SHARHIN FIM ƊIN DOCTOR STRANGE

SHARHIN FIM ƊIN DOCTOR STRANGE

* Bada Umarni - Scott Derrickson

* Ɗaukar Nauyi - Kevin Feige

* Rubutawa Da Tsarawa - John Spaihts/Scott Derrickson/C. Robert Cargill

* Taken Fim - Michael Giacchino

* Tacewa - Wyatt Smith/Sabrina Plisco

* Ranar Fita: 4 ga Nuwamba 2016

* Kuɗin Da Ya Kawo: Dala Miliyan $677

Doctor Strange Fim ɗin jarumta ne da aka yi shi a shekara ta 2016 a Ƙasar Amurka. Labarin fim ɗin ya samo asali ne daga littattafan almara na Marvel Comics mai suna Doctor Strange wanda Stan Lee da 
Steve Ditko suka rubuta. Kamfanin Marvel Studios ne ya shirya fim ɗin Yayinda Kamfanin Walt Disney Motion Pictures ya rarraba. Doctor Strange shi ne Fim na goma sha huɗu daga cikin Fina-Finan duniyar Marvel mai suna Marvel Cinematic Universe (MCU).

An fara ɗaukar Fim ɗin ne a watan Nuwamban shekara ta 2015 a garin Nepal, kafin a koma United Kingdom, Hong Kong, Sannan aka kammala a Birnin New York cikin watan Afirilun 2016. An saki wannan Fim a Hong Kong a ranar 13 ga watan Oktoba na 2016, yayin da kuma aka sake shi a Ƙasar Amurka a ranar 4 ga watan Nuwambar shekara ta 2016 a zubin 3D da IMAX 3D. Wannan Fim ya samu karɓuwa matuƙa a wajen masana da kuma 'yan kallo baki ɗaya, inda ya kawo maƙudan kuɗaɗe kimanin Dala miliyan $677. Kuma an yabawa Fim ɗin sosai, musamman dangane da irin kayan aikin da aka yi amfani da su a cikin Fim ɗin.


LABARIN FIM ƊIN

A Kathmandu, babban Matsafi Kaecilius tare da muƙarraban sa sun samu damar shiga wani ɓoyayyen gida da ake kira Kamar-Taj inda suka kashe mai gadin ɗakin karatun wurin ta hanyar fille masa kai. Bayan haka, sai Matsafi Kaecilius ya ciri wasu shafuka daga cikin shafukan wani tsohon littafin tsafi ya fece, shi wannan littafin tsafi mallakin wata babbar Matsafiya ce da ake kira da 'Ancient One', kuma ita ce take koyar da tsafi a wannan wuri na Kamar-Taj, shi kanshi Kaecilius ɗin ma ita ce ta koyar da shi tsafin. Wannan Matsafiya ta bi bayan su Kaecilius inda har sukai artabu amma bata samu damar kama su ba. 

Dakta Stephen Strange Shahararren-Ƙwararren Likitan cutukan da suka shafi ƙwaƙwalwa ne kuma mai Kuɗin gaske. Wannan likita yana zaune ne a birnin New York. 
Watarana Dakta Stephen strange yana tafiya a mota sai ya gamu da wani mummunan haɗari wanda ya haifar masa da matsala a hannayen sa har ya zamanto cewa ba zai taɓa iya aikin ƙwaƙwalwa da hannayen ba. Dakta Christine Palmer tsohuwar budurwar Dr. Strange ce kuma abokiyar aikin sa tayi iya ƙoƙarin ta wajen ganin ta taimaka masa, amma shi baya gani saboda lamarin gaba ɗaya ya dame shi. Sai dai yaje nan ayi masa aiki in bai yiba ya koma can har dai dukiyar sa gaba ɗaya ta kusa ƙarewa.

Watarana sai ya samu labarin wani mutum mai suna Jonathan Pongborn wanda shima ya taɓa samun matsalar ƙafa kwatankwacin irin nasa amma ya warke. Stephen Strange sai yace wurin wannan mutumin inda shi kuma yayi masa kwatance da Kamar-Taj. A can ne Matsafi Mordo ya gabatar da shi ga wannan Matsafiya wato 'Ancient One'. Da ƙyar da siɗin goshi ta karɓe shi a matsayin ɗalibi, Kasancewar zafin kai da dogon burin sa suna mata kama da na Kaecilius.

Stephen Strange ya samu horaswa sosai a fannin tsafi daga wajen wannan Matsafiya, sannan ya samu horon faɗan hannu da hannu a wajen Mordo. Sannan yana yawan karanta littattafan tsafi daga ɗakin karatun wannan wuri wanda a yanzu yake ƙarƙashin kulawar Matsafi Wong. A nan ne Stephen ya gano cewa wannan Daular tamu ta mutane tana samun kariya daga hare-haren duk wani abu da ya shafi tsafi daga sauran Dauloli sakamakon wata garkuwa a sararin samaniya daga wurare uku da ake kira da Sanctums. Waɗannan wurare ɗaya na Landan, ɗaya New York sai Kuma ɗaya a Hong Kong. Dukkan waɗannan wurare guda uku sun haɗe ne a kamar-Taj, kuma daga nan wurin ana iya zuwa Sauran wuraren cikin sauƙi. Aikin dukkan matsafan da ke kamar-Taj shi ne gadin waɗannan wurare guda uku, amma shi Pangborn sai ya zaɓi yin amfani da tsafin kawai don samawa kansa lafiya.

