DANNAU


*DANNAU* 

Dannau shi ne lokacinda mutum ya kwanta yana bacci, sai ya ji kamar an zo an danne shi, an shake masa hanci da baki, ba ya iya motsi ko numfashi ko magana kuma yana ihu amma ba a ji. Mutum ya kan cika da tsoro da tunanin mutuwa lokacinda abun yake faruwa da shi.
Kashi uku zuwa shida bisa dari (3-6%) na mutanen duniya suna fama da matsalar Dannau. Yayinda kashi talatin bisa dari (30%) na matasa kuma suna fama da wannan matsala, aqalla kowanne acikinsu ya ta6a fuskantar matsalar Dannau ko da sau daya ne ashekara.

A gargajiyar Bahaushe, Dannau wani Aljani ne da yake zuwa ya hau kan mutum lokacin da yake bacci, ya shaqe shi, ya hana shi sukuni.
A binciken da Cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah ta gudanar, ta gano wadansu abubuwa da suke kawowa `yan Adam matsalar Dannau wadanda suke da alaqa da Aljanu da kuma masu nasaba da abubuwa na zahiri wadanda ba na Aljanu ba.

 *Menene Dannau?* 

Akan samu wasu nau'in Aljanu da suke zuwa su hau kan ruwan cikin mutum, su daddanne shi, su shaqe shi, sannan su toshe masa kafofin fitar iska kuma su daure masa jijiyoyi. Sukan zauna akan mutum daga `yan mintuna zuwa `yan awoyi, har sai sun gama yi masa abinda ya kawo su.

 *ALAMAR ALJANI YANA SO YA DANNEKA* .

Tun kafin bacci ya dauke ka, Aljanin zai iya zuwa ya tsaya akanka, yana jira kayi bacci, ya danneka.

 *Ga alamomin da zak gane* 

1- Kafin abin ya faru, za ka fara jin ciwon kai ta qeyarka, kafin bacci ya dauke ka.

2- Faduwar gaba, lokacin da ka dan fara gyangyadi.

3- Jin nauyi a kafadarka, kamar ana daddanna maka.

4- Mutuwar jiki gaba daya, musamman in kana so ka tashi kayi alwala kafin bacci. Karshe dai saidai ka kwanta haka.

5- Mutum zai ji ya kasa yin addu'a kafin bacci, ko kuma ya ce sai an jima zai yi.

6- Idan ka fara yin bacci sai ka ji kamar an zungureka ka farka.

7- Jin tsigar jikinka tana tashi kafin bacci.

8- Wani zai ga kamar ana giftawa ko ya dinga jin motsi a wajen kwanciyarsa.

9- Za ka ji kamar ka zama dan mitsitsi ko kuma ka zama gingimeme, ka cika daki.

10- Mutum zai ji kamar ana yin sama da shi, ko kuma kamar ana gudu da shi a mota.

Dadai sauran alamomi.
Wadannan alamomin da muka