UKU-BALA'I 39

UKU-BALA'I

NA

KAMALA MINNA

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA TALATIN DA TARA.




Juyi kawai take yi zuciyarta na zafi da wani irin raÉ—aÉ—i mai girman gaske sosai take jin komai ya sauya mata sosai take jin duniyar da abin da ke cikinta sun zame mata kunci da ukuba komai take kallo a mara dadi zuciyarta da ruhinta suna wani mataki na tashin hankali ba abin da take tunawa sai kalaman Dr.Karami sosai suka taba mata zuciya da ilahirin jikinta bata taba zato ko tsammani ba ko a mafarkinta bata taba zaton Dr.Karami ya dube ta ya na gaya mata magana son ransa har haka ba ko da yake bata ga laifinsa ba har da ita da ta tsaya tana kai kawo akan sa ashe duk kulawa da yake nuna mata a zahiri ba haka bane zuciyarsa sam bata tare da ita.
Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata da saurin ta kai hannunta ta shafe su don bata so Umma ta lura da halin da take ciki yau kusan sati uku kenan amma ta kasa manta kalaman Dr.Karami sai faman kuwwa suke yi mata akai da kunnuwa ta rasa mai yake yi mata dadi a filin duniyar nan bata san abin da ke kokarin faruwa da ita ba ta ji zafin kalamansa amma kuma zuciyarta taki bashi laifi taki yarda da laifin da take dorasa masa bata ma san mai haka yake nufi ba tun da abin nan ya faru ta kasa sukuni tunanin Dr.Karami ya sha mata kai ko barci take yi shine dai take tadda cikin barcin nata.
Mikewa tayi daga shingiÉ—en da take ta shiga safa da marwa a cikin dakin domin samowa kanta mafita sosai take jin ciwo mai girma a zuciyarta sosai take jin gangar jikinta na kawo mata bakutan wani yanayi mai girman gaske wanda ta rasa yarda zata kwatantashi sosai Dr.Karami yashiga yin tasiri akanta da kalamansa da suka hanata sukuni.
Bata san mutum na tsaye ba kuma za ta iya cewa ga lokacin da ya shigo yana jima yana dubanta da yanayin ta kafun ya motsa laɓɓansa cikin wani irin yanayai.
"Ya jikin naki?".
A firgice ta juya jikinta har rawa yake yi jin sautin muryarsa lokaci guda ta dube shi da idanuwanta da suka kaÉ—a sosai shima ita yake kallo da wani irin yanayi mai girman gaske kallon kallo suka shiga yi a tsakaninsu da wani yanayi wanda suka kan su ba su san haka na faruwa a garesu ba sun jima a wannan halin kafun Dr.Karami ya kau da idanuwansa jin zuciyarsa na bijiro masa da wasu lamura da ya tabbata ba za su haifa masa da É—a mai ido ba numfashi yaja mai tauri yana jin yarda zuciyarsa ke buÉ—ewa da wani yanayi akan Mariya sosai yake jin ko wani sashi na jikinsa na ansa amon tausayawa da yanayin da ya ganta a ciki bai yi tsammanin lamarin ya kai har haka ba nisawa ya kuma yi yana fesar da wani zazzafar huci kafin ya dago idanuwansa da suke lumshewa kamar mai jin barci.
"Uhmm jiya munyi waya da Umma take sanar dani wai baki da lafiya".
Ya fadi yana mai yawatawa idanuwansa akan fuskarta da wani irin yanayi mai taba zuciya yatsine fuska ta shiga yi tana kau da kanta gefe kafun ta motsa laɓɓanta kamar wacce akayi wa dole.
"Ni ba abin dake damu na".
Ta fadi da yanayin fushi a muryarta murmushi yayi kafun ya taka ya karasa shiga cikin dakin hannayensa sarƙe a kirjinsa ya zuba mata idanuwansa sosai yana mata kallon tuhuma kallon da take ji har cikin jikinta yake shiga ji take yi kamar zata narke ta watse a wajan.
"Kin fiye gardama wallahi kenan Umma karya take yi miki ko? Sau nawa ina kiran wayar ina cewa a baki amma bakya ansa na sani ba wai rashin lafiyar ta hanaki ansar kirana ba fushi kike yi dani ko akan abin da na san na fada miki gaskiya ko".
