SARKIN SARAKAI BOOK 1 - 3

SARKIN SARAKAI BOOK 1. 3
KODA SARKI YAJI HAKA saiyayi murmushi yace yakai haluf ka sani cewa muddin kana tare dani babu wani abu mai rai da ya isa ya cutar dakai abinda nake so dakai shine ka kwance guzurinmu ka dauka abinci mu ci tare cikin tsananin mamaki bawa haluf ya dubi sarki yace haba ranka ya dade ina ni ina cin abinci tare dakai? Ai fiye da shekaru goma baya ma sa adda na fara yimaka bauta ban taba samun kusanci da kaiba kamar yanzu sarki sahibul hairi yayi murmushi a karo na biyu yace yakai haluf ka sani cewa wannan tafiya da ka samu ikonyi tare dani ba karamar matsayi ta janyo maka ba don haka ina so ka yaye dukkanin wani hijabi dake tsakaninmu na bawa da maigidansa ka dauka cewa tare da abokinka ne in kuwa kana sabawa hakan zan umarceka da komawa birnin misra in yaso nayi tafiyata ni kadai koda jin haka sai bawa haluf ya nutsu cikin hanzari ya bude guzuri ya fidda abinci ya zuba a faranti sannan ya dauko salkar ruwa ya tsiyaya a cikin kofi guda ya ajiye a gaban sarki, sarki sahibul hairi ya nannade hannun rigarsa sannan haluf ya zuba masa ruwa ya wanke hannu gama wanke hannun keda wuya sai sarki ya karbi salkar ya umarci haluf daya tara hannayensa shima ya zuba masa ruwan ya wanke cikin matukar mamaki haluf ya noke kamar ba zaibi umarni ba amma dayaga sarki ya murtuke fuska sai yabi umarnin da gaggawa nan dai suka kama cin abincin tare suna nishadi tamkar aboki da aboki harma sarki na zakulo wasu labarai yana baiwa haluf na ban dariya shi kansa haluf bai san sa adda ya saki jikinsa yayi ta kyalkyalewa ba basu gushe ba suna wannan nishadi ba har dare ya fara tsalawa a sannan ne sarki ya kishingida bisa shimfida nan da nan kuwa barci ya sace shi sa adda bawa haluf yaga sarki sahibul hairi yayi barci saiya mike tsam ya fita wajan tantin ya tsaya haluf ya dubi gabas da yamma kudu da arewa baiga komai ba kuma baiji motsin komai ba face kukan tsuntsaye sai kuma wata irin iska mai karfi da sanyi ke kadawa koda haluf yaji sanyi yayi masa yawa sai yahada wuta a bakin tantin ya zauna yana jin dumi jim kadan da faruwar haka sai shima ya fara gyan gyadi yana jin wannan hali ne wadannan gabza gabzan mutane suka fara ketowa ta cikin duhun dare daga cikin bishiyoyi suka durfafo wannan tanti nasu sarki sahibul hairi sudai wadannan mutane sun kasance karti majiya karfi adadinsu yakai dubu dukkaninsu sanye suke da walkin fata kuma damatsansu cike suke da gurayen tsafi kowannensu na dauke da muggan makaman yaki kuma ya murtuke fuska dajan shuni kai wannan mutane dai matukar kwarjini da ban tsoro suke dan ko a mafarki mutun ya gansu sau daya har abada ba zai daina tunawa dasuba.
Cikin sanda mutanen suka iso daf da bawa haluf wanda ke ta sharar barci bai san abindake faruwa ba da zuwansu sai babbansu ya dubi mutum uku yayi musu inkiya dasu duba cikin tantin nan take kuwa mutum ukun suka shiga cikin tantin sai gashi sun fito dauke da sarki sahibul hairi a kan shimfidarsa yanata shara barci shima baima san cewa an fito dashi ba daga cikin tantin Al amarin da ya baiwa shugaban mutanen dariya kenan ya takarkare ya saki mahaukaciyar dariya mai kama da kukan jaki karfin dariyar ne ya farkar da sarki sahibul hairi da bawa haluf daga barci koda haluf yayi arba da wadannan karti ababan tsoro saiya firgice ya yunkura da nufin ya ruga da gudu shubana kartin ya dakawa bawa haluf tsawa yace tsaya nan inda kake ko yanzun nan takobina ta sha jininka Jin wannan batune yasa haluf ya dada rudewa ya fadi kasa yana makyarkyata bai san sa adda ya saki fitsari a wando ba shi kuwa sarki sahibul hairi koda ya farka ya bude idanunsa yaga wadannan zakwakuran karti saiya kare musu kallo ya kwanta yana mai lumshe idanu da nufin yaci gaba da barcinsa tamkar baisan da tsayuwar kartin ba al amarin da ya bawa shugaban kartin mamaki kenan kuma ya fusatashi kawai ya sake dokawa sarki sahibul hairi tsawa kai waye har da zaka bude idanu ka ganmu amma baka tsorata ba? Na rantse da darajar wannan sana a tamu ta fashi yau shekara ashirin kenan muna wannan aiki ama bamu taba haduwa da wani mahaluki ba face ya razana da ganinmu kai kuwa gashi harma kwanciya kake a gabanmu da nufin yin barci, Sa adda sarki sahibul hairi yaji wannan batu sai ya mike zaune ya fuskanci shugaban yan fashin yace yaku wadannan kartin banza masu sana ar banza kuyi sani cewa baza kusan komu suwaye ba face kunci gaba da hanamu yin barcinmu koda gama fadinhaka sai sarki ya koma ya kwanta ya sake lumshe idanu cikin tsananin fushi da kuma zafin nama shugaban kartin ya zare wata lafceciyar takobi ya kaiwa sarki sara a ciki da nufin ya tsinkashi gida biyu kafin takobin ta dira a jikin sarki sahubul hairi tuni ya goce yai tsalle can gefe daya tamkar an janyeshi da majaujawa gaba daya kartin saida sukayi mamakin wannan zafin nama da jarumtaka tashi.....
Zan Cigaba Insha Allah
Post a Comment (0)