MATA KU NISANCI WANNAN HALI SABODA MUNINSA
*Sanya turaren da kamshinsa yake tashi wanda ake jin kamshinsa daga nesa,lokacin fita daga gida dan aji kamshinsa*.
Manzon Allah ﷺ yana cewa;
*(Idan mace ta sanya Turare sai ta wuce wajan mutane dan su ji kamshin wannan turaren,to Mazinaciyace)*
@ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ - ﺭﻗﻢ :( 323 )
Manzon Allah ﷺ yana cewa;
*(Wannan yana cikin mazinaciya,Mace idan ta sanya turare sai ta wuce wajan zaman mutane dan suji kamshi,to Mazinaciyace)*
@ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ - ﺭﻗﻢ :( 4540 )
ﺍﻟﻤﻨﺎﻭﻱ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ
Yana cewa:
"Abin da ake nufi da ita Mazinaciyace,saboda ta aikata abinda sanadiyyarsa yana yada zina tsakanin al'umma,domin babu abinda yake saurin jan hankali da motsa sha'awa har ya kai zuwa ga haka kamar sanya turare mai yada kamshi......... "
@ﻓﻴﺾ ﺍﻟﻘﺪﻳﺮ : ( 1/355)
Manzon Allah ﷺ yana cewa;
*(Dukkan matar da ta sanya turare to kada ta halarci sallar Isha'i tare da mu)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ - ﺭﻗﻢ : ( 444 )
Idan har Manzon Allah ﷺ ya hana macen da ta sanya turare zuwa Masallaci dan kada wani yaji kamshen turarenta,a hana mata su sanya turare lokacin fita kasuwa da wajan chakuduwa maza da mata da wucewa wajan zama na maza shi girman tsanin hani sosai.
*Turaren Mata kala Biyune*
1-Na farko
*Shine na sanyawa agida dan gyaran aure da kyautatawa mijinta,shine turare mai kamshi sosai wanda za'aji kamshinsa tun daga nesa,to irin wannan turare haramunne mace ta sanya shi ta fita waje,zata sanya a cikin gida dan mijinta,idan kuma ta sanya ta fita to Mazinaciyace ko tana yada zina kamar yanda Manzon Allah ﷺ ya fada*
2-Na biyu;
*Shine turaren jiki wanda ake shafawa ko fesawa amma kamshinsa baya ta shi sai anzo kusa da mace ake jin kamshinsa,to wannan ya halasta ga mace ta sanya agida da lokacin fita kuma baya cikin hanin da Manzon Allah ﷺ yayi,saboda ba'ajin kamshinsa yana tashi*.
Allah ne mafi sani.
*Allah ka sanya mata iyayen mu su gyara wannan hali marar kyau kuma ka gafarta masu zunubansu baki daya*.