Da sauri ta dube shi idanuwanta a warware kafin ta tura baki gaba.
"Fushi fa kace kai din ne zan yi fushi da kai akan wani dalili saboda ni kuma gani wahallaliya ko bani da aikin yi".
Tun da ta fara magana yake kallon ta da mamaki mai girma a ransa dubanta yake yi har ta dire kafun ya ja wani numfashi yana jin yarsa zuciyarsa ke wani irin juyawa a mataki na wahala runtse idanu yayi kafun ya sake buÉ—e su kalaman nata yake jin su kamar saukar ruwan zafi a dukkan sassan jikinsa takawa ya shiga yi yana isa gabanta ganin haka da tayi taja baya da sauri shikuwa bai bar takawa gabanta ba har sai da ya kusan mannuwa da jikinta sannan ya tsaya.
"Me kika ce maimaita ban ji ba".
Ya fadi yana mai karkaÉ—e kunnuwansa fuskarsa a daure tamau hakan ya fadar mata da gaba don ta tabbata maganarta ta bata masa rai sosai don ga fuskarsa nan ta nuna.
"Maimaita mana ina jinki".
Ya sake fadi yana watsa mata wani kallo da ya razana mata zuciya da sauri tayi baya har tana kokarin faduwa kasa.
"Ni kike fadawa haka ko Mariya Good kin kyauta".
Yana fadin haka ya juya yana kokarin fita juyowa yayi ya dubeta sosai.
"Dr.Aqeel da Huzaif ba zan hanaki tsayuwa da su ba don na lura su ne kika mai da abokan zama har kuna SA'INSA amma ki sani ko samarinki ne ko auren su zakiyi dole ki fidda daya domin kuwa maza biyu ba auren su ake yi ba gabadaya kisan da wannan".
Yana gama fadin haka ya dage labulan ya fice daga cikin dakin.
Sosai ta ware idanu waje jin maganar da yake fadi mata sosai taji zuciyarta ta tabu ta rasa mai Dr.Karami yake nufi da haka ta rasa mai ya mai da ita da yake fadi mata irin wadannan kalaman wayace masa son su take yi wa yace masa samarinta ne har yake gaya mata magana har haka.
Dafe kanta tayi da take jin yana barazanar tarwatsewa ta runtse idanu tayi tana jin wani zuki da raÉ—aÉ—i na taso mata tun daga kasar ruhinta yana direwa a dukkan jikinta sosai taji duniyar na juya mata komai take ji yana kara hargitsewa sosai kalaman Dr.Karami suke taba ta don ta lura kallon wata mace daban yake yi mata mai wani hali na daban...
"Ke Mariya wai shin meke damun ki ne? na rasa gane kan ki gabadaya kin daurawa kan ki wani bakin hali da ZURFIN CIKI wanda ban san ki dashi ba".
Maganar Umma ce ta katse mata dogon tunani da ta afka da firgice ta juyo tana duban Umma da ke tsaye bakin kofa tana watsa mata wani irin kallo.
"Na gaji nagaji da halin ki Mariya haba mana ke kenan kullu yau min ki hana kan ki sukuni ki hana wasu kuma haba mana ai wannan shiga Hakki ne an tambayeki me ke damun ki kin ki fadi to ya kike so kiyi yanzu shima Hisham din ya zo daga yanayin da ya fita na san ke ce kika bata masa rai ko shikenan ki cigaba da yi abin da ranki ke so karki daina kin jiko".
Tana gama fadin haka ta juya ta fice daga cikin daki ranta a matukar bace.
Mariya da tayi mutuwar tsaye ta shiga duban kofar kanta na kara rikicewa da sarawa sosai taji komai ya sake kwance mata wani abu mai nauyi take ji ya zo kirjinta ya zauna sosai kwallar da take makalewa taji sun zoba mata akan kuncita kafafuwanta taji suna kokarin kasa daukarta da sauri tayi kasa ta zube wani kuka taji ya zo mata ba zato ba tsammani kanta ta tura cikin cinyoyinta jikin har k'yarma yake yi hawaye suka balle mata kamar an buÉ—e famfo ita kam bata san yarda zata cakuÉ—a wannan lamarin ba komai ya kulle na kanta sosai take jin tashin hankalin na daÉ—uwa a filin duniyarta.
