SHEIK PANTAMI DA KWANKWASO DUK ƳAN UWAN MU NE


Sheikh Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami Da Engineer Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso Duk 'Yan uwan Mu Ne!

Daga Imam Murtadha Gusau

Laraba, 25/09/2019

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Assalamu Alaikum

Ya ku 'yan uwana masu kima da daraja! Kamar yadda kuka sani, sanannen dan siyasar nan, tsohon Gwamnan Kano, tsohon Minista, tsohon Sanata, dan jihar Kano kuma dan arewacin Najeriya, Engineer Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da bikin tura 'ya'yan talakawa har su dari biyu da arba'in da biyu (242) zuwa kasar India domin karatun digiri na biyu, wanda gidauniyar sa ta Kwankkwasiyya Foundation ta shirya, muna rokon Allah ya saka masa da alkhairi, kuma ya yawaita muna irin su a arewacin Najeriya, amin.

A daidai lokacin da suka tafi filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano, da ke cikin birnin Kano, wato Malam Aminu Kano International Airport, domin yin rakkiya ga wadannan yara, kwatsam, sai ga mai girma Ministan Sadarwar Nigeria, Abu Abdir-Rahman, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami shi ma yazo filin jirgin saman domin komawa gida daga ziyarar aiki da ya kai jihar Katsina. A nan sai aka samu wasu shedanun yara, marasa tarbiyya, daga cikin magoya bayan Kwankwasiyya din suka yi masa ihu, suna cewa 'BA MAYI, BA MAYI', wanda da ma dukkanin mu muna sane, a wannan kazamar dimokradiyyar ta Najeriya, wannan ba sabon abu bane, domin shi kan sa Dr. Kwankwason na sha ji ko ganin anyi masa hakan, misali a garin Kaduna da kuma filin jirgin sama na Abuja, a shekarar da ta gabata.

A gaskiya, Allah ya sani, wallahi ni ban ji dadin wannan abun da aka yiwa Dr. Pantami ba, duk da ya kasance yanzu riga biyu ce yake sanye da ita a jikin sa; akwai ta Malanta wadda ita ce asalin sa, da kuma ta mukamin Minista a tsari irin na kazamar siyasar dimokradiyya.

Amma dai ni yanzu abun da nike so mutane su fahimta shine, da Dr. Kwankwaso da Dr. Pantami dukkanin su namu ne. Dukkannin su Musulmai ne kuma 'yan arewa; don haka wallahi ni ba zan yi bangaranci in koma gefe guda ba, wato in goyi bayan Kwankwaso ko in goyi bayan Pantami. Dukkan su mun san su, kuma muna yi masu fatan alkhairi, da addu'ar gamawa lafiya. Dr. Isa Pantami malami na ne kuma babban masoyi na, wanda nike matukar kauna da girmamawa tsakani na da Allah mahallici na ba domin wani abu ba. Ni da shi mun san juna shekaru masu yawa da suka gabata ba tun yanzu ba, ba sai yanzu da ya zama minister ne nike neman ya sanni ba kamar yadda naga wasu na kokarin yi, a'a. Sheikh Pantami Malami na ne wanda yake bani shawarwari da nasihohi masu amfani a duk lokacin da Allah yasa muka hadu da shi; yana bani shawarwari da nasihohi irin na uba ga dan sa. Don haka, Allah ya sani, sam ban ji dadin abun da aka yi masa ba, ba domin komai ba sai don kasancewar sa dan uwan mu, sannan shi dan Najeriya ne mai 'yanci, sannan sai rigar da yake saye da ita ta Malanta da wa'azin Musulunci wadda tafi kowace riga daraja matukar mutum ba Annabin Allah bane shi. Ina rokon Allah ya shiryi wadannan yara da suka yi masa wannan cin mutunci, su gane cewa abun da suka yi masa ba daidai bane. Shi kuma ina rokon Allah ya kara masa hakuri da juriya, yasa hakan ya zamar masa kaffara da karin daukakar darajar sa, amin. Allah ya sani, na dade ina nuna damuwa akan irin yadda aka dade ana ciwa Malamai da ma wadanda ba Malamai ba mutunci akan siyasar nan ta dimokradiyya, musamman daga shekarar 2015 zuwa yau.

