ILLOLIN ZINA, LUWAƊI DA MAƊIGO 2


*02→ILLOLIN ZINA ,LUWADI DA MADIGO*

*Hukuncin zina:*

Zina haramun ce a addinin Musulunci. Allah Madaukakin Sarki Ya haramta ta inda Yake cewa : “Kada ku kusanci zina, domin ita alfasha ce kuma tafarki ne mummuna.” (Isra’i:32).
Malamai suna cewa, fadin Allah “kada ku kusanci zina,” kai matuka ne wajen hana ta, don ya fi a ce “kada ku yi zina.”
Sheikh Abdur-Rahman Assa’idiy yana cewa: “Hani ga a kusanci zina ya fi kai matuka a kan hana yin ta, saboda cewa kada a kusance ta ya hada hana dukkan yin abubuwan da suke gabatar ta kuma suke kawo yin ta, domin kuwa duk wanda ya yi kiwo a gefen shinge, to ko yana daf da fadawa cikinsa, musamman ma a kan irin wannan lamari, wanda da yawa daga cikin zukata suna dauke da abin da yake sawa a afka masa. 


Sannan Allah Ya siffata zina da cewa alfasha ce. Ma’ana zina wata aba ce da shari’a da hankali suke ganin muninta, saboda keta alfarmar Ubangiji ce da shiga hakkin macen da hakkin danginta da mijinta, kuma bata wa miji shimfidarsa ne da cakuda dangantaka da makamancin haka.” (Tafsirin Assa’idiy).
A wani wurin a cikin Alkur’ani Mai girma, Allah Madaukakin Sarki Ya siffata bayinsa muminai da cewa su ne wadanda ba sa zina, inda Ya ce, “Wadanda ba sa kira ko bauta wa wani tare da Allah; ba sa kashe rai da Allah Ya haramta sai da hakki; kuma ba sa zina, duk wanda ya aikata haka zai gamu da azaba.” (Alfurkan: 78). 


Ya tabbata a cikin Hadisi an tambayi Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) a kan wane zunubi ne ya fi girma, sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Shirka da Allah alhali Shi ne Ya halicce ka.” Sai aka ce, ‘sai wanne?’ Sai ya ce, “Sannan kashe danka don kada ya ci tare da kai.” Sai aka ce, ‘Sannan sai wanne?’ Sai ya ce, “Ka yi zina da matar makwabcinka.” (Buhari). 
Allah Madaukakin Sarki Ya sanya hukuncin wanda duk ya yi zina kuma ya taba aure, a jefe shi, namiji ko mace; idan kuwa bai taba aure ba, sai a yi masa bulala dari, sannan a bakuntar da shi a wani gari daban tsawon shekara guda (ma’ana a daure shi a kurkuku).
Duk wanda ya kalli hukuncin zina, zai ga Allah Ya kebance shi da wasu abubuwa masu yawa, saboda munin zina. Ga kadan daga cikin abubuwan da hukuncin ya kunsa:

• Kausasawa wajen ukubar mazinaci, ta hanyar jefewa. Ko kuma bulala da bakuntarwa shekara guda.

• Hana jin tausayin mazinaci ko mazinaciya yayin da ake musu ukuba. Allah Ya ce: “Mazinaciya da mazinaci ku yi wa kowane daya daga cikinsu bulala dari. Kada ku ji tausayinsu a cikin addinin Allah, in dai kun yi imani da Allah da Ranar karshe.” (Annur:2). 
 

• Yi musu ukuba a gaban mutane. Ba a yarda a yi musu a boye ba. Allah Ya ce: “Wasu bangare na muminai su halarci wajen yi musu ukuba (haddi).” (Annur:2).
Duk wadannan abubuwa suna nuna mana munin zina da rashin kyanta a Musulunci. Imam Buhari ya kawo a cikin ingantaccen littafinsa daga Maimun Al’audiy ya ce, “A lokacin Jahiliyya na taba ganin wani biri da ya yi zina da wata biranya, sai sauran biran suka taru suka jefe su.”
Mafi munin zina ita ce wadda mutum zai yi da mahaifiyarsa; sai da muharramarsa; sai wadda zai yi da mata (ko ’yar) makwabcinsa. Allah Ya kare mu.


Zamu kwana a nan, a dakacemu 

Rubutawa:- Dr, Muhammad Rabi’u Umar Rijiyar Lemo, 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Post a Comment (0)