********
A hargitse ta fado cikin gidan bayan mai gadi ya buÉ—e mata Get din sam ba ta lura da wanda yake gabanta ba sai da taji ta daki mutum tayi taga taga kamar zata fadi da sauri ya riko mata hannu idanuwanta a rufe don ta sadakar ta je kasa jin an riketa ne ya sanyata saurin buÉ—e idanuwanta ta sauke su a cikin nasa da suke zube akan ta.
"Tareeq".
Ta furta tana mai zare idanuwanta sosai kafun tayi hanzari fizge hannunta taja da baya.
"Yi hakuri don Allah wallahi ban gan ka bane...".
Hannu ya daga mata idanuwansa na kan wayarsa ba tare da yayi mata magana ba ya rabata ya wuce abin sa wani takaici ya kule ita kam bata san wani irin hali wannan mutumin gareshi ba na shariya da kyaliya tun da ta fara ganinsa a hakan dai yake jiya iyau ko muryarsa bata taba ji ba sosai hakan ke taba mata rai ta ki jinin mutum mai irin wannan hali shiyasa Dr.Karam...
Shiru tayi da sauri jin tunaninta na kokarin canza jaha da sauri ta figi kafarta tayi cikin gidan.
Abin da bata sani ba shi Tareeq ko da ya tafi makalewa yayi yana kallon ta da wani yanayi wanda shi kadai ya barwa ransa tun ranar da ya fara ganin Mariya yaji gabadaya ta tafi da imaninsa amma ya rasa ya zai yi kuma gani yake yi kamar da raini ace k'awar kanwasa yake bibiya shiyasa ke ta faman tsare gida shi ala dole girma ne nan yake dauka bayan kuma zuciyarsa ta jima a wani fanni na rashin wannan girman don tuni ta yasar dashi akan abin da tajima tana so.
Numfashi ya ja yana fesarwa kafin ya fice daga cikin gidan.
Ko da tashiga cikin falon ba kowa sai karar Tv kawai dake tashi numfashi taja kafun ta ja kafa da sauri ta haye saman bangaren Baseera kofar a buÉ—e ta same ta don haka da sauri ta tura ta shige kwance ta hango Baseera tayi É—ai-É—ai saman gado sai faman zabga murmushi take yi kamar wacce aka zunduma gidan aljanna kunnan ta dauke da waya alamun wayar da takeyi mai muhimmanci ce turjiya Mariya tayi ta harÉ—e hannayenta a kirjinta ta zuba mata ido cike da mamaki kafun taja kafarta da sauri ta isa gareta duka ta daga mata ganin yarda ta saki jikinta har rigar ta na tattarewa cinyoyinta sun bayyana a firgice ta tashi ta zunduma ihu ta cillar da wayar can gefe idanuwa warwaje Mariya da ke tsaye bata san lokacin da ta kwashe da dariya ba tana dubanta ita kuwa Baseera nar-nar tayi da idanu kamar zata yi kuka kafin ta yi hanzari sankowa daga gadon ta cakumi wuyar Mariya.
"Idan kina da mutunci in nitse wallahi baki da mutunci sam!".
Ta tureta can gefe tayi tana susar cinya inda Mariya ta dake ta.
"Ai ke za a kira haka wannan ai rashin hankali ne kina waya har baki san kayan suna kokarin bayyana jikinki ba yanzu in da wani ya shigo ya ganki a haka fa me kike tsammani".
Gefen gado ta koma ta zauna tana faman turo baki gaba tana rarraba idanu in da zata ga wayarta can gefen gado da hango da sauri ta rarrafa ta dauko kafin ta shiga kaÉ—a idanuwa.
"Yo ba dole na fada cakwalkwalin nishadi ba ni da mai kaunata ne fa rabin raina sakata zuciyata jinin jikina...".
"Ke dalla jaye ki bani waje mara kunya kawai".
Baseera ta kwashe da dariya tana tafa hannaye.
