SHARHIN FIM ƊIN CAPTAIN AMERICA: CIVIL WAR
* Bada Umarni - Anthony Russo/Joe Russo
* Ɗaukar Nauyi - Kevin Feige
* Rubutawa Da Tsarawa - Christopher Markus/Stephen McFeely
Captain America: Civil War fim ɗin jarumta ne da aka fitar da shi a cikin shekara ta 2016 a Ƙasar Amurka. Labarin fim ɗin ya samo asali ne daga littattafan almara mai suna Captain America wanda Joe Simon da Jack Kirby suka wallafa a ƙarƙashin kamfanin Marvel Comics. Kamfanin Marvel Studios ne ya shirya fim ɗin, Yayinda Kamfanin Walt Disney Motion Pictures ya rarrabashi.
Fim ɗin shi ne na ukun Captain America: The First Avenger (2011) da kuma
Captain America: The Winter Soldier (2014),Sannan kuma shi ne Fim na goma sha uku daga cikin Fina Finan Duniyar Marvel mai suna Marvel Cinematic Universe (MCU).
An fara ɗaukar wannan Fim ne a cikin watan Afrilu 2015 a
Pinewood Atlanta Studios da ke Fayette County, Georgia, Sannan aka ci gaba a Metro Atlanta Yayinda aka ƙarƙare a Ƙasar Germany cikin watan Agusta 2015.
An fara haska Captain America: Civil War ne a birnin Los Angeles a ranar 12 ga watan Afrilu 2016, sannan aka sake shi a Ko'ina cikin Ƙasar Amurka a ranar 6 ga watan Mayu 2016 a cikin zubin 3D da IMAX 3D. Fim ɗin ya samu yabo da kasuwa sosai, domin ya kawo maƙudan kuɗaɗe Kimanin Dala Biliyan $1.1 a harkar Kasuwancin Fina-Finan duniya baki ɗaya.
Bugu da ƙari, an yabawa Kafcen Jaruman Fim ɗin (musamman Evans da Downey), sannan kuma an yabi labari, jigo, faɗa da kuma umurnin Fim ɗin. Fim ɗin shi ne Fim ɗin da yafi kowanne kawo kuɗi a 2016, har ila yau kuma dai shi ne Fim na goma sha biyu daga cikin Fina-Finan da suka fi kowanne kawo kuɗi a duniya baki ɗaya a wancan lokacin.
Fim ɗin ya fara ne da nuna mana Bucky Barnes a shekara ta 1991, inda bayan an juyar masa da tunani sai aka fito da shi daga wani Sansanin Hydra da ke Siberia domin ya tsare waɗansu mutane da ke tafiya a mota ɗauke da wata Allura.
A yanzu kuma, bayan shekara ɗaya da kawo ƙarshen Ultron a birnin Sokovia da tawagar Avengers suka yi, sai Steve Rogers, Natasha Romanoff , Sam Wilson , da Wanda Maximoff suka tafi birnin Lagos da ke Nijeriya domin su dakatar da Brock Rumlow daga satar wani Makamin ƙare-dangi. Bayan sun yi artabu, sai Rumlow ya kunnawa kansa wutar bam domin ya kashe Rogers, amma sai Maximoff tayi amfani da ƙarfin tsafinta wajen ɗauke tartsatsin wutar da ya tashi ta jefa shi sama, hakan ya jawo rugujewar wani gini da ke kusa da su.
Mutane da yawa sun mutu a Sanadiyyar wannan wuta, ciki harda wasu mutanen Ƙasar Wakanda waɗanda suka zo aikin agaji a wajen. Sakataren Gida na Amurka Thaddeus Ross ya bayyanawa tawagar ta Avengers cewa Ƙungiyar haɗa kan ƙasashen Duniya (UN) tana Shirin Samar da wata doka wacce zata baiwa Ƙungiyar damar kafa cibiya ta musamman wacce zata dinga kula da tawagar. Hakan ne ya jawo rarrabuwar kawunan Membobin tawagar.
Shi dai Tony Stark ya amince da hakan saboda gudunmuwar da ya bayar wajen ƙirƙiro Ultron da kuma Bala'in da ya faɗowa Sokovia a Sanadiyyar hakan. Amma shi Rogers yafi aminta ne da hukuncin da ya yanke da kansa fiye da wanda gwamnati zata yanke. Ana cikin haka ne kuma, sai Helmut Zemo ya gano wanda ke lura da Barnes ya kashe shi, sannan ya sace littafin da ke ɗauke da kalmomin da in an furta su za'a juyar masa da tunani.
Yayin da aka je wani taro a Vienna domin ƙaddamar da wannan doka da za'a sanyawa tawagar Avengers, sai bam ya tashi inda har yayi Sanadiyyar mutuwar Sarkin Wakanda wato T'Chaka. Wasu Na'urorin tsaro da aka bincika sun bayyana Barnes a matsayin wanda yayi kisan. Hakan yasa yariman Wakanda wato T'Challa ya sha alwashin ganin bayan sa.
