SARKIN SARAKAI BOOK 1 - 4

SARKIN SARAKAI BOOK 1. 04

Shugaban yan fashin ya sake rugawa da gudu kan sarki sahibul hairi da nufin ya sake kai masa sara shikuwa sai ya daka tsalle sama ya doki kirjinsa da kafa guda karfin dukanne yasa shugaban kartin yai sama ya fado kasa ya baje kamar an shanya tsumma koda ganin haka saigaba dayan dakarun nan suka zare maka mansu sukayi kan sarki sahibul hairi babu wanda ya kula da batun bawa Haluf wanda ya bude baki yana kallon abinda ke faruwa cikin tsananin mamaki nanfa karti da sarki sahibul hairi suka kacame da azababben yaki suna kai masa sara da suka yana gocewa amma duk wanda ya nausa saikaga ya zube kasa sumamme wani lokacin kuma in ya kama hannun mutum ko kafarsa sai dai kaji ya karya basss! Tamkar ya karya silin kara babu abinda zai baiwa mutum mamaki face tsananin zafin naman sarki sahibul hairi da iya kauciya da zilliya sai da aka shafe kusan rabin sa a yana turmutsa yan fashin nan amma baiyi tunanin zare makami ba da makaman nasu suka dinga sarar junansu saida yacewa gaba dayansu su dubu sun zube kasa daga matattu sai sumammu sai karyayyu shi kuwa shugaban yan fashin nan kirjinsa ya karye bai iya motsawa ba bare ya samu ikon tashi sa adda bawa haluf yaga irin wannan tsabar sadaukantaka ta mai gidansa sarki saiya cika da mamaki dukda cewa yasha jin labari a birnin misra cewa indai aka fita filin yaki sarki bai taba kasa samun galaba ba akan abokan gaba Ance idan ya fusata ma yana shafe sa a bakwai yana yaki bai gajiba kuma a duk rayuwarsa baitaba gudu ba ko juyawa abokan gaba baya yayinda sarki sahibul hairi ya gama da dukkanin yan fashin saiya dauki shimfidarsa ya koma cikin tantinsa yayi kwanciyarsa nan da nan barci ya sake kwasheshi harda minshari tamkar baiyi wahalar komai ba shikuwa bawa haluf sai idanunsa suka kekashe saboda ganin wannan masifa har gari ya waye bai sake rintsawa ba wannan shine abinda ya faru ga sarki sahibul hairi da bawa haluf bayan sun baro birnin misra da nufin zuwa birnin Askandariyya don dakko gatarin sihiri ++ A cAN birnin misra kuwa tun sa adda sarki sahibul hairi ya sallami fadawansa akan cewa ya barwa Galadima Aminul has rikon kasa sai gaba dayansu suka taru a gidan waziri Akiyanu da tsakar dare suka shiga tattaunawa ta sirri kan yadda zasu bullowa wannan lamari Waziri akiyanu ne ya fara mikewa tsaye yace yaku yan majalisar birnin misra kun sani cewa talauci ya zauta sarkinmu har ya bazama cikin duniya neman arziki labari ya isar mana cewa duk duniya babu matsafi kamar boka shamzul azwas kuma babu wani mahaluki daya taba shiga cikin wannan fada tasa wadda ke can tsuburin bahar zallas amma haukan sarkinmu da tunaninsa na shirme ya yanke hukuncin zuwa can don dauko yarinya Alfila ko shakka babu Ajalin sarki yazo dole ne ya hallaka a kokarin shiga gidan boka shamzubul azwas kaibama shiga fadar boka shamzubul azwas ba ai zuwa fadar sarki Barusa na birnin Askandariyya ma tafi karfinsa bare har ya shiga ya dauko gatarin sihirinsu duk abinda sarki ke takama dashi walau jarumta ko tsafi dakarun sarki barusa sun ninkashi sau goma lallai idan ya shiga wannan fada saiya zama gawa wannan bayani da nayi muku yaisa ku tabbatar da cewa sarki ya tafi kenan har abada ba zai dawo ba a raye saidai gawarsa tazo yanzu gashi munaji muna gani