"Ba maganar rashin kunya akan me zan cuci akai na haka kawai ai dole na tattali kayana ke kin san kuwa yarda nake son wannan gayen kuwa ya hadu iya haduwa ko ta ina ke dai kawai bari sai kin ga Fine Bobo dina sai kin kusan mutuwa ke dai yi ta zama a haka ba ki ga tsuntsu baki ga tarko yan maza sai gwara kan ki suke yi kin kasa fahimtar komai ki kasa sanin komai AKAN SO wallahi tun wuri ki koyi soyayya malama ki ji yarda ake fadawa cakwalkwalin nishadi wayyo Allah sahibi na mai sona ina son ka".
Wani tukukin bakin ciki ya turnuke Mariya ganin yarda Baseera ke wani narkewa tana bin lafiyar gado sai wani lumshe idanu take yi mamaki ne ya cikata har yaushe Baseera ta koyi soyayya har haka ita bata sani ba ko WUKA A MAKOSHI zata gani bazata iya cewa ta taba ganin Baseera da saurayi ba amma yau RANA DAYA wai soyayya take yi ta gani kashe har tana koranta mata tsaki taja kamar harshenta zai tsinke kafun ta mike tana hararar Baseera kamar idanuwanta za su zubo kasa.
"Wayyo Allah My Dr.Hisham".
Baseera ta fadi tana kara rungume fulo sosai sai narkar da idanu take yi.
Sunan da ta kira ne ya sanya Mariya firgita tana dubanta bata san lokaci da ta isa bakin gadon bata zauna idanuwanta a warwaje.
"Me kika ce Baseera wani suna naji kin kira".
Sake narkewa tayi kafun ta mike zauna tana sakin wani lallausar murmushi.
"Abin da kunnuwanki suka jiye miki mana masoyina nakira ko saɓo nayi ne nayi saurin tuba".
Girgiza kai Mariya ta shiga yi cikin wani irin yanayi sunan da Baseera ta ambata ba karamin tayar mata da hankali yayi ba in har ba kuskure tayi ba kamar sunan Dr.Karam ne takira ko da sunan masoyin ta anya kuwa ko dai ba shi bane ai masu sunan da yawa a filin duniyar nan zuciyarta taki gasgata haka ta fi yarda da Dr.Karami ne masoyin Baseera wani irin bugu taji kirjinta yayi da sauri ta dafe tana faman jan numfashi kadan-kadan duban Baseera tayi wacce sai faman danne-danne takeyi a waya fuskarta da murmushi.
"Cikin raina na sanyoka ka bani guri nima in shigo naka".
Baseera ta fadi tana rungume wayar a kirjinta idanuwanta a lumshe kafun ta buÉ—e su akan Mariya da tayi fakare tana dubanta kirjinta sai faman lugudan bugu yake yi.
Tsaki taja na karo ba a dadi kafun ta ja numfashi.
"Wai meke damun ki ne haka wajan ki fa na zo amma kin tsaya kina raina min hankali in ba zaki kulani ba malama na tashi na san in da dare yayi mani".
Ta karashe a hassale kamar zata kife Baseera da mari.
"Haba my Besty ina ni ina raina miki hankali kawai dai kisan in mutum ya tsunduma cikin kogin love din nan ne abun ne ba sauki walla...".
Tun kafun ta karasa Mariya ta mike kan kafafuwanta sai faman huci take yi kamar zata hadiye Baseera wani kallo tayi mata kafun ta ja kafa da sauri tana kokarin barin dakin ganin haka da Baseera tayi da sauri ta mike ta riko hannunta sosai.
"Yi hakuri mana mai yayi zafi shi ba wuta ba haba mana Besty bai kamata kiyi mani haka ba zo muje ki gaya min abin da ke faruwa na lura da yanayin ki kina cikin damuwa sosai".
Fizge hannunta tayi rai bace kafun ta dubi Baseera.
"Ni ki rabu dani kawai tafiya zan yi...".
Ware idanu tayi sosai ta sake riko hannunta murya a kasa cikin rarrashi.
"Zo muje na baki labari kin ji san nan ki sanar dani abin da ke damun ki a duniyar nan besty baki da wata k'awa wacce tafi ni nima kuma bani da wata k'awa wacce ta fiki mu rufe MATSALOLINMU a tsakaninmu tare da samun mafita ba tare da kowa yaji ba don Alalh zo muje mana".