Sannan shi kan sa Dr. Kwankwaso, a irin sanin da nayi masa, nayi imani da Allah, ba zai ji dadin abun da aka yiwa Dr. Pantami ba, saboda meye ribar sa a ciki idan har aka yiwa Sheikh Pantami ihu? Don haka ni ina ganin ba daidai ba ne muyi kudin goro ga dukkan 'yan Kwankwasiyya kace duk haka suke, ko kuma kace ai da sanin Dr. Kwankwaso ko da umurnin sa suka yi wannan aika-aika. Domin idan za mu yi adalci, ko a cikin bidiyon da na kalla, naji wasu suna cewa ba daidai ba ne, wasu suna cewa ba'a haka fa, kai wasu har hoto suka yi da shi, to kaga kenan a cikin kowace irin tafiya akwai masu hankali da marasa hankali.

Allah yana fada muna a cikin Alkur'ani mai girma cewa:

"Wata rai ba ta daukar laifin wata."

Kuma idan mun ce haka, kenan yanzu idan wani bara-gurbin Musulmi yayi wani shirme sai ace Musulunci ne ya sa shi yin hakan kenan? Ai ba za mu ce haka ba. Don haka zai zama zalunci kenan kace don wasu 'yan Kwankwasiyya sunyi shirme, kazo kana la'antar shi Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso, ko kuma kace shine yasa su, ko ka zagi sauran masu hankalin cikin su. Idan maganar girmama Malamai ne ai a cikin Kwankwasiyyar ma akwai wasu Malaman na Sunnah masu daraja, abokanan Da'awar Dr. Pantamin da suke tare da Dr. Kwankwaso.

Wallahi ni har mamaki nike yi idan naga wasu suna tayar da jijiyar wuya, suna ihu, suna kunfan baki, wai da sunan kare Dr. Isa Pantami, don sun ga yanzu Allah ya daukaka shi, ya ba shi mukamin Minista, wanda a da can baya, wallahi suna cikin masu cin mutunci da zagin sa, ni da su kar-ta-san-kar ne, idan sun kuma yi musu to sai mu ji, domin a hannun mu akwai faifan bidiyo da na odiyon da suke zagin sa mu kuma muna kokarin hana su. Idan sun musa za mu nuna wa duniya ta gani! Wato su a wurin su sai yanzu ne Sheikh Pantami ya zama mutum ko? Allah Sarki! Wallahi ya kamata mu ji tsoron Allah a cikin al'murran mu. Kuma shi Dr. Pantamin ai yasan ku kar, domin shi ba wawa ba ne kuma ba jahili ba. Ina rokon Allah ya shirye ku, amin. 

Sannan ya zama wajibi a gare mu mu san cewa Dr. Kwankwaso da Dr. Pantami dukkanin su kowa akwai alkhairin sa, sannan akwai kuskuren sa. Don haka ina rokar masu Allah da ya tausaya masu, ya yafe masu kura-kuren su, ya basu ladan kyawawan ayukkan su. Sannan dukkanin mu muma masu laifi ne. Ina rokon Allah ya yafe muna kura-kuren mu, amin.

Sannan ina rokon Allah, wannan jarrabawa da ya jarabi Dr. Pantami da ita, ta mukamin Minista, ya bashi ikon tsallake ta cikin nasara. Shi ma Dr. Kwakwaso wannan kokari da yake yi na taimakawa 'ya'yan talakawa suyi karatu, domin su zama masu dogaro da kansu a nan gaba, shima Allah ya saka masa da alkhiari, amin.

Ya Allah ina rokon ka, don tsarkin Sunayen ka, kasa wadannan bayi naka, wato Dr. Pantami da Dr. Kwankwaso su fahimci juna, su sasanta kawunan su, suyi wa juna afuwa, amin. Ya Allah kar kasa su saurari 'yan kore daga kowane bangare, sannan kar kasa su saurari 'yan zuga. Sannan ya Allah, ina rokon ka, idan muka mutu, muka hadu da kai, ka sa ni, da Dr. Pantami da Dr. Kwankwaso, da duk wanda ya karanta wannan rubutun a Aljannar ka, don rahamar ka, amin.

