta runtse idanuwanta ta buɗe su Huzaif ne yake dauke su da hankicif dake hannunsa dubansa take yi da idanuwanta masu kokarin rufewa da kwalla dubansa take yi gabanta na kara tsananta buguwa komai take ji ya kwance mata bata san ya za tayi ba zuciyarta take so ta buga ko zata mutu ta huta da wannan bala'in da take ciki kau da kai tayi lokaci guda ganin irin kallon da Huzaif yake jifanta dashi mai kokarin rikitata ta tsane shi tsana sosai amma bata san abin da yasa lokaci guda zuciyarta ta tuna mata da babinsa ba ta tuna mata da GURBIN da ta bashi a zuciyarta har yake kokarin buɗewa.
"Yaa Rabbi".
Ta furta can kasan makoshinta kafin ta dago kanta ta sake dubansa Dr.Aqeel ta hango ya tunkaro wajan kamar wani mayunwacin zaki sai faman hirji yake yi yana kara hura iska a hancinsa idanuwansa sun kaɗa sunyi yayi kamar anyi masa surace da Barkono hankali ta fara kokarin ja da baya amma ina kafafuwanta take ji kamar an turkesu a waje guda ko motsi basa yi.
"Wai kai ba wani iri mutum ne? shin baka san in da so ya dace bane da yarda bai dace ba na lura kai ma dan takife ne a harkar so ka daina tunanin za kayi wani tsawon rai a harkar so tun wuri ka tattare tashin balagar kyankyasan ka da kake ji dashi sannan kake ganin karan ka ya kai tsaiko har kake tunanin TASIRIN SO zai zauna akan ka ni ne nan wanda so zai yi wa rana ba kai ba".
"Me yasa kafi ye kaunar kan ka ne mai yasa kake son cutar da zuciyarka ne mai yasa kake son ajje GURBIN SO a zuciyarka bayan ka san wauta kake yi wa kan ka bana tunanin ka san meye so kafun ka shige shi a filin duniyarka...".
Duban junan su suke yi kamar wasu mayunwatan zakuna sai faman kallon kallo sukeyi wa juna mai cike da tsananin rigima da tsanar juna.
Bige hannun da Dr.Aqeel yayiwa Huzaif ne ya sanya shi tsagaitawa da maganar da yake yi yana mai murmushi a hankali kuma ya shiga duban Mariya kamar zai shige jikinta idanuwansa sarke da nata.
"Kice baki Kaunata ki fadi su ji ba kya sona".
Runtse idanu tayi tana jin zuciyarta na kara buɗe wasu kofofi har kashi uku wanda ta jima da kullesu gabadaya take jin su suna buɗe kan su da kan su dubansa tayi kafun ta daura hannu aka tana kokarin kurma ihu amma ina ihun ma yaki zuwa hawaye kawai suke mata ambaliya a daidai lokacin Baseera ta iso tana faman duban Mariya fuska a raunane.
"Da matsala Mariya ban san ya zan sanar dake ba amma maganar gaskiya Dr.Karami ba so na yake yi ba ke yake so nayi wannan shirin ne akan cewa ko za ki nuna kishi ki fito ki sanar masa shi kike so kika kasa fadi masa...".
Ji kake kau! hannun Mariya akan kuncinta ta shiga nuna ta da hannu tana faman tangaɗi kamar wanda ta sha barasa tayi makas gabadaya ta fice daga cikin hayyacinta.
"Kina tunanin zan so shi ne bayan kin ce mani kuna soyayya kina tunannin maganar da kika fadi mani zatayi tasiri akai na ne ki bar ni kawai naji da bala'in da kuka jefa ni a ciki na san dama duk ba kwa kaunata dama na sani rakiya nayi duniyar nan na zo ne don kawai a tarwatsa min zuciya na mutu kowa ya huta burin ku ya cika Shikenan..Shikenan zan mutu yanzu zan mutu yanzun nan...".
Kawai fadin maganganun take yi tana dariya idanuwanta na zubda hawaye da sauri Baseera ta isa gareta ta riketa sosai tana faman hade jikinta da nata wani kuka mai zafin gaske ta saki zuciyarta na faman a zalzala da zafin mai girman gaske.
"karki yi saurin yanke tsammani Mariya so ya gaji haka...".
Da sauri ta kwace kanta tana faman ja da baya tana sakin huci.
"So ya gaji haka fa kika ce? dama haka so yake da bala'i a cikin sa, dama haka so yake da kayan guba a cikin sa, dama haka so yake da masifa a cikin sa?. tabbas na yarda SO DA RAININ HANKALI yake, na tabbata so akai na ya fara haifar da masifa, na tabbata akaina so ya fara haifar da bala'i, na tabbata akai na so ya fara haifar da cuta mara magani, tun kafin aje ko ina so ya fara min haka to ina kuwa in na fara zama ina yiwa so biyayya...".
Goge fuskarta tayi kafun ta dubi Dr.Aqeel da Huzaif da suka zuba mata idanu cikin halin ta shin hankali.
"Kace kana so, kai ma kace kana so sannan kuma shima...".
Sai kuma tayi shiru tana duban Dr.Karami da ya zama wani butum butumi gaɓadaya ya kasa motsi a yarda yake tsaye kawai numfashi ke fita a jikinsa amma ya tabbata ba abin da yayi saura mai motsi a ko ina a jikinsa bai taba tsammani zai shiga tashin hankali irin na yau ba bai taba zaton zai ga bala'in rayuwa ba irin na yau sai yau ya kara ganin wautarsa da gangancinsa ya kara tabbatar da maganar hausawa nacewa 'BAR RAINA ALLURA KARFE CE' in ya cire rashin dacewa ya cire ganin kankata ya dauko ma'aunin so a yarda yake ya ajje a zuciyarsa da duk haka bata faruwa ba ga shi yanzu abin da ya raina yana kokarin haifar masa da CIWON RAI mara magani.