A hankali taja hannunta ta kaita bakin gado ta zaunar kafin taje ta dauko mata ruwa mai rangwamin sanyi tare da lemon Exotic ta dire mata a gabatan amma Mariya ko kallo ba su isheta ba halin da take ciki a yanzu ji take yi kamar zuciyarta zata kama da wuta don bala'in da take ji a ranta komai take ji ya rikice mata kwanyarta ta tsaya cak! da aiki.
"Ban san me zance miki ba Mariya akan wannan lamarin amma ba karamin taba min zuciya yake yi ba na rasa yarda zan kama domin samo mafita na rasa gane kan ki kin ki sakin jiki ki fayyace abin da ke damun ki sannan in aka ce ga abin da ke damun ki baki daukar haka ne sai ki nuna kin amincewarki zuciyarki na wahalar dake sosai da sosai akan abin da kika san gaskiya amma kin ki amsa".
Baseera ta fadi fuskar da yanayi na tausayi kafun ta mike kan kafafuwanta da wani irin yanayi na sanyi jiki taku tayi daya biyu kafun ta juya ta dubi Mariya wacce zuciyarta gabadaya ta gama sakin wannan layin da Baseera ta dauko maganar soyayyar Baseera ce yake kai kawo akan sa wanda ke fadar mata da gaba baka dan ba tagumi tayi hannu bibbiyu idanuwanta cikin yanayi na tsananin damuwa.
"Kullum abu cigaba yake yi na rasa in da kika sa gaba na lura kina jin dadin rayuwa a haka ne shiyasa sam baki damu da kan ki ba baki damu da matsalar da kike ciki ba ZURFIN CIKI da kike yi wallahi ba zai kai ki ko ina ba zuciyarki ne zata haifar miki da matsala tun da kin kasa gasgata abin da take zuwa miki dashi".
"Baseera wai da gaske soyayya kike yi?".
Mariya ta fadi cikin yanayi na faduwar gaba da ansar da Baseera zata bata akan hakan kallon sosai Baseera ta shiga yi mata jin ta saki layin da ta dauko mata na matsalar ta ta dauko wani na daban murmushi tayi kafun ta juya idanuwanta sosai.
"meye abin yi mani wannan tambayar Mariya ya za ayi muna wata magana ki na dauko wata kum...".
"Tambayarki nayi ansa nake bukata kawai".
Mariya ta tare ta a hassale kamar zata fizgota daga tsayen da take.
Juyawa tayi kamar zata fice daga cikin dakin kafun ta sake juyo ta koma cikin dakin sosai tana bin Mariya da kallo murmushi dauke a fuskarta.
"Bana tunanin wani mugun abu nake yi bana tunani saɓo nayi don na fara soyayya lokaci nane yayi na kai matsayin ace ina da saurayi kamar yarda ake bukatar ko wata 'ya mace ta kasance da saurayi in har lokacin ta yayi...ko da yake naga kamar mamaki kike yi ko Mariya amma ban san dalilin ba".
Wani irin zillo taji zuciyarta tayi gabanta ya buga da karfi a hankali ta shiga rintse idanuwanta tana tura laɓɓanta cikin bakinta da wani irin yanayi mai girman gaske a zuciya mai tattare da kunci buɗe su tayi akan Baseera da take kai kawo a tsakiyar dakin fuskarta da annuri na farinciki so take yi ta tambayeta da wa take soyayya amma tana tsoron ansar da zata bata domin kuwa sosai gabanta ke dokawa da tashin hankali mai girman gaske akan Baseera sosai zuciyarta take gasgata zarginta sosai take jin gangar jikinta na amanna da lamarin mikewa tayi kan kafafuwanta da yanayin na karfin hali domin har wani jiri-jiri take gani taku tayi daya kafun ta sauke kanta kasa tana ambaton sunan Allah ya tsareta da mugun ji.
"Uhmm naji kamar kin ce Dr.Hisham ko".
Ta fadi dak'yar kamar wacce zata fashe da kuka gabanta na dokawa da tashin hankali.
"Yarda kika ji haka lamarin yake ba kokwanto kike yi ba shine mai kauna ta din".
