WAƘAR ZAUREN INDIA 🇮🇳

WAƘAR ZAUREN INDIA 🇮🇳 🇳🇬


Daga Haiman Raees


* Bismillah na fara da sunan mai duniya.

* Sarki Jalla Wanda bai da tamka ko ɗaya.

* Gaisuwa ga ɗaha shugaban dukanin duniya.

* Manzona mai karamci da gudun duniya.

* Da Sahabbai da Alihi dukka gaba ɗaya.

* Da masu son sa ko ina a cikin duniya.

* Yau waƙe na masoya ni na shirya

* Masoyan Jarumai na Ƙasar Indiya.

* Kiɗa da waƙa duk na mutanen Indiya.

* Fim da salo da wanka wanda ya buwaya.

* Wannan ne ya sa ayau muka yo tarayya.

* Ta zumunci da haɗin kai babu hamayya.

* Wannan ne ya jawo kafuwar zauren Indiya.

* Gashi mun zamo da ban a dukkan nahiya.

* Aikinmu mu ke yi babu hayaniya.

* Sahihan Labarai ba wata tankiya.

* Sharhin Fim da Hausa babu Haniniya

* Nishaɗi a tsakanin mu babu ragin ɗaya.

* Amma yau gashi mun samu wake ƙwar ɗaya.

* Da ya jawo ɓacin gari da ƙiyayya.

* Ruɗu da firgici yana so muyi ta hamayya.

* Sai dai mun gano Ja'irai tun bayan da akai Walƙiya.

* Kuma In shaa Allaah duk sai sun bayyana.

* A idon kowa in Rabbi ya so zako su bayyana.

* Roƙona ni dai yau a wajen Rabbana.

* Ya amince macuta dukka su bayyana.

* ƴan ƙota hamagawa masu baƙin kunnuwa.

* Shashashai falalan yankin laulawa.

* Ja'irai mugaye masu adawa.

* da zumunci da muke yi da mutuntawa.

* Rabbana Bala'i a garemu kai yi tsarewa.

* Haƙuri a tsakanin mu ka daɗa ninkawa.

* Ka bamu juriya da jajircewa.

* Assalamu Alaikum ni kam nan zan tsaya.

* ni ne naku mai son ayi gaskiya.

* Haiman Khan na zauren Indiya.

* Nayi jinjina ga Mahukuntan zauren India 🇮🇳 🇳🇬

<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com
Post a Comment (0)