"Baseera ban san wata ƙaddara bace ta jingino mani wadannan mutanan ba, ban san mai yasa ALKALAMIN ƘADDARA da ya tashi rubuto min tashin hankalin rayuwa ba, ya jehomin ta hanyar so...".
Da sauri ta iso gareta tana mai rufe mata baki.
"Karki ce haka ki dauki komai a matsayin jarabawa sannan kuma ƙaddararki ta rayuwa...".
"zan dauki komai a matsayin ƙaddara amma ban da lamarin na domin na tabbata bala'i ne bala'i mai ansa suna bala'i domin na tabbata duk ikirarin da suke yi suka ce suna sona ba wanda yake tausayi na a cikin sun in da suna sona ba za su so su gannin cikin bala'i ba amma da yake su masu son kai ne ko wanne ya dauko tawagar rigunan bala'in sa ya jinginawa rayuwata".
A hankali ta fara taku tana kokarin barin wajan kafin ta tsaya ta juya tana duban su.
"UKU BALA'I kuka dasa min a rayuwa domin ba zan kira shi UKU ALHERI ba kuma ina so ku sani dukkan ku ina son ku ko wannan ku na saka shi a zuciyata yanzu abin da ya rage a tsakanin ku sai ku zo ku dandatsani kowa ya dauki kason sa".
Ta na gama fadin haka ta juya cikin sassarfa kuka na kara tunkodo mata zuciya hannayenta ta saka ta toshe bakin ta har ta fada cikin gida a zaure ta durkushe tana faman jan numfashi hawayen da take so su zubo mata sun ki zuwa kukan ma lokaci guda ya tsaya cak! kanta ta daga sama ta runtse hannayenta duk biyu ta dora a saman kirjinta tana faman haki kafun lokaci guda numfashinta ya dauke idanuwanta suka ƙaƙƙafe.
Ihu Baseera tayi lokacin da ta biyo bayanta taga halin da take ciki da sauri ta isa gareta ta kai hannu tana kokarin jinjingata amma ina lokaci guda ta bingire kasa ba alamun numfashi hakan ya kara sanyata sake kurma wani uban ihu tayi waje da gudu a daidai lokacin su su duka ukun sukayo cikin soro Dr.Karami har yana cin karo da Baseera da sauri ya rikota tana kokari faduwa ya fada cikin soron a daidai lokacin kuma Umma da Goggo Marka gami da Hafsat suka duro cikin soron ganin Mariya asheme ba alamun rai ya sanya kowa sakin salatin Dr.Karami yayi kanta yana kokarin daukarta Dr.Aqeel yayi saurin riko shi fizge kansa yayi yana yin kurin sake kaimata sura Umma dake tsaye ta shiga duban su su duka ba wanda bata sani ba da sauri ta isa wajan da Mariya take yashe ta durkushe tana mai dundubata kafin da dago ta dube su da hawaye a fuskarta.
"Yaa Allah".
Ta fadi tana mikewa kafun ta dubesu ba tare da wani firgici ba.
"Sai ayi kokarin yi mata suttura a kai ta gidanta ko saboda Allah yayi mata cikawa".
Ba wai Dr.Ƙarami da su Dr.Aqeel ba kadai ba hatta Baseera sai da numfashinta ya dauke.
Saukar ruwan da suka ji ne ya dawo da su hayyacin su Hafsat ce dauke da rusheshen baho tsaye tana faman yatsine fuska sai faman kallon uku ahu take jifan su dashi take yi gabadayan su a firgice suka dawo hayyacinsu sai faman kara kaina sukeyi a tsakanin su sun rasa abin yi ma Dr.Karami ya ja tunga ya tsaya yana mai da numfashi kafun ya dubi in da Mariya take yashe har zuwa lokacin dai jiya-i-yau ƙura mata idanu yayi sosai yana kallonta tun daga babban dan yatsanta har zuwa kanta gata nan sambal! Kansa ne ya shiga juyawa yana dawo masa da maganganun da Umma tayi da karfin gaske ya toshe kunnuwansa yana furta.
"Nooooo!".
Kafin lokaci guda ya sureta kamar wanda ya dauki 'yar tsana ya fice da ita daga cikin soron gidan dukkan su suka goya masa baya illa Goggo Marka da Hafsat dake tsaye suna duban su da wani irin yanayi da nuna halin-ko-in-kula ga lamarin Umma kuwa cikin gida ta koma ta dauko mayafinta ta yo waje ko kafin ta iso ba wanda ta tadda nan ta jin gina da bango tana faman ajiyar numfashi mai zafi kafin ta rintse idanuwanta ta buɗe su.
"Allah ga bayinka kai ka san abin da yake damun su a filin duniyar nan kayi musu maganinsa".
Tana gama fadin haka ta juya cikin gida cikin yanayi na rashin tabbas din 'yar ta ta domin kuwa ta san ko sun kaita asibiti sai dai su dawo da ita domin tuni ta tabbbatar Mariya ta shuri burji rai yayi halinsa.
*_Ina bukatar ra'ayoyinku Makaranta da duk wani masoyina na labarin nan kafin muje ga cigaba ina so duk ku antayo min wani tsokaci game da labarin da ya danganci sharawa ko gyara_*
  *_KAMALA MINNA_*😍😍😍
Post a Comment (0)