AN GAISHE DA EL-RUFA'I

An Gaishe Ka Namijin Duniya, Gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i

Daga Imam Murtadha Gusau

Talata, 24/09/2019

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin kai

Assalamu Alaikum

Ya ku 'yan uwana 'yan Najeriya masu girma, masu daraja! Wallahi, Allah ya sani, kuma shine shaida, na dade ina kwakkwaran bincike da kuma bibiyar ayukka da tsare-tsare, da salon mulki irin na gwamnatin jihar Kaduna, karkashin jagorancin mai girma adalin gwamna, masoyin talakawa, mai kaunar kawo canji na gaskiya a cikin al'ummah, wato Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i; sai daga karshe sakamakon bincike na ya tabbatar mani da cewa, lallai wannan mutum alkhairi yake nufi ga jihar sa ta Kaduna da kuma kasar nan baki daya. Na gano cewa wannan gwamna wallahi, wallahi, wallahi, talaka ne a gaban sa ba aljihun sa ba, kuma na gano, burin sa shine, yaya za'a yi a gyara tsarin kasar nan, ta dawo kamar yadda ake tafiya a can da, ya zamanto babu banbanci tsakanin dan mai kudi da dan talaka; tsakanin 'ya 'yan masu mulki da 'ya 'yan wadanda ake mulka.

Ya ku bayin Allah! A kasar nan ta mu mai albarka Najeriya, mun dade muna ta kiraye-kiraye zuwa ga gwamnati da dukkanin wani mai ruwa da tsaki a harkar ilimin kasar, cewa, wallahi idan ana so ilimin kasar nan ya gyaru, ya koma mai inganci kamar can da, inda da dan Sarki da dan gwamna da dan attajiri duk ajin su daya, to sai an cire son zuciya, ya zamanto an rusa duk wani tsari na makarantu masu zaman kan su (private schools), ko kuma a rage yawan su, abar masu inganci daga cikin su, sannan ya zamanto duk wani mai hali, da 'yan siyasa, da manyan jami'an gwmnatoci, da sarakuna duk su kai 'ya 'yan su makarantun gwamnati tare da 'ya 'yan talakawa, kamar yadda tsarin karatu yake a can da. Wannan hanyar ce kadai idan Allah ya taimake mu, sai tsarin ilimin mu ya gyaru. Amma matukar aka ce makarantun 'ya 'yan manya daban, na 'ya 'yan talakawa daban, to wallahi har abada harkar ilimin mu ba za ya taba gyaruwa ba, wannan ita ce gaskiyar magana.

Idan zamu tuna a shekarar 2015, lokacin da ake Kamfen din neman kuri'un talakawa, gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i ya dau alkawari, ya bayyana cewa idan Allah yasa yaci nasara, zai sa dan sa a makarantar gwamnati tare da 'ya 'yan talakawa.

Tun a wancan lokacin 'yan adawa da sauran jama'ah suke ta ganin cewa gwamna El-Rufa'i ya fada ne kawai amma sam ba zai iya yin haka ba, saboda lalacewar makarantun gwamnati a kasar nan.

Sai ga shi jiya litinin, 23 ga watan Satumba 2019, a lokacin da aka bude makarantu, bayan hutun karshen zango da aka tafi, mai girma gwamna El-Rufa'i ya ba mara da kunya, ya cika akakawari, ya garzaya da dan sa na cikin sa, Abubakar Al-Sadiq mai shekaru shida (6), zuwa makarantar gwamnati ta Kapital School da ke Kaduna, kamar yadda yayi alkawari a can baya, a inda aka yi masa rajistar shiga aji daya; kuma yayi kira ga sauran jami’an gwamnati da 'yan siyasa da su yi koyi da shi, su sa 'ya’yan su a makarantun gwamnati kamar yadda yayi, domin ta nan ne kadai hanyar da 'yan siyasa da hukumomi za su bi suyi hobbasa domin inganta ilimi.

Sannan kamar yadda kowa ya sani ne, tun bayan hawan gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i kujerar mulkin Kaduna ya fara aiki tukuru wajen ganin cewa ya gyara makarantun jihar, wanda a halin yanzu aka kusa kammalawa da yardar Allah.

Sanadiyyar kokarin sa, an samu karin dalibai masu shiga makarantu a fadin jihar, da kuma karin daukar malamai kwararru da yayi.

Da wannan ne nike cewa a gaskiya Allah ya taimaki jama'ar jihar Kaduna da zakakurin shugaba, jarumi, kuma adali, mai kishin talakawan sa. Ina rokon Allah yaci gaba da taimakon sa, da yi masa jagora, akan irin wadannan namijin kokari da yake yi wa jjhar sa, sannan ina rokon Allah ya ba shi ikon dare wa kan karagar mulkin Najeriya baki daya, domin irin wadannan shugabannin ne kasar nan ta ke bukata a halin yanzu; wadanda za su sa gaba wurin ganin talakawa sun ji dadi. Allah ya taimake shi, yayi masa jagora, amin.