Baseera ta fadi a iyakacin gaskiyarta ba alamun wasa wani irin zubewa Mariya tayi bakin gado numfashinta na fita a hankali-hankali kamar wacce tayi gudun CETON RAI idanuwanta ta runtse da karfin tsiya ji take yi kamar ba ita ba komai take ji na jikinta yana narkewa da wani irin tashin hankali wanda tun da take bata taba jin zuciyarta ta kawo mata haka ba jikinta har É“ari yake yi ta buÉ—e idanuwan nata da suka fara kaÉ—awa cikin karfin hali ta shiga saita kanta tana kalato murmushi mai sanya ciwo a zuciya mikewa tayi kan kafafuwanta tana kallon Baseera da ta zuba mata idanu da wani irin yanayi kafun tace.
"ba laifin kaddara a lamarin nan naki Mariya har da laifin ki komai ke faruwa ya kamata ki sassautawa kan k...".
Daga mata hannu tayi cikin karfin hali ji take yi kamar zuciyarta zata tarwatse jikinta take ji yana wata irin k'yarma kamar wacce aka jonawa wutar nepa.
"Wai kina nufin Dr.Karami dai Baseera".
Ware idanu Baseera tayi sosai lokaci guda yanayin ta ya sauya kafun ta motsa laɓɓanta idanuwanta aƙan Mariya tana karantar yanayin da take ciki.
"Kin san dai a filin duniyar nan tamu ba wani Dr.Hisham bayan Karami ko...".
Ai bata kai aya ba tuni Mariya ta fice daga cikin dakin cike da tashin hankali mai tsananin girma da kokarin yayyaga zuciya da jiki baki daya kafafuwan kawai take dorawa a duk in da taji sun sauka har ta isa cikin falon ba kowa hakan ya sanyata ficewa da sauri hannayenta saman kirjinta idanuwanta sai lumshewa suke yi a hankali kamar wacce ke jin matsanancin barci haka ta isa bakin Get ko maigadi batayi wa magana ba ta buÉ—e kofar ta fice cikin hanzari hanya ta dauka sosai tana tafiya idanuwanta da wasu zafafan hawaye da suke ambaliya so take yi ta karya abin da kunnuwanta suka jiye mata so take yi ta karyata zuwanta gidan su Baseera a zahiran ce so take yi ta karyata kanta da kan ta ba taji wannan furucin ba so take yi ace ma a tashi duniyar baki daya ba tare da tabbatuwar wannan lamarin ba baza ta iya dauka ba zuciyarta baza ta iya daukar wannan lamarin ba ina! ba zata iya ba so take yi a tashi duniya so take yi a ce tashin alkiyama ne so take yi komai ya zama tarihi kamar ba ayi shi ba.
Wasu hawaye masu kokarin dauke fatar fuska suka sake balle mata zuciyarta take ji na kara kamawa da wuta ji take yi kamar narkewa take yi ji take yi kamar ba ita bace ji take yi kamar ba a halicce ta ba a filin duniyar nan.
Sam bata lura ta kai bakin titi ba har ta hau tsakiyarsa ihun mutane da Horn din motoci ya fargar da ita cikin razana zare idanu tayi waje ganin irin Go-Slow din da ta hada mutane wasu na ganin kamar bata da hankali wasu kam danna mata ashar kawai suke yi gaɓadaya ta firgice ta rasa ina zatayi hayaniyar mutane ya kara razana mata kwakwalwa hannu ta daura akai tana kokarin kurma ihu taji an ja hannunta anyi gefe da ita runtse idanu tayi jin wani irin Shock da ya ansa duk kan sassan jikinta da sauri ta buɗe idanuwanta buɗe baki tayi tana kokarin kurma ihu ganin wanda ke rike da ita da sauri ya sanya dan yatsarsa akan laɓɓansa fuskarsa ba wasa alamun tayi shiru tsit tayi amma har lokacin fuskarta da tashin hankali jikinta sai k'yarma yake yi fizge hannunta tayi tana faman ja da baya shi kuwa bin ta yake yi da kallo cikin tsananin mamaki da tu'ajibi hannayensa harɗe a kirjinsa ganin dai tana kokarin komawa kan titin da sauri ya fizgota ya ja ta kamar zata kifa can inda yayi parking din motarsa ya isa ya buɗe gidan gaba ya bata umarnin shiga amma taki sai faman tirjewa take yi tana faman wurga masa mugun kallo take yi kamar idanuwanta za su fado kasa.
