🍀 *KARKI BIJIREWA MAI KYUTATA MIKI* 🍀
🍀Idan kika samu MIJI mai kula da ke kuma yana cika miki haqqoqinki yadda yakamata, to ki godewa Allah, kuma ki rikeshi kataman da hannu biyu.
🍀Saboda idan har kika bijirewa kyuatatawar da yake miki, kikayi butulci, to fa kisani akwai 10 irinki a waje da kuma 40 wadanda suka fiki komai, duk suna nan suna jiranshi yashigo da su dakinki.
🍀Idan kinyi Sa'a ahadaku idan kuma akasin haka sai kuma kiyi waje , abaki Red Card. Allah yakiyaye.
🍀Kirika duba makomarsu mana, wasu fa irin yadda kikeyiwa mijinki haka sukayiwa nasu, da tunanin cewa: ai idan ma sun fita akwai masu jiransu.
🍀Shaidan yayi musu alkawarin bogi, kuma akarshe suka kare ahaka babu wanda ya shinshina su balle adaukesu, gararanbar dai kawai suke tayi, da kuma yin bara a kufai.
🍀Matukar kin godewa Allah, to Allah zai kara miki jim dadi doriya akan wanda kike kai, ku ma duk wanda bai godewa kadan ba ko anbashi mai yawa ma bazai gode ba.
🍀 Akarshe dai duk wanda bai godewa Mutane akan kyautatawar da Sukeyi masa ba, babu yadda za'ayi kuma yagodewa Allah. karshen butulci kenan, mutum yaki godema Allah.
*GANI GA WANE....*
*IDAN KUNNE YA JI....*
Allah yasa mudace kuma yakara gyara tsakanin ma'auratannmu.
✍🏻 Rubutawa
*Idris M Rismawy*
Rismawy86@gmail.com