Rogers sai ya yanke shawarar shi zai kawo Barnes domin abokin sa ne, kuma abokin fita yaƙin sa. Rogers da Wilson sun samu damar gano inda Barnes yake a Bucharest inda suka yi Yunƙurin kare shi daga T'Challa da kuma Hukuma, sai dai dukkansu su huɗun an kama su harda T'Challa.
Helmut Zemo sai yazo a matsayin likitan Mahaukatan da zai yi gani da Barnes, a nan Zemo ya karanto waɗannan kalmomi domin ya sa Barnes yayi masa biyayya. Bayan yayi masa wasu ƴan tambayoyi, sai ya sashi kaiwa kowa dake wajen hari Yayinda shi kuma ya gudu.
Yayinda Barnes ya dawo hayyacin sa, sai ya bayyanawa Rogers cewa Zemo shi ne asalin wanda ya kai harin Vienna, kuma yana neman wani waje ne da aka ajiye sauran sojoji irin sa a ɓoye. Ba tare da tsayawa jiran Hukuma ta bashi izinin kamo Zemo ba, Rogers da Wilson kawai sai suka yi gaban kansu inda suka nemo Maximoff, Clint Barton da Scott Lang domin su taimaka musu. Shi ma Stark sai ya nemi izinin Ross domin ya haɗa tasa tawagar, bayan ya samu ne sai ya kira Romanoff, T'Challa, James Rhodes , Vision da kuma Peter Parker domin su kama gudaddun sojojin.
Tawagar Stark sai ta tare tawagar Rogers a filin jirgin sama na Leipzig/Halle Airport, inda suka yi artabu kafin daga ƙarshe Romanoff ta baiwa Rogers da Barnes dama suka gudu. Hakan ya bada damar kama sauran Membobin tawagar Rogers inda aka kulle su a kurkuku, yayin da shi kuma Rhodes ya samu matsalar Shanyewar jiki a Sakamakon ɓaro shi da Vision yayi bisa tsautsayi. Ita kuwa Romanoff sai ta ɓoye.
Daga baya sai Stark ya gano cewa Barnes bashi da laifi a wannan hari da aka kai, don haka sai ya nemi Wilson ya faɗa masa inda Rogers yake. Ba tare da ya Faɗawa Ross ba, sai Stark ya tafi Sansanin Hydra da ke Siberia inda suka samu haɗin kai a tsakaninsu da Rogers da Barnes, ba tare da sun san cewa T'Challa yana biye da su ba.
A nan ne suka gano cewa Zemo ya kashe ragowar sojojin, Zemo sai ya nuna musu wani bidiyo wanda ya bayyana cewa wannan mota da Barnes ya tsare a 1991, tana ɗauke ne da iyayen Stark waɗanda Barnes ya kashe.
Jin haushin cewa Rogers ya san da hakan amma bai faɗa mishi ba yasa Stark ya Far musu dukkan su, hakan ya jawo zazzafan yaƙi a tsakanin su. A garin hakan ne Stark ya Lalatawa Barnes hannun ƙarfen sa, shi kuma Rogers ya lalata masa rigar sa ta ƙarfe.
Daga nan sai Rogers ya bar Garkuwar sa a nan Yayinda ya tafi da Barnes. Jin daɗin cewa ya rama kashe masa iyaye da aikin tawagar Avengers tayi SANADI a Sokovia ta hanyar raba kawunan su, sai Zemo ya nemi kashe kansa, amma sai T'Challa ya hana shi, sannan ya miƙa shi ga Hukuma.
Bayan ƙura ta lafa, sai Stark ya ƙerawa Rhodes wata na'ura wacce ta bashi damar ci gaba da tafiya, Yayinda shi kuma Rogers ya samu Mafaka a Wakanda bayan ya ceto abokansa daga kurkuku.
A wata fitowa ta ƙarshe, an nuno Barnes a Wakanda Yayinda ya nemi a sashi a gidan ƙanƙara inda zai yi bacci har sai an samo maganin juyar masa da tunani da aka yi. Sai kuma Peter Parker wanda aka nuno shi yana gwada wata na'ura da Stark ya ƙera masa.
JARUMAN FIM ƊIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO A CIKIN SA
* Chris Evans - Steve Rogers / Captain America
* Robert Downey Jr. - Tony Stark / Iron Man
* Scarlett Johansson - Natasha Romanoff / Black Widow
* Anthony Mackie - Sam Wilson / Falcon
* Sebastian Stan - Bucky Barnes / Winter Soldier
* Don Cheadle - James "Rhodey" Rhodes / War Machine
* Jeremy Renner - Clint Barton / Hawkeye
* Chadwick Boseman - T'Challa / Black Panther
* Paul Bettany - Vision
* Elizabeth Olsen - Wanda Maximoff / Scarlet Witch
* Paul Rudd - Scott Lang / Ant-Man
* Emily VanCamp - Sharon Carter
* Tom Holland - Peter Parker / Spider-Man
* Frank Grillo - Brock Rumlow / Crossbones
* William Hurt - Thaddeus "Thunderbolt" Ross
* Daniel Brühl - Helmut Zemo
* Marisa Tomei appears - May Parker
* John Kani - T'Chaka
* Hope Davis - Maria Stark
* Gene Farber - Vasily Karpov
* Florence Kasumba - Ayo