Shi kan sa sai da ya ji gabansa ya fadi da kallon da Mariya take yi masa kallon da ya tabbatar akwai abin da yasa take yi masa shi kallo ne na tuhuma kallo ne kuma na ka yaudare ni kallo na kayi mani ba daidai ba.
"Please Mariya shiga daga ciki mana...".
Fizge kanta tayi tana kokarin raɓashi ta wuce batare da ta shiga motar ba amma ganin irin tsayuwar da yayi babu wasa ga wani girma taga yayi mata da kwarjini wani irin bugu taji gabanta yayi lokacin da taga rinannun idanuwansa ta kalle shi kallon da taga yana jifanta dashi da yanayin da taga kwayar idanuwansa na canzawa gabadaya ya firgita ta da sauri tayi kasa da kai.
"Muje nace".
Ya fadi da wata murya wacce ba wasa a cikinta dubansa ta sake yi cikin nuna son yin gardama amma yarda taga ya tsare gida sosai ya sanya jikinta mutuwa murus ta tokare bakin kofar ita bata shiga ba ita kuma ba ta wuce ba.
"Yaa Allah! Mariya kina da matsala sosai a rayuwarki kin fiye taurin kai".
Ya fadi yana dafe kansa da wani yanayi na damuwa kafun ya sake dubanta wacce ita ma a lokacin ta dago kanta ta watsa masa kallo.
"Nifa ba zan shiga ba kawai ka rabu dani kayi tafiyarka ba abin da ya dame ka dani ba abin da ya dame ka da yanayin da nake ciki don haka Leavea Alone Please".
Da mamaki yake dubanta jin maganar da take fadi wanda suka kusan tarwatsa masa kai amma sai ya maze cikin tsare gida sosai ya nuna rashin wasa.
"Kisan Allah ki shiga motar nan tun kafin raina ya baci don na lura sai na nuna miki kala irin taki sannan zamu zauna lafiya dake ban san abin da yake hawa miki kai ba ban san mai yasa gabadaya kike kokarin sanya kan ki cikin matsala har haka b...".
"Wannan ba damuwarka bace kawai ka rabu dani nayi tafiya...".
Ai ba ta kai ga dire zancenta ta ji ta saman set din motar baje numfashin da take ji na sauka akan fuskarta ne ya sanyata saurin dubansa kallonsa tayi shima ita yake kallo da matsanancin bacin rai sai faman huci yake yi tana jin yarda zuciyarsa ke bugawa da sauri-sauri sosai take kallonsa ta kasa dauke idon ta kamar yarda shi yake kallonta da wani yanayi wanda ya shiga haifar mata da kasala mai tsanani gabadaya taji duk wani tashin hankali da take ji da bacin rai game dashi yana kaucewa a hankali wasu kibiyoyi take hangowa suna fitowa daga cikin idanuwansa suna sauka ana ta sosai taken jin zuciyarta na buÉ—ewa da wani lamari mai giraman gaske kallon Dr.Karami take yi kamar bashi ba kallonsa take yi a wani mutum mai kwarjini da haiba gami da cikar zati wani kallo take jifansa dashi kamar tun da take bata taba ganin mai kyau da k'yan kallo kamar sa ba.
Hure mata idanu da yayi ne ya dawo da ita hayyacinta ba tare da yace da ita komai ba ya juya dayan barin na zaman direba ya shiga yayi wa motar ki har zuwa lokacin fuskar tashi ba alamun wasa sai ma kara tsare gida da yake yi ita kuwa gabadaya ta gama narkewa sai faman juyi take yi ta kasa zama sosai a kujerar da take duk yana kallon yanayin ta har ya yiwa motar Key ya cillata saman titi yana mai kara sautin wakar 'BECAUSE OF YOU' ta Amanda Mena dake tashi a cikin motar...


*_KAMALA MINNA_*😘😘😘😘
Post a Comment (0)