ALJANIN BANƊAKI

*ALJANIN BANDAKI* 
( ﺧﺎﺩﻡ ﺍﻟﺤﻤﺎﻡ)
 Nau'in Aljanu masu zama a bandaki_
Wato *Khadimul Hammam*

wasu nau'in Alajanu ne masu zama a bandaki ko bola ko kuma dukkan wani wajen kazanta da Dauda.

Bandaki shi ne inda suka fi zama da iyalansu domin a nan ne suka fi samun abinda suke bukata.
Wadannan Aljanu masu zama a bandaki galibinsu ko kuma dukkanninsu Arna ne kuma Mugaye masu hadari sosai.
Suna zama a bandaki suna kallon tsaraicin mutane, kuma tanan ne suke samu su shiga jikin 'yan-Adam har su saka musu wannan cutar da ake kira sanyi ko sabara ko kuma toilet infection a turance. Wato cututtukan da ake dauka a bandaki.
Khadimul Hammam, sune Aljanun da Bokaye suke amfani da su wajen sanyawa mutane Warin_Jiki ko Warin_ga6a kamar yadda wasu suke kiran cutar. Wato idan akayi wa mace irin wannan Asiri to duk wanda ya zo da nufin aurenta sai ya ji tana wani irin wari ko doyi mara dadi, haka ma in matar aure ce sai mijinta ya dinga ji tana yimasa doyi amma ita ba ta jin doyin kuma ba wanda zai ji sai me neman auren na ta ko kuma mijin na ta.
Sai ka ga mace duk wanda ya zo zance wajenta ba ya dawowa kuma ta rasa dalili.
Irin wadannan Aljanu mazauna bandaki sune suke sa Bokaye su binne layoyi a masai ko a bandaki. Sukan sa mutum ma ya karanta Alqur'ani a bandaki ko ya karanta wasu dalasimai na sihirin bokanci don ya samu kusanci izuwa gare su.
Ba sa yadda su zauna tare da mutum sai ya zama cikakken kazami me yawo da Daud'a da janaba kuma mara son ibada mara imani.

*ABUBUWAN DA KE SAWA ALJANIN BANDAKI YA SHIGA JIKIN MUTUM*

Wadannan wasu abubuwa ne da suke sawa Aljanun bandaki su shiga jikin Dan-Adam su zauna har su dinga cutar da shi;

1. Rashin tsaftace bandaki, Idan ana barin bayi yana doyi da wari ba a kula da shi ana tsaftace shi, to Aljanu za su zauna aciki kuma za adauki cututtuka.

2. Yin fitsari ko bayan gida tsirara, Idan mutum yana cire kayansa tsaf ya ajiye a gefe lokacin da zai yi fitsari ko bayan gida, yana sawa Aljanu suy sha'awarsa su shiga jikinsa.

3. Kallon gabas ko juya mata baya yayin bayan gida ko bawali. Ba a so mutum ya kalli sashin Ka'abah ko ya juya mata baya lokacin da yake bayan gida (kamar yanda yatabbata daga Annabi, acikin hadisin sa) hakan yana sa Aljanu su ga tsiraicin mutum.

4. Yin tsarki da kashin dabba ko qashin dabba_ domin abincin Aljanu ne. Wannan ma yatabbata daga Annabi, ya hani Al'ummarsa da yin ''Istijmar" da kashi ko kashin Dabbobi

5. Yin surutu ko maganganu marasa amfani a bandaki, Ko yin waya ko jin kida da dai sauransu. ( Manzon Allah yayi hani dayin Magana acikin Ban daki). Wannan yana sa su shiga jikin mutum.

6. Rashin wanka da zama da kazanta ko janaba. (Allah Ta'ala ya Umarci Annabimmu daya tsaftace tufafin sa. Manzon Allah (SAW) acikin wani hadisin sa, yana cewa: "Tsafta tana daga cikin Imani". Tashin yinta, Yana sawa su shiga jikin mutum domin sun ga dan'uwa.

7. Zama, a kofar bandaki ko a bola ko juji ko dukkan gurare masu kazanta.

8. Sihiri:- Koda ba ka yin wani daga abubuwan da muka ambata to da akwai sharrin masihirta 'yan bid'a da suke tura wa mutane Aljanu jikinsu.
Ana iya siyen irin wannan Aljani a tura shi jikin mutum, don ya mayar da shi kazami kuma mai baqin jini acikin al'umma.