Kasancewar Stephen mutum ne mai hazaƙa matuƙa, nan da nan ya iya abubuwa iri daban-daban a fannonin tsafi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. Sa'annan a ɓoye kuma yana karanta Manya-manyan littattafan tsafin da ke tsibe a Ma'ajiyar littatafai dake kamar-Taj. A garin haka ne watarana yaci karo da wata sarƙar tsafi da ake kira da 'Eye Of Agamotto', ita wannan sarƙar tana ɗauke ne da dutsen lokaci wanda shi wannan dutse ɗaya ne daga cikin duwatsun al'ajabi guda shida da ake da su a duniya. Ita wannan sarƙar tana baiwa mutum damar juya lokaci yadda ya ke so.

Don haka sai Stephen yayi amfani da wannan sarƙar ya karanta littafin da Kaecilius ya yagi shafuka daga cikin sa. Mordo da Wong sun gargaɗi Stephen kan ƙoƙarin yiwa dokokin rayuwa Katsalandan da yake yi. Inda har suke kamanta shi da Kaecilius wanda yake son ganin ya rayu har abada.

Shi kuwa Kaecilius bayan da ya samu damar yago waɗannan shafuka, sai yayi amfani da su wajen tuntuɓar shugaban lardin duhu wato Dormammu. A lardin duhu babu lokaci kwata-kwata, Kaecilius yana tunanin in ya tuntuɓi Dormammu zai iya Samar masa da rayuwa ta har abada. Sai dai Dormammu ba zai iya shigowa lardin mutane ba matuƙar waɗannan wurare uku suna nan, don haka sai Kaecilius ya lalata Sanctum ɗin Landan sannan ya ɗebi muƙarraban sa suka nufi Sanctum ɗin birnin New York domin shi ma su lalata shi.

Ko da yake sun samu nasarar kashe mai gadin wurin, Stephen ya hana su damar rushe wurin har saida Matsafiya Ancient One' da Mordo suka zo. Strange da Mordo sun ji ba daɗi Yayinda suka fahimci cewa tsawon rayuwar da wannan Matsafiya ta samu ya tabbata ne sakamakon tsafin da take jawowa daga lardin duhu. Ancient one da Kaecilius sun tafka baƙin gumurzu sosai a lardin madubi har yayi mata mummunan rauni sannan ya fece izuwa Hong Kong.

Kafin mutuwar ta, Matsafiyar ta shaidawa Stephen cewa shima dole sai ya karya dokar rayuwa matuƙar yana so ya samu galaba akan Kaecilius saboda ita ma dole ce ta sa ta yin hakan. Bayan mutuwar ta sai Stephen da Mordo suka nufi Hong Kong inda suka cimma Wong a mace, Sanctum ɗin a rushe sannan Dormammu yana shirin shigowa lardin mutane wanda hakan zai sa duhu ya mamaye ko ina. Strange sai yayi amfani da wannan sarƙar ya maida lokaci baya inda ya ceci Wong, sannan ya shiga lardin duhu ya Samar da maimaicin lokaci a tsakanin sa da Dormammu. Bayan Dormammu ya kashe strange sau barkatai amma duk a banza, daga ƙarshe dai dole ta sa ya haƙura yabi tsarin da Strange ɗin yake so, wato ya kwashe yanasa-yanasa ya bar daular mutane ya san nayi.

Bayan komai ya koma daidai, sai Mordo ya ce shi ya gaji da ganin irin wannan ta'asa da ake yiwa dokokin rayuwa ta hanyar tsafi, don haka sai ya tafi abin sa. A ƙarshe dai, strange ya maida wannan sarƙa kamar-Taj sannan ya koma sanctum ɗin birnin New York domin ya ci gaba da karatun sa.

A wata fitowa ta ƙarshe, an fasko mana strange tare da Thor inda ya taimaka masa da bayanin inda zai ga Mahaifin sa Odin, bayan sun duba inda lokiY ya ajiye shi amma basu ganshi ba.

JARUMAN FIM ƊIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO A CIKIN SA

* Benedict Cumbebatch - Dr. Stephen Strange

* Chiwetel Ejiofor - Karl Mordo

* Benedict Wong - Wong

* Michael Stullbarg - Nicodemus West

* Benjamin Bratt - Jonathan Pongborn

* Scott Adkins - Lucian

* Mada Mikkelsen - Kaecilius

* Tilda Swinton - Ancient One

* Chris Hemsworth - Thor


<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring

Post a Comment (0)