BACCIN DOKI A TSAYE

BACCIN DOKI A TSAYE

Daga: Zakariyya Shu'aib Adam

Doki dabba ne mai ƙarfi da kyawu. Masu sarauta da dukiya ne suka fi anfani dashi. Saɓanin jaki da raƙumi, doki bai cika aikace aikace na wahala ba. Yafi kuzari da karsashi a wurin hawan sallah (Durbar festival), sukuwa (Horse race) da kuma wasan ƙwallon doki (Polo). Doki yana da tsafta shi yasa bai cika kwanciya a wuri mai dauɗa ba. A mafi yawan lokuta, baya fita kiwo sai dai a kawo masa abinci turkensa.

Shekaran jiya, ni da abokina mun wuce wani doki yana barci a tsaye. Abokina yayi mamakin wannan ɗabi'a matuƙa. Sanin cewa ni ɗalibi ne a Tsangayar likitancin dabbobi tasa ya jefo tambaya gareni. Me yasa doki ke da wannan ɗabi'a? Ba shi kaɗai ba, na san da yawan mutane (har da wasu daga cikin masu karanta wannan rubutu) sun taɓa ganin doki na barci a tsaye kuma za su so jin hikimar hakan.

Doki dabba ne mai nauyin gaske. Idan ka kwatanta girman jikinsa da ƙafafunsa, za ka riski cewa ƙafafun ba za su iya ɗaukar nauyin jikin na tsawon lokaci ba tare da hutu ba. Wannan tasa Allah (SWT) yayi wani masarrafi da ake kira
STAY APPARATUS a ƙafafunsa na gaba da na baya (Fore and hind limbs). Wannan tsari na stay apparatus, shi ke ba doki damar tsayuwa na tsawon lokaci tare da bacci ba tare da ya faɗi ba.

STAY APPARATUS yana nufin haɗuwar tsoka (Muscles), tendons da ligaments waɗanda ke ɗaure (locking) gaɓɓan ƙafafun doki (limb joints). Wannan masarrafi yana taimakawa doki wurin sauke nauyin jikinsa ga ƙafafu uku yayinda yake hutawa da guda. Bayan ya huta da ƙafa gudan, sai ya kuma sauke nauyin ga wasu ƙafafun uku ya huta da wata ƙafar guda.

'STAY APPARATUS' ya ƙunshi ababe kamar haka:

(1) Suspensory apparatus (irinsu superficial da deep digital flexor tendon, proximal da distal check ligament haɗi da sesamoidean ligament).

(2) Tsokoki irinsu Biceps brachii, Triceps brachii da kuma Extensor carpi radialis.

(3) Stifle-locking mechanism, hock, patella tendon da patella ligaments.

[Ayi haƙuri da waɗansu kalmomi da na kasa fassara su zuwa Hausa. Hakazalika, ban faɗaɗa bayanin Mechanism na stay apparatus ba saboda rubutun zai tsawaita kuma fahimtar abin zai yi wuya ga wanda ba ɗalibin likitanci dabbobi ba.]

Allah shine mafi sani.
Post a Comment (0)