*RAYUWAR ƘABARI*
*Rubutu na 1*
بسم الله الرحمن الرحيم
Da hantsi (kusan ƙarfe 10: 00 na safe) a ranar Lahadi 24/Zul-Hijjah/1440 (25/8/2019) ne na gabatar da wa’azi ga taron mata: Tsofaffi da dattijai da matan aure da yaran mata mai taken: *Rayuwar Ƙabari* , a babban masallacin Jumma’a da ke cikin garinmu: Zangon Katab.
Bayan kammala darasin ne aka gabatar da tambayoyin da suka rubuto, waɗanda kuma na bayar da amsoshinsu a taƙaice.
To, bayan gama karatu littafin: *RAYUWAR ƘABARI* a nan, sai na ga ya dace in sake kawo tambayoyin da amsoshin. Me yiwuwa su yi amfani ga sauran jama’a, _wal Laahu A'lam:_
*T1- Menene hukuncin wanda ke haɗa mutane faɗa?*
*A1-* Haram yake yi, saboda dalilai masu yawa kamar haka:
1. A rayuwar nan babu mai ƙaunarsa ko son zama da shi a cikin al’umma, muddin dai aka gano shi.
2. Yana da matsanancin azaba a cikin ƙabarinsa a bayan mutuwarsa, kamar yadda hadisin nan sahihi na matar da Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya tarar da ita tana kuka a jikin ƙabarin ɗanta ya nuna.
3. A ranar Ƙiyama kuma ba zai shiga Aljannah ba, kamar yadda wani hadisin sahihi ya nuna!
Watau: Ba zai shiga a karon farko ba, ko ba zai shiga tare da mutanen kirki ba, har sai an gama horar da shi da azabtar da shi! Allaah ya tsare mu.
4. Wajibi abin da ke kansa shi ne, ya yi gaggawar tuba ga Allaah Ta'aala daga wannan mummunar ɗabi'a, tare da kulawa da sharuɗɗan tuban, kamar yadda malamai suka ambata.
5. Sannan kuma lallai ya nemi waɗanda ya cutar da su ta dalilin wannan mummunan aikin, da su yafe masa, kafin zuwan mutuwarsa.
Allaah Ta'aala ya yafe mana kura-kuranmu.
_Bari mu dakata a nan, mu saurari zuwan Tambata ta 2._
Daga: USTAZU ABDULLAH MOHAMMAD IBRAHIM.