Sannan wallahi ni babban abun da ya burge ni game sha'anin mai girma Minista, wato Sheikh Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami a cikin wannan cin mutuncin da aka yi masa shine: suna yi masa ihu, suna aibata shi da cin mutuncin sa, amma shi kuma yana tafiyar sa yana fara'ar sa da murmushi abin sa, bai ko ma san suna yi ba.

Na san dai duk mun sani cewa, yin murmushi da fara'a sadaka ne a cikin addinin mu na Musulunci, sannan kuma koyarwar Manzon Allah (SAW) ce.

Da man masu iya magana sunce, amfanin ilimi aiki da shi. Don haka Sheikh Pantami, mun shaida cewa, ka yi ilimi kuma kayi aiki da ilimin ka, da ka rabu da jahilai ba ka kula su ba suna ta ihun su a banza.

Sannan ya ku 'yan uwa! Don Allah ku kalli yadda wasu shedanun 'yan siyasa suke so suyi amfani da wannan jarabawa da ta faru ta Dr. Pantami a matsayin wata hanya ta yada barna, sharri da husuma a cikin al'ummah! Suna so su cimma wani buri nasu na sharri. Wallahi shi yasa nike cewa, ya zama wajibi wadannan shugabanni namu guda biyu su kiyaye, wato Dr. Pantami da Dr. Kwankwaso. Domin na lura da kyau, ana son yin amfani da wannan kaddara domin a cusa barna a tsakanin 'yan arewa. Wani wai shi Fa'izu Alfindiki, mai bai wa Gwamnan Kano shawara (Adviser), ya yada wata karya da wani shirme a soshiyal midiya, da ya zama dole mu kiyaye! Ga rubutun da ya yada kamar haka, ba tare da na canza komai a cikin rubutun sa ba, ta ken rubutun nasa shine:

"MAGOYA BAYAN KWANKWASO SUNYI YUNKURIN HALLAKA MINISTA A NIGERIA
Abinda wasu 'yan daba daga cikin darikar Kwankwasiyyah suka yiwa Ministan Sadarwa a Nigeria Dr Isah Ali Ibrahim Pantami jiya a filin jirgin sama na Kano yunkurin kisa ne, imba don Allah Ya kaddara jami'an tsaron da ke rakiyarsa sunyi bajinta ba wajen bashi kariya watakila da yanzu wani labarin ake na dabam. Za'a iya tuna watannin baya lokacin da wasu 'yan daba daga cikin magoya bayan darikar Kwankwaso suka tabbatar wa duniya cewa zasu hallaka Malam Isah Ali Pantami tun kafin ya zama Ministan Sadarwa lokacin yana matsayin Darakta Janar a ma'aikatar NITDA a tsakiyar Azumin watan Ramadan da ya gabata, sai gashi a jiya sun tabbatar mana da yunkurin kashe shi din. Sannan sunyi kokarin su keta masa mutunci ta hanyar cire masa hula da kayan jikinsa su masa tsirara bayan jifar da suka masa da ihu da tsinuwa sai Allah Ya kubutar dashi. Muna cike da tsoro idan basu saka wa Maigirma Minista guba (poison) ba saboda sun samu sa'ar taba jikinsa, akwai killer poison ko killer cancer disease wanda 'yan leken asiri (spy) suke amfani dashi su saka a jikin mutumin da suke so su hallaka cikin kankanin lokaci ba tare da an gane su ba, don haka ko da wasa mu ba mu yarda da mamayar da 'yan dabar Kwankwasiyya suka yiwa Ministan Sadarawa ba, dole ayi bincike. A cikin birnin Kano wannan mummunan al'amari ya faru, don haka muna kira ga gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta da dauki matakin gaggawa wajen zakulo mutanen da suka jagorancin yunkurin hallaka babban mutum a tsarin dokokin gwamnatin Nigeria Maigirma Ministan Sadarwa don su fuskanci hukunci ko da sun kasancewa daga cikin wadanda aka tura Indiya ne a dawo da su gida a hukuntasu. Sannan muna kira ga gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar daukar matakin gaggawa akan darikar Kwankwasiyya, don kiyaye faruwar abu makamancin wanda suka yiwa Maigirma Ministan sadarwa, babu shakka da sun samu sa'a hallakashi zasu yi. Muna rokon Allah Ya cigaba da tsare mana rayuwar Dr Isah Ali Ibrahim Pantami daga dukkan sharri Amin."