ya bayar da karagarsa ga Aminul has mutumin da gaba dayanmu mun fishi cancanta da karagar mulkin yanzu wacce shawara kuke da ita bisa wannan lamari? Sa adda waziri akiyanu yazo nan a zancensa sai gaba daya yan majalisar su bakwai sukayi shiru aka rasa wanda zaice wani abu daga can sai wani dattijo waishi KILZAM ya gyara murya yace juyin mulki na farat daya a cikin wannan dare ! Ina nufin musa aje gidansa a kashe shi kuma a hallaka iyalansa gaba daya inyaso gobe da safe saimu nada ka sarki mu kuma ka raba mana mukamai waziri Akiyanu ya jinjina kai yace kaima kazo da shawara mai kyau amma kuma akwai matsala matsalar kuwa itace gaba dayan jama ar gari sun san cewa sarki ya bawa Aminul has rikon gari idan aka wayi gari akaga an kashe shi kuma har na hau mulki nan da nan za ayi zargin cewa ninaje nasa aka kashe shi lallai ba zamuyi gaggawar hallaka shiba dolene mu tsaya muyi tunani da hangen nesa don kada jama a suyi mana tawaye yanzu mu bari ya fara mulkin muga iya gudun ruwansa lallai nayi muku alkawarin cewa saina dawo mana da mulkin kama karya irin wanda muka saba dashi Ada kafin hawan sarki sahibul hairi' koda jin wannan batu sai farin ciki ya kama gaba dayan yan majalisar suka aminta da wannan shawara ta waziri Akiyanu sannan taro ya watse kowa ya tafi izuwa gidansa a sirrance ++ Al amarin magajin karagar mulki kuwa wato Aminul has tun sa adda sarki ya sallameshi a matsayin ya bashi rikon kasa sai ya tafi izuwa gidansa yana mai matukar farin ciki mara misaltuwa koda dawowarsa gida sai ya iske matarsa SHULAIBA tsaye a harabar gidan tana wasa da wadansu tsuntsaye dake cikin keji tsuntsayen sun kasance yan kanana ababan sha awa masu launin ruwan Kwai ,
sulaiba ta kasance kyakkyawar mace mai karancin shekaru domin bata haura ashirin ba tun tana da shekara tara ta auri Aminul has har yanzu bata taba samun haihuwa ba koda shigowar aminul has cikin harabar gidan ya hango shulaiba a cikin nishadi saiyaji ya kara cika da farin ciki ka tsaye suka nufi juna kowannensa na murmushi ta tarbeshi cikin murna tana mai cewa yakai mijina yau kuma wanne farin cikineya samemu naga ka shigo da walwala ba kamar yadda ka saba ba kullum sa adda aminul has yaji wannan tambaya sai yakama hannayen shulaiba ya rike sannan yace ya abar kaunata kiyi sani cewa daga yau na zama sarkin birnin misra'' koda jin wannan batu sai shulaiba ta dago idonta a firgice ta soma ja da baya fuskarta cike da alamomin tsoro da fargaba ba zato ba tsammani sai idonta suka ciko da kwallah suka fara zubar da hawaye al amarin da yayi matukar tayarda hankalin Aminul has ke nan ya matso daf da ita ya sake rike hannayenta yace yake matata ina dalilin zubar wannan hawaye naki shulaiba tayi ajiyar zuciya tace yakai mijina hakika kayi ganganci kuma kayi babban kuskure harda ka bari ka karbi rikon kasar nan a hannun sarki domin kuwa yanzu ne zaka tara makiya masu yawan gaske yanzu ne rayuwanmu zata zamo a cikin mugun hadari domin farautarta za a shiga yi ka san irin mulkin da sarki yake yi a kasar nan mulkine wanda talakawa ke so amma kuma su sarakai basa so, ina tabbatar maka da cewa wannan tafiya da sarki yayi damace babba ga sarakunan kasar nan wacce suka samu donsu dawo da mulkin zalunci da murdiya na sani cewa kai baka da irin ra ayinsu , ra ayinka