Ya ku 'yan uwana! Idan za ku iya tunawa, a shekarun baya, mutanen jihar Kaduna sun fada cikin rudani sanadiyyar yawan barkewar rikice-rikice da tashe-tashen hankula a jihar, musamman a wurare irin su Kasuwar Magani da sauran su; rikicin da yake yin sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama da kuma dukiyoyin su; sannan ga garkuwa da ake yi da mutane domin karbar kudin fansa, ga rashin zaman lafiya da aka yi fama dashi a fadin jihar, wanda yasa mutane da dama sun fada cikin dimuwa da fargaba a wadancan lokuttan.

Cikin taimakon Allah, mai girma gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i, ya tashi tsaye haikan, da yake Allah ya dubi kyakkyawar niyyar sa, sai ya taimake shi, ya kawo karshen wadannan rikice-rikice.

Sanadiyyar Allah ya azurta jihar Kaduna da jarumin gwamna, marar tsoro, wanda ya kasa zaune ya kasa tsaye don ganin rikici a jihar bai fi karfin gwamnati ba kamar yadda yakan faru a da can baya, da sai an yi dimbin kashe-kashe, an kona gidaje da dakunan Ibadah kafin a kawo wa mutane dauki, wannan karon gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i yayi namijin kokari da tsayuwar daka, wurin ganin hakan bai sake faruwa ba da ikon Allah da taimakon sa.

Da kansa ya rika fita titunan jihar, kwararo-kwararo, sako-sako, lungu-lungu, kauye-kauye, karkara-karkara yana kokarin tabbatar da ganin ana bin doka da oda, sannan kuma mutane basu dauki hukunci da doka a hannun su ba.

Ya ku 'yan Najeriya! Lallai, babu shakka, irin wannan salon gudanar da mulki irin na mai girma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i, ya nuna cewa, shi ya cika gwani kuma abin alfaharin kowa, duba da yadda ya tabbatar da cewa, ya zama zakaran gwajin dafi cikin takwarorin sa gwamnoni, kuma garkuwa ga al'ummar sa ta jihar Kaduna.

Tun bayan rantsar da shi a karon farko, da shigar sa Ofis, a shekarar 2015, a matsayin zababben gwamnan jihar Kaduna, karkashin tutar jam'iyyar APC, Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i ya tarar da jihar cikin kangin fatara da talauci gami da tabarbarewar al'amurran tsaro, da na ilimi, hadi da kiwon lafiya, biyo bayan kura-kurai da tabargazar da gwamnatocin baya suka tafka. Amma cikin hanzari da himma, mai girma gwamna ya sanya kaimi domin magance dukkan matsalolin da suke addabar jihar.

Cikin wadannan shekaru, duk wanda yasan Kaduna, wallahi yasan cewa mai girma gwamna ya samu gagarumar nasarar ciyar da jihar Kaduna gaba ta fannoni daban-daban, sai fa idan mutum ya kasance shi dan adawar siyasa ne, to anan irin wadannan kuwa ba za su taba ganin gaskiya ba balle har su bi ta. Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i ya bayar da gudummawa sosai a wurare da dama, misali:

1. Fannin Tsaro

2. Fannin Ilimi

3. Fannin Tattalin Arziki

4. Fannin Kiwon Lafiya

5. Fannin Siyasa

6. Rikicin Fulani Da Makiyaya da sauran su.

Haka zalika, duba da nagartar sa, da kuma irin ayyukan alkhairin da ya shuka a jihar sa, yasa mai girma shugaban kasa, Alhaji Muhammadu Buhari ziyartar jihar sau da dama domin kaddamar da ayukka tare kuma da yaba masa kan yadda yake kokari wurin tabbatar da zaman lafiya da hadin kan 'yan jihar.

Duk wadannan batutuwa, kadan ne na zazzakulo maku daga kowane fanni da mai girma gwamna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i ya tabo cikin shekarun da yayi yana jan ragamar mulkin jihar Kaduna. Domin wannan shafi yayi kadan matuka wurin iya zayyano komai a cikin lokaci guda.

Shakka babu, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i ya cika jarumi kuma gwarzon namiji, kuma ya cika shugaba nagari abin koyi. Don haka ina ganin ya zama dole in yaba wa wannan jajirtacce, gwani, zakaran gwajin dafi cikin takwarorin sa gwamnoni, kuma abin alfaharin talaka, wanda ya cancanci ya jagoranci kasar nan zuwa tudun-mun-tsira da yardar Allah!

Duba da wannan, yasa nike ganin cancantar 'yan Najeriya su tashi tsaye gaba dayan su, da rokon Allah da addu'o'i, domin ganin cewa Allah yasa wannan bawan Allah ya zama shugaban kasar Najeriya, domin kowa yaji dadi, ya amfana! Ya Allah ka amsa muna, amin.

Wassalamu Alaikum,

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za'a iya samun sa ta adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma 08038289761.

Post a Comment (0)