WANDA BAYA SALLAH

WANDA BAYA YIN SALLAH


Wanda baya yin Sallah malamai sun kasa shi gida biyu;

*A-Na farko baya sallah saboda bai yarda da wajibci,yana ganin ba dole bace sai kayi sallar ba yana ganin wanda baiyi sallah baya da laifi, abune wanda kaga dama kayi ko kabari,mai wannan halin kafirine wanda ya fita daga musulinci*.

Saboda da Fadin Manzon Allah SAW;
*(Banbancin da yake tsakanin Mutum da tsakanin shirka da kafirci shine barin Sallah)*
@رواه مسلم (82)

Da kuma fadin Manzon Allah SAW yace;
*(Alkawali da banbancin da yake tsakaninmu da tsakanin kafirci shine Sallah,dukkan wanda baya sallah to ya kafirta)*
@أخرجه الترمذي (2621)، والنسائي (463)، وابن ماجه (1079)، وأحمد (22987)

*B-Wanda baya sallah sabodaa kasala da lalace amma yasan abinda yake sabon Allah ne kuma ba daidaibane ba,kuma yana mai yarda da sallah wajibice sai dai baya yine saboda sakaci da addini,to wannan malamai sun sami sabani akansa;*

Wasu malaman suna ganin bai kafirtaba yana nan a matsayin musulmi mai raunin imani,wasu suna ganin ya zama kafiri na fita daga musulinci saboda hadisan da muta kawo a sama.

Wasu malaman suna ganin musulmine mai raunin imani matuqar bai halasta kinyin sallah ba,sai ayia masa nasiha ya gayara.

الإمام ابن عثيمين رحمه الله-: 
Yana cewa;
*"Dukkan wanda ya bar yin Sallah to ya kafirta daga cikin tafarkin musulinci,ida yana da mata to aurensu ya mutu kuma za'a rabasu,baza'ace yankansa ba,ko yayi Azumi da sadaka Allah bazai karbi wannan aikiba,kuma baza'aci yankansa ba,bazai shiga garin makka ba,idan ya mutu baya halasta ayi masa wanka ko sanya masa likkafani kuma baza'ayi masa sallah ba kuma baza'a binne saba a maqabarta musulmi ba,.........."*
@الفتاوى ( ٣٦/۱٢ ) ]


وقال رحمه الله في شرح رياض الصالحين:

*"Wanda baya sallah yafi Yahudu da Nasara sharri,domin su idan sukayi yanka halasne aci yankansu amma wanda baya sallah haramunne aci yankansa,hakan nan Halasne namiji ya auri wadda ba musulmaba daga cikin Yahudu da Nasara,amma wanda baya sallah ko wadda bata sallah harammune a aureta koda suna zauna sai ya daina sallah to auransu ya mutu....."*
@شَرحُ رِيَاضِ الصَّالِحِينَ : (100/5)

A taqaice dai;
*Wanda baya sallah dan sakaci da wasa da addini amma ya yarda sallah wajibice amma baya yi gaba daya,to wannan za'a bashi damar ya tuba kwana 3 idan yaki sai akashe shi kisan haddi,amma idan yana yi amma yana inkarin wajibancin Sallah to wannan ya fita daga musulinci*


  Allah ne mafi sani


Post a Comment (0)