Ya ku 'yan uwana masu karatu, wannan fa shine abun da wannan mutum ya yada! Don haka yanzu meye amfanin wannan? Sannan me yake son cimmawa da wannan shirme na sa? Ni dai na san mutane ba wawaye bane, sannan shi kan sa Dr. Pantamin ba wawa bane. Don haka yanzu ya rage namu, shin zamu yarda da zugan wawaye ne ko kuwa yaya? Mu dai fatan mu da rokon Allah da muke yi, shine Allah ya daidaita su, su fahimci juna, amin.

Kuma gaskiyar lamari shine, wannan rashin tarbiyya na yiwa shugabanni ihu ba sabon abu ba ne a kazamar siyasar arewacin Najeriya; irin haka yasha faruwa ga 'yan siyasa da jami'an gwamnati a wannan yankin. Don haka, ba abin mamaki ba ne don shi ma mai girma Minista ya samu rabon sa na wannan al'ada ta cin zarafin manya.

Na tabbata wadannan mutane sun yi wa Sheikh Pantami abun da suka yi masa ne a matsayin sa na Minista, wanda yake rike da mukamin gwamnati, ba wai don yana Malamin addini ba, kamar yadda naga wasu suke ta kokarin fassara al'amarin. Kar mu manta, a can baya anyi ihu da jifa ga 'yan majalisar tarayya, sanatoci da gwamnoni, wasun mu suna jin dadi da murna da yabawa. Har ma Shugaban kasa da Mataimakin sa an taba jifar su a garuruwan mu, a lokacin mutane suna ta jin dadi da farin ciki. Duk da cewa muna sane wannan duk ya saba wa koyarwar addinin mu na Musulunci da kuma tarbiyyar mu a matsayin mu na 'yan arewa.

Muna kallo aka rika tozarta musamman 'yan majalisar tarayya wadanda ba sa goyon bayan Shugaba Buhari a siyasan ce, mutane suna ta yin tafi da murna, tare da yada hotunan cin mutuncin a soshiyal midiya. Da ma na san ranar kin dillanci tana nan tafe. Domin munafunci dodo ne, kuma mai shi yake ci.

Muna sane, muna ji, kuma muna gani, anan kasar, babu irin zagi, la'anta, batanci da cin mutunci da magoyan bayan Shugaba Buhari ba su yiwa Dr. Ahmad Gumi ba. Shin shi ba Malami bane?

To ashe kenan tun da wannan wata al'ada ce da 'yan siyasa da shugabannin yankin mu suka gina matasan mu akai, matasan da babu karatu, babu aikin yi balle makoma mai kyau, kenan babu wani abin mamaki don an yi wa Sheikh Pantami haka. Don kowa ma za a iya yi masa ihu, hatta Buharin! 

Don haka wallahi gara ma tun yanzu mu fara tunanin daukar matakan gyara wannan shashancin, kafin lokaci ya kure muna! Allah ya kyauta, amin.

Daga karshe nike cewa, a zahiri, a iya sanin mu, babu mutumin da ya kai Mumini, Malami, Mahaddacin littafin Allah, kuma mai kira zuwa ga addinin Allah daraja (Badini wannan sai Allah), saboda ayoyi da hadisai masu tarin yawa sun tabbatar da hakan, kuma babu mai musun haka sai jahili, wawa, wanda bai yarda da addinin Allah ba.

Wassalamu Alaikum,

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za'a iya samun sa a adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma 08038289761.
Post a Comment (0)