TAMBAYA AKAN KASUWANCI

Assalamu alaikum


Tambaya:

 malam inawuni anyi sallah lafiya malam tambaya gareni malam ni Yar kasuwace to sai wani harka yataso inada Wanda nake sayen Kaya gareshi muna kasuwanci tare to malam watace keson Kaya kuma bakudi ahannuna sainace takawo kudinta sai a,aikomata amma kuma kamar akan sarine zata saye to malam dagacan idan za,a,aikowa tahanuna ake aikowa Wanda yake aikomin inabiyanshi shizaikawo to malam da,akayimata kan sari nima saina aza wani abusama kamar cikin naira dubu sainasamu ribar Dari biyu itama akan sari zata saida saita,aza wani Abu Asama to shine nace zan iya aza Dari biyun ko bazan azaba nagode malam sainajika
.

Amsa:


Ba za ki aza komai akai ba, anan abin da xa ki yi shi ne tunda ta amince miki ta baki kudinta a sayo mata kaya kan sari, sai ki mata cikakken bayani cewar akwai wadda kike aika ya karbo kayan, amma kina biyansa, sai ki fada mata abin da kike bashi dan ta sani, amma ki boye kudin da kike ba shi then ki dora ribar 200 wannan haramun ne, ana son a gina kasuwanci a fili komai a bayyana shi a kan sharadi idan abokin hulda ya amince kalas shikenan in bai amince ba a haqura.



Wallahu A'lamu.
.

Imam Ridwan Sabo Aujara.

Daga Zauren
🕌ISLAMIC POST.

Ga masu bukatar shiga group dinmu sai su turo da cikakken suna zuwa 08166650256 ta WhatsApp.
Post a Comment (0)