WANKAN TSARKI DA KITSO NA ULU



WANKAN TSARKI DA KITSO NA ULU

https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

*TAMBAYA*❓

_Assalamu Alaikum._
Malam don Allaah, ina da tambaya.
Wai kitson zare na ulu wanda aka yi Ζ™ari yana wankan tsarki?

*AMSA*πŸ‘‡

_W alkm slm w rhmt laah._

1. A cikin Hadisin Abu-Hurairah _(Radiyal Laahu Anhu)_ wanda Al-Imaam Muslim _(Rahimahul Laah)_ ya fitar da shi, Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya yi bayanin siffofin waΙ—ansu mata 'yan wuta daga cikin al'ummarsa, waΙ—anda kuma ko Ζ™anshin Aljannah ma ba za su ji ba, balle ma su shiga cikinta. Ya ce:
 *ο»­َο»§ِοΊ΄َοΊŽοΊ€ٌ ο»›َﺎﺳِο»΄َοΊŽοΊ•ٌ ο»‹َﺎﺭِο»³َοΊŽοΊ•ٌ ، ﻣَοΊŽοΊ‹ِο» َοΊŽοΊ•ٌ ﻣُﻀِο»΄ο» َοΊŽοΊ•ٌ ، οΊ­ُοΊ…ُο»­οΊ³ُﻬُﻦَّ ο»›َοΊ„َοΊ³ْﻨِﻀَοΊ”ِ ﺍﻟْοΊ’ُοΊ¨ْοΊ–ِ ﺍﻟْﻀَοΊŽοΊ‹ِο» َοΊ”ِ*
*Da waΙ—ansu mata masu sanye da tufafi amma kuma suna tsirara! Karkatattu, masu karkatarwa! Kawunansu kamar tozayen raΖ™umma karkatattu!*

2. A wurin sharhi da Ζ™arin bayani a kan siffar ' *kawunansu kamar tozayen raΖ™umma'* sai malamai irinsu Al-Imaam An-Nawawiy _(Rahimahul Laah)_ suka ce:
Suna girmama girman kawunan nasu ne ta hanyar nannaΙ—a manyan rawunna, ko cukwikwiya tsummokara da makamantansu a kawunan nasu, har sai sun yi kamar tozayen raΖ™umma!

. Daga nan muke 3fahimtar cewa:
Matsalar yin kitso, ko yin ‘ _attachment’_ da zaren ulu ba Ζ™aramar matsala ba ce. Domin tana da alaΖ™a mai Ζ™arfi wurin hana mai yinsa samun kusanta, balle ma shiga Gidan Aljannah a Lahira!

4. Don haka, mas'alar ta fi Ζ™arfin maganar halacci ko rashin halaccin yin wankan tsarki da shi. Haka kuma maganar ta wuce batun irin abin da aka maΖ™ala a cikin gashin: Ko ulu ne, ko gashin mutum ne, ko na dabba, ko na tsuntsu, ko kuma tsumma ne kawai, da sauransu!

5. Amma game da wankan tsarki, a zance mafi inganci a wurin malamai: Akwai babbar matsala, idan aka Ζ™yale mai _‘attachment’_ ta cigaba da yin wankan tsarki da su a kanta.
Domin tun da dai ana umurtan wacce ba ta sanya irin wannan abin a kanta ba da ta warware kitson gashin kanta a wurin wankan haila (ban da na janaba), a zance mafi Ζ™arfi a wurin malamai, wannan ya nuna lallai ita ma da ta yi wannan Ζ™arin a kanta, lallai sai ta warware shi, a wurin wankan tsarki (haila ko nifasi).

_Wal Laahu A'lam._

*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyarπŸ‘‡
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on FacebookπŸ–•

2 Comments

Post a Comment