irin na sarki sahibul hairi ne lallai duk yadda zasuyi suga bayanka sai sunyi ina mai shawartarka daka hakura da wannan matsayi ka mika musu abinsu yayinda shulaiba tazo nan a zancenta sai hankalin aminul has ya dugunzuma ya rasa abindake masa dadi a duniya domin tabbas ya san cewa duk abinda ta fada gaskiya ne aminul has ya sunkuyar da kansa kas yana mai tunani zuwa dan lokaci daga can kuma saiya dagao ya dubeta a lokacin shima idanunsa suka ciko da kwalla yace yake abar begena dare da rana ina sonki tuna cewa yau shekara goma sha daya kenan dayin auranmu amma har yanzu bamu sami magaji ba ki tuna cewa akan wannan matsala muka je wajan boka Hadimul Asur yayi mana bincike inda ya sanar damu akan cewa bazamu taba samun haihuwa ba face mun kwanta akan gadon sarautar kasar nan sau sittin yau ga dama ta samu donme zakice mu barta? Nikam na yarda na hakura da wannan mulkin amma bayan cikar kwanaki sittin akan gadon sarautar sa adsa aminul hass yazo nan a zancensa sai hankalin shulaiba ya kara dugunzuma fiye da koyaushe ta fashe da kuka tana me cewa hakika azzaluman kasar nan bazasu bari muyi kwana sittin ba a cikin gidan sarautar kasar nan face sun rabamu da rayuwarmu cikin tsananin tausayi aminul has yasa hannu ya gogewa shulaiba hawayanta yace ki kwantar da hankalinki abar kaunata ki tuna cewa daga yau gaba dayan dakarun sarki sahibul hairi masu tsaron lafiyarsa sun dawo karkashina ina nufin zasuci gaba da tsaron lafiyata kamar yadda suke tsaron tasa kinga kuwa ashe babu abinda ya isa ya taba lafiyata kodajin wannan batu sai shulaiba tayi yake tace haba mijina ashe ka manta da karin maganar da akace 'makashinka na jikinka' ina tabbatar maka da cewa da dangari akanci gari su dakarun da kake takama dasu aidasune za a hada kai aci amanarka yayinda aminul has yaji haka sai yayi shiruyana tunani domin ko shakka babu haka abin yake bayan dan gajeran tunani sai ya sake duban shulaiba yace ki tuna cewa mahaifinki shine mutuminda yafi kowa hikima da hangen nesa a cikin birnin misra kafin rasuwar mahaifinki saida ya zamana cewa babu abinda za a zartar face an nemi shawararsa kuma bai taba bayar da gurguwar shawara ba hatta yake yaken da ake fita ance shine yake sanar da sarki hanyoyinda ake bi a samu nasara cikin gaggawa A tarihin kasar nan babu wanda yafi mahaifinki sanin sirrin mutanen kasar da sirrin gidan sarauta yake matata nikam na sani cewa babu yadda za ayi barewa tayi gudu danta yayi rarrafe yanzu wacce shawara zaki bani wacce zata kaimu ga iya kare kanmu daga sharrin makiya har izuwa lokacinda sarki zai dawo daga wannan tafiya na damka masa amanarsa? Lokacinda aminul has ya tuno mata da mahaifinta mutuminda ake kira ABU HAKIM nan take tashiga tunani mai zurfi abu hakin ya kasance shahararren mutum ko ina a cikin birnin misra ya kasance mutum mai hangen nesa kakkaifar kwakwalwa tarin ilimi da basira saida abu hakim ya shekara sittin a duniya sannan ajali ya riskeshi abu hakim nada tsatstsauran ra ayin rayuwa fiye da sarki domin har ya rasu bai mallaki dukiyarda ta kai darajar dinare goma ba suturarsa guda biyuce kacan sai takalminsa na fada guda daya sai kuma wata sandarsa wacce duk inda ka ganshi yana tare da ita yana dogara duk da kasancewarsa ba tsoho ba.....
Zan Cigaba Insha Allah
Post a Comment (0)