ALLAAH YA HALITTA MANA KAYAN JIN DAƊI NE DOMIN SU TAIMAKE MU AKAN YI MASA ƊA'A

ALLAH YA HALITTA MANA KAYAN JIN DADI NE DON SU TAIMAKEMU A KAN YI MASA DA'A

Shaikhul Islami Abul Abbas (r) ya ce:
" ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺳﺒﺤﺎﻧﻪ ﺇﻧﻤﺎ ﺧﻠﻖ ﺍﻟﻠﺬﺍﺕ ﻭﺍﻟﺸﻬﻮﺍﺕ ﻓﻲ ﺍﻷﺻﻞ ﻟﺘﻤﺎﻡ ﻣﺼﻠﺤﺔ ﺍﻟﺨﻠﻖ؛ ﻓﺈﻧﻪ ﺑﺬﻟﻚ ﻳﺠﺘﻠﺒﻮﻥ ﻣﺎ ﻳﻨﻔﻌﻬﻢ ﻛﻤﺎ ﺧﻠﻖ ﺍﻟﻐﻀﺐ ﻟﻴﺪﻓﻌﻮﺍ ﺑﻪ ﻣﺎ ﻳﻀﺮﻫﻢ ﻭﺣﺮﻡ ﻣﻦ ﺍﻟﺸﻬﻮﺍﺕ ﻣﺎ ﻳﻀﺮ ﺗﻨﺎﻭﻟﻪ ﻭﺫﻡ ﻣﻦ ﺍﻗﺘﺼﺮ ﻋﻠﻴﻬﺎ .
ﻓﺄﻣﺎ ﻣﻦ ﺍﺳﺘﻌﺎﻥ ﺑﺎﻟﻤﺒﺎﺡ ﺍﻟﺠﻤﻴﻞ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺤﻖ ﻓﻬﺬﺍ ﻣﻦ ﺍﻷﻋﻤﺎﻝ ﺍﻟﺼﺎﻟﺤﺔ ...
ﻓﺎﻟﻤﺆﻣﻦ ﺇﺫﺍ ﻛﺎﻧﺖ ﻟﻪ ﻧﻴﺔ ﺃﺗﺖ ﻋﻠﻰ ﻋﺎﻣﺔ ﺃﻓﻌﺎﻟﻪ ﻭﻛﺎﻧﺖ ﺍﻟﻤﺒﺎﺣﺎﺕ ﻣﻦ ﺻﺎﻟﺢ ﺃﻋﻤﺎﻟﻪ ﻟﺼﻼﺡ ﻗﻠﺒﻪ ﻭﻧﻴﺘﻪ ﻭﺍﻟﻤﻨﺎﻓﻖ - ﻟﻔﺴﺎﺩ ﻗﻠﺒﻪ ﻭﻧﻴﺘﻪ - ﻳﻌﺎﻗﺐ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ ﻳﻈﻬﺮﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﻌﺒﺎﺩﺍﺕ ﺭﻳﺎﺀ ...
ﻭﻛﻤﺎ ﺃﻥ ﺍﻟﻌﻘﻮﺑﺎﺕ ﺷﺮﻋﺖ ﺩﺍﻋﻴﺔ ﺇﻟﻰ ﻓﻌﻞ ﺍﻟﻮﺍﺟﺒﺎﺕ ﻭﺗﺮﻙ ﺍﻟﻤﺤﺮﻣﺎﺕ ﻓﻘﺪ ﺷﺮﻉ ﺃﻳﻀﺎ ﻛﻞ ﻣﺎ ﻳﻌﻴﻦ ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ ".
ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ‏( /28 368 - 370 )
"Asali Allah Tsarkakakke ya halicci kayan dadi da ababe sha'awa ne don cikar maslahar halitta, don su janyo ma kawukansu abin da zai amfanesu da su, kamar yadda ya halicci fushi don su ture abin da zai cutar da su da shi. Kuma ya haramta abin da amfani da shi zai cutar da su na ababe sha'awan, kuma ya zargi wanda ya takaita a kansu.
Amma wanda ya yi amfani da abu na halas mai kyau don ya taimake shi a kan gaskiya to wannan yana daga cikin kyawawan aiyuka...
IDAN MUMINI YA KASANCE YANA YIN NIYYA A KAN DUKKAN AIYUKANSA SAI AIYUKANSA NA HALAS (MUBAHAT) SU KASANCE DAGA CIKIN KYAWAWAN AIYUKANSA, SABODA KYAUN ZUCIYARSA.
MUNAFUKI KUWA - SABODA MUNIN ZUCIYARSA DA NIYYARSA - ZA A YI MASA UQUBA A KAN AIYUKAN IBADA DA YAKE BAYYANAWA A MATSAYIN RIYA.
Kamar yadda aka shar'anta Uqubobi (horo) don su sa a aikata wajibai a bar aiyukan haramun, HAKA AKA SHAR'ANTA DUKKAN ABIN DA ZAI TAIMAKA A KAN HAKA (Da'a ma Allah)".

ABIN LURA:
1- Dalilai a kan cewa; aiyuka na halas suna zama aiyukan samun lada in an kyautata niyya, akwai Hadisin da Annabi (saw) ya ce: "Saduwa da iyali Sadaka ne".
Da kuma Hadisin loma da za ka sa a bakin iyali (ciyar da iyali).
2- Dalili a kan cewa; Ibadar Munafiki batacciya ce saboda bacin zuciyarsa da niyyarsa shi ne Hadisin Zuciya idan ta gyaru gangan jiki ya gyaru, idan ta baci gangar jiki ya baci.
3- Ya kamata a taimaka ma iyalai da 'ya'ya da sauran na karkashin mutum a kan aiyukan alheri da da'a ma Allah ta hanyar abubuwa na halas da kayan jin dadi, kamar kudi, da ababen more rayuwa da sauransu, don a karfafesu a kan aiyukan alheri da da'a ma Allah.
Post a Comment (0)