*ABINCIN KHADIMUL HAMMAM.*

Abinda Aljanin bandaki yake ci ya rayu;

1- Yana lasar tsummokaran jini da mata suka ajiye a bandaki basu wanke ba.

2- Suna cin bayan gidan me shiga bandaki baya addu'a.

3- In bandaki yana da kazanta to suna tarewa a ciki.

 *YADDA ZA KA GANE ALJANIN BANDAKI YA SHAFE KA.* 

Idan har wannan Aljani ya shafeka, ko kuma an tura maka shi ta hanyar sihiri, to ga wasu alamomi da zaka iya gane hakan;

1- Mutum zai dinga dadewa a bandaki ata jiransa ya ki fitowa kuma ba abinda yake aciki sai tunani.

2- Yawan ganin wani mutum ko wata mata a bandaki ko kuma ganin abin tsoro a ciki.

3- Mutum zai zama me zama da kazanta da kuma rashin son yin tsafta. Za ka iya samun budurwa ba ta wanka sai an mata duka, ko dole Ko kuma magidanci yayi sati bai wanka ba.

4- Za ka dinga yawan jin warin kashi a jikinka ko a kusa da kai, har mutum ya dinga tunanin ko a bandaki ka shafo kashin amma ba zaka ganshi ba.

5- Mutane za su dinga gudun mai lalurar basa son zama da shi. Domin suna jin yana wari, shi kuma ba ya ji. Saidai kawai ya fuskanci mutane suna kyamarsa amma bai san dalili ba.

6- Rashin son yin Sallah da karatun Alqur'ani da sauran ibadu.

7- Mai lalurar zai dinga ganin kimar bandaki da muhimmancinsa fiye da ko ina. Don haka yana da son kasancewa a bandaki.

8- In mutum ya shiga bandaki sai ya ji ya fi nutsuwa da samun nishadi. Wani ko kudi zai kirga ya fi so ya shiga bandaki.

9- Yin surutai haka kawai a bandaki. Ka ji mutum yana magana shi kadai saidai hakan ya fi faruwa ga yara.

10- Za ka dinga jin kamar motsi ko kuma anayi maka magana in ka shiga bandaki.

11- Yawan shiga bandaki ba tare da wani dalili ba.

12- Jin kamar an caka maka allura ko kibiya a tsaraicinka lokacinda kake biyan bukata a bandaki.

13- Kaikayin-gaba mara jin magani.

14- Kurajen_gaba marasa jin magani.

15- Fitar farin_ruwa_mai wari musamman ga mata.

16- Yawan ganin kashi a inda kake zaune ko kuma jikin tufafinka.

17- Warin jiki ko warin qashi mara jin magani.

18- Mace zata dinga jin kamar wani abu zai fito daga gabanta kuma sai ya ki fitowa. Kullum yanai mata amma in ta je asibiti za ace ba a ga komai ba.

18- Rashin sha'awa da jin zafi lokacin saduwa.

19- Fitar ruwa mai wari da kuma yin al'ada bakikkirin mai doyi.

20- Yawan kasala musamman lokutan sallah.

Da dai sauran alamomi makamantan wadannan.

*NEMAN TSARI DAGA SHARRIN ALJANIN BANDAKI.*

In kana kula da wadannan insha Allahu wadannan Aljanu ba za su samu damar ra6arka ba.

1- Cire zobe idan za ka shiga bandaki.
2- Karanta addu'ar shiga bandaki.

 *ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﺍﻟﺨﺒﺚ ﻭﺍﻟﺨﺒﺎﺋﺚ* 

wato *_"Allahumma inniy a'uwzu bika minal khubuthi wal khaba'ithi"._*

3- Shiga bandaki da kafar hagu. Kamar yanda yatabbata daga Annabi.

4- Fitowa daga bandaki da kafar dama.

5- Fadar *_ ﻏﻔﺮﺍﻧﻚ _*

wato *_"Gufra nak"_*
bayan fitowa daga bandaki.

6- Yawan tsafatace bandaki.

7- Ka lazumci zama da tsarki da kuma zama da alwala.

8- Yawan karatun Alqur'ani da Azkar na Safiya da Marece.

والله تعالى أعلم.
Dan uwanku a Musulunci
Ahmad Muhammad Nata'ala
(Abu Fu'ad)
CEO: Daru As'habun- Nabiy Islamic chemist Kaduna

08069823502, 08075049989, 08083335561.


Post a Comment (0)