ABUBUWA GUDA GOMA DA MATA ZA SU YI DOMIN FARANTAWA MAZAJEN SUY

*Abubuwa 10 da mata za su yi don faranta wa mijinsu*



*Ga wadannan abubuwa 10 kamar haka*

─━━━━━━░★░━━━━━━─

*1-Jima’i*
Hanya ta farko da mata za su faranta wa mijinsu ita ce, ta bangaren jima’i.
Sau da yawa mata babu ruwansu da nuna wa mijinsu suna bukatar jima’i, akwai abokina da ya fada mini ya shekara fiye da 10 da yin aure amma matarsa ba ta taba neman ya sadu da ita ba, kullum idan har suka yi jima’i to shi ne ya neme ta, hakan ya sanya ya daina jin dadin jima’in domin ba ya ganin matarsa tana shaukin jima’in, hakan ya sa ko ya sadu da matarsa ba ya jin gamsuwa.
Don haka idan mata tana son ta rika faranta wa mijinta, to ta rika nemansa, idan ba za ta iya kai tsaye ba, to ta kirkiro hanyar aika dan sako. Mace za ta iya aika dan sako ta hanyar sanya tufafin mai daukar hankali, mace za ta iya aika dan sako ta hanyar kissa da kwarkwasa da kuma kisisina. Motsa gabobi ga mace kan iya tura dan sako cikin kankanen lokaci. Mata su rika ba da kansu ga mijinsu a duk lokacin da ya bukaci hakan, kada su rika azabtar da shi don ya bata musu rai, su ce tun da ya yi musu abin da ba su so, to shi ma ba zai samu abin da yake so ba.
Mata su rika tarairayar mijinsu, ta hanyar nuna musu shi dan lelensu ne, hakan zai sanya shi farin ciki. Ga matan da suke aiki kada bayan sun dawo gida maimakon su lura da mijinsu sai su rika yin aikin ofis. Ko su rika korafin sun gaji. Kada su bari mijinsu ya je aiki ya dawo gida.


*2-Tsabta*
 Mata su kasance masu tsabta, tsabtar jiki da ta muhalli. Ku rika tsabtace gidanku, kada ku bari datti ya rika kaka-gida a gidanku. Ku share ko’ina, sannan ku sanya turaren kamshi. Ku mayar da gidanku wurin da mijinku zai rika tunaninsa ko da yana wurin aiki. Ya rika dokin dawowa gida, domin ya san zai samu kwanciyar hankali da natsuwa.


*3 Amincewa da bukatun miji*: 

Ku kasance kodayaushe masu amincewa da bukatun mijinku. Ku rika tunanin wane abu ne mijinku yake so wadanda ba ku yi ba, sannan ku rika tunanin abubuwan da idan kuka yi masa zai ji dadi. Kada ku hana shi bukatar saduwa, ko kin yi masa girki mai lagwada. Idan ransa ya baci har yana muku fada ku kaskantar da kanku, sannan ku samu hanya mafi hikima wajen sanar da shi abin da ya faru. Kada ku rika daga murya idan kuna magana da mijinku zai rika jin kun raina shi.
Idan har ya fahimci kuna biya masa dukkan bukatunsa to zai ji dadi a ransa.


*4-Yarda da miji a matsayin shugaba*

Mata su yarda mijinsu shi ne shugaba, sannan su rika ladabi da biyayya da kuma da’a ga miji, hakan zai sanya ya rika jin farin ciki a zuciyarsa. Kada mata su manta cewa, Manzon Allah (SAW) a cikin wani Hadisi ya ce “Da zan umarci wani ya yi wa wani sujuda da na umarci mata ta yi wa mijinta sujuda.” Don haka yi wa miji biyayya kodayaushe zai sanya ya rika samun farin ciki mai dorewa a rayuwar aure.

*5-Kwalliya da ado*

Kamar yadda tun a lokacin da ba ku yi aure ba, kuke rangada masa kwalliya da ado idan zai zo wurinku hira, Yi wa mijinku ado da kwalliya kafin ya dawo daga wurin aiki zai sanya shi farin ciki. Ku yi wanka, ku yi kwalliya, ku fesa turare mai kamshi, hakan zai sanya mijinku natsuwa da jin dadi da kuma farin ciki.


*6-Addu’a*
A duk lokacin da mijinku zai fita idan ya ji kun yi masa addu’a sai ya ji farin ciki ya kama shi, hakan kuma zai sa ya dage wajen nemo abin da za a ci a gidan, domin ya san kun san fitar da zai yi tana da muhimmanci a wurinku. Ku rika cewa: “Allah Ya kiyaye, “Allah Ya dawo da kai lafiya,” ko “Allah Ya sa a fita a sa’a,” ko kuma “Allah Ya sa a samo abin da aka je nema,” da sauransu.

*7- Godiya*
 Babu abin da namiji yake so face idan ya fita ya nemo wani abu ya kawo gida, walau ya sha wahala ko cikin sauki har idan ya kawo gida, ya ji matarsa ta yaba, sannan ta yi godiya. Yana da kyau mata su rika gode wa mijinsu, hakan zai rika sanya shi farin ciki. Wani lokaci ma matan za su iya kambama abin da ya samo, ta hanyar bayanin yadda al’amura suka yi tsanani, su rika nuna ba karamin kokari mijinsu ya yi ba. Su nuna sun yi sa’ar miji. Yin godiya ga miji zai sa ya ji farin ciki, sannan ya zage damtse wajen neman abinci don ya kawo gida. Kada mata su manta Manzon Allah (SAW) ya ce “Duk matar da ba ta gode wa kyautar mijinta ba, to Allah (SWT) ba Ya kallonta (da rahama).”

*8-Tausasa lafazi*
 Miji kan yi farin ciki a duk lokacin da matarsa take yi masa magana cikin tausassan lafazi. Domin ya fahimci akwai girmamawa daga matarsa. Ko da miji ya yi muku abin da ba ku so, to kada ku manta da yin bayani cikin lafazi mai taushi, kada ku ce kullum mijinku na maimaita abin bakin cikin da yake muku, su fahimci daga murya ba zai sanya ya daina ba, amma ta hanyar amfani da lafazi mai taushi sai ta sa zuciyar miji ta yi sanyi har ya yi nadamar abin da ya aikata, ya bada hakuri, sannan farin ciki ya wanzu a tsakanin ma’auratan.

*9-Tausayi*: 
Idan mata suka rika tausaya wa mijinsu musamman mijin da yake shan wahala wajen nemo cefane, to zai rika jin farin ciki. Kada ya fita ya samo abin da za a ci da kyar amma ku rika kushewa ko korafi a kai, ku rika cewa gidansu wance abinci sai an ture, ko kuma kowane wata sai ya yi mata dinki. Mata su fahimci kowa da karfinsa. Tausaya wa miji wani sinadari ne da zai sanya miji cikin farin ciki.


*10-Iya Girki*
Wata hanya mai matukar muhimmanci da mata za su faranta wa mijinsu ita ce, wajen iya girki. Akwai wani abokina ya ce dalilin da ya yake kara son matarsa shi ne, yadda ta kware wajen iya girki iri-iri. Idan mata suka iya girki za su samu wata daraja ta musamman a wurin mijinsu, zai kuma rika jin farin ciki, domin duk wahalar da ya sha wajen yin cafane ya san kwalliya za ta biya kudin sabulu. Idan mata ba su iya girki ba ya kamata su koya, kada su tsaya a salon girki iri daya kawai, hakan zai gunduri mijinsu, har ya rika korafi, inda maimakon samun farin ciki sai ya rika jin haushi.

A karshe ina fata mata za su bi wadannan hanyoyin don faranta wa mijinsu. 

Allah Ya taimake mu, amin.

Post a Comment (0)