UBAN GIDA NA
Aminu Ladan Abubakar Alan WaΖa
Uban gida na da zaka Ιauki zance na, Aradu Allaah da ka haye hasashena x2
In banda bautar zuciya da bata tserarwa,
Ya za na tara abincin da bani cinyewa?
Ya za na gina gida wanda ba shi Ιorewa?
Ya za na tara Tufafin da bani sanyawa?
Ya za na dasa hasashen da ba shi Ιorewa?
Ya za na shimfiΙa daula da bata Ιorewa?
Ya za na Ιaura majanyin da za ya suncewa?
Uban gida na da zaka Ιauki zance na, da kayi gyara kafin a gincire kwana...
Uban gida na da zaka Ιauki zance na, Aradu Allaah da ka haye hasashena
Iyye... In banda bautar zuciya da ke halakarwa,
Abin hawa na ya zarce na hawan kowa
Rigar sakawa ta zarce ta jikin kowa
Gami da takalma sun fi na Ζafar kowa
Dangi agogona ya fuce na gun kowa
Daidai da zobena yafi hasashen kowa
Hatta da birona alΖalam na zanawa
Uban gida na da zaka Ιauki zance na, wallahi da an gyara da tsakiyar rana...
Uban gida na da zaka Ιauki zance na, Aradu Allaah da ka haye hasashena
Hmm... Gida dubu na gina tanadin wajen kwana
Ciki da falo dubbai daban-daban Ιana
Don tanadi na talauci da ke tsumin rana
Sannan in kaucewa idanduna da ke bina
In Ιadda sawayena ga masu biko na
An Ιauki duniya mai tabbata gidan kwana
Gida ga mai burin rayuwa gidan Ζuna
Ya mai gida na da zaka duba zance na, wallahi Allaah da ka cikan Muradina..
Uban gida na da zaka Ιauki zance na, Aradu Allaah da ka haye hasashena
Iyye... Mun zama bayi na ciki da ba shi turewa
Muna haΖa ya na mai rijiya da babu ruwa
Muna nutsewa Ζasa zuciya tana Ζwawa
Muna ta bautar gangar jikinmu ba Ζiwa
Muna biye al'aura muna Tsiyacewa
Giya ta rai ta sanya mu Ζara ruΙewa
Ina tunani da sani da ke a ΖwaΖwalwa?
Uwargidana da kin fahimci zance na, wallahi Allaah da an rufe tunanina...
Uban gida na da zaka Ιauki zance na, Aradu Allaah da ka haye hasashena
Ni zuciyata kuma ta hanani yin barci
Dare da rana kuma ba ragi na sassauci
Tana ta kakabi ko abinci bata ci
Cikinta mamaki ya game ta ga Ζunci
Sannan tunani yayi tarnaΖi gadon barci
Ina ta mamaki kan hali na zalunci
BaΖin maciji da ake kira da Kumurci
Uban gida na bisa ΖarΖashin tunanina, ya fi mu jin gantsar nasa a tunanina...
Uban gida na da zaka Ιauki zance na, Aradu Allaah da ka haye hasashena
Duk inda ka ga Ζasa country a Ilimina
To arzikin da buwayi ya basu dangina
Ya zarce dukka buΖatu nasu da an tona
Sai dai idan jagoransu ya zamo Ιauna
Sai babu adalci gunsu shugabannina
Idan da adalci babu mai shiga rana
Kowansu ya zarce wajibinsa dangina
Ya shugabana in an nazar a zance na, wallahi Allaah Ya tseratar da mu Ζuna...
Uban gida na da zaka Ιauki zance na, Aradu Allaah da ka haye hasashena
Hannunka mai sanda yau nake iyayena
Nuni da NishaΙi ne nake wa babana
Yau gyara kayanka ba shi maida mu rana
Ya shugabana in har ka Ιauki zance na
Abinda ka tara ka aje gidan kwana
Da wanda ka yi bushasha kake tsumin Ζauna
To wanda ka bayar za shi yayi ma rana
Uban gida na in yanzu kaga laifi na, ai zaka gane ran tsai da mu cikin rana...
Uban gida na da zaka Ιauki zance na, Aradu Allaah da ka haye hasashena
Ku taimaka mini gun dakatar da kuka na
Don kar na Ζarar da ruwan cikin idanuna
Suna da rana a gaba zubar hawaye na
Wai shin ko ruhi da jiki da hankali Ιana
Sun yarda ranar tsayuwa tana tsumin kwana?
Wai shin ko labari na wuta da Aljannah
Anya bani adama ya aminta ko Ιana?
Ya shugabana da ka amince zance na, me za ya ruΙe ka da handama tsakar rana...
Ubangijina Afuwar Ka ni nake nema....
Ubangijina gafarar Ka ni nake nema
Ubangijina Afuwar Ka mu muke nema
Ubangijina sauΖin Ka ne abin nema
Ubangijina Rahamar Ka mu muke nema
Ubangijina gafarar Ka mu muke nema
Ubangijina Ceton Ka mu muke nema...
Uban gida na da zaka Ιauki zance na, Aradu Allaah da ka haye hasashena X2
