NA DAƊE DA FAHIMTAR HAKAN 02

NA DAƊE DA FAHIMTAR HAKAN 02

Kamar yadda na faɗa a baya, tabbas kowa na da alaka da jarumin da yake so, ko dai a bayyane ko kuma a sirrance. Akwai mutanen da suke son wasu jarumai kaɗai saboda suna da ban dariya, misali; Johnny Lever, M.S Narayana da kuma Brahmanandam duk sun yi suna a wajen jama'a saboda sun iya bada dariya.

Haka nan kuma, sau tari akan samu wasu gungun mutane kuma waɗanda su kuma Zunzurutun muguntar Jarumi ce ke sa suji suna son shi, ko da kuwa ace su ba mugaye bane a fili. Misali; Amrish Puri, Danny da Prakash Raj duk sun yi ƙaurin suna ta yadda wani ma saboda su Kawai yana iya zuwa ya kalli fim duk da cewa a matsayin azzalumai suke fitowa.

Hallau kuma dai akwai mutanen da su suna son ganin fim ɗin tausayi da shiga mawuyacin hali a rayuwa, to suma suna da irin nasu Jaruman da suke liƙewa.

To kasancewar ita baiwar Allaah tana da yawa, a wasu lokutan sai ka iske Jarumi guda ɗaya ya ƙware a wajen iya abubuwa biyu, uku ko sama da haka waɗanda duk in ya hau yana yin su daidai, hakan ke sa Masoyan waɗannan abubuwan su ji suna sonsa, hakan kuma shi ke sa Aga Jarumi ya tattara masoya da yawa. Misali; Jarumi Hrithik Roshan ya iya rawa, ya iya Kafce kuma ya iya dambe, hakan tasa yana fitowa nan da nan ya samu karɓuwa saboda masu son irin waɗannan abubuwa suna da yawa, kuma a da suna samun su ne kawai a wajen Mabanbantan jarumai yanzu kuma sai gashi sun same su a waje guda.

Misali na gaba kuma shi ne, Shah Rukh Khan. Srk Jarumi ne da maganar gaskiya ba wai don shi ne Jarumi na ba ya iya abubuwa da yawa, ya iya mugunta, ya iya ban tausayi, ya iya ban dariya, ya iya Kafce sannan kuma ya iya soyayya, duniya ma ta san da haka, a taƙaice dai, da wuya a samu wani mutum mai kallon Fina-Finan Indiya da zai ce srk bai taɓa taɓa masa zuciya ba tun da ya fara Fina Finansa, ban ce babu ba, amma da wahala. Kuma wannan dalili yasa Masoyan srk suke da yawa a duniya.

To idan mun fahimci wannan, akwai kuma wasu Jaruman da sun ƙware a wani waje, amma in an je wani wajen ma babu laifi nan ma suna ɗan taɓukawa. Misali; Salman Khan Jarumi ne da ya iya suburbuɗa na gaban kwatance babu ja, kuma ya iya soyayya da Kafce, amma bai iya rawa ba, sai dai kuma hakan baya hana shi taɓuka abin arziki idan ya hau filin rawa, bai iya bada dariya ba, amma da wuya yayi abin ban dariya baka yi dariyar ba.

Zan ci gaba In Shaa Allaah 

<••••••••••••••••••••••••••••>
  ɧãımãŋ Kɧâŋ Řâééʂ <••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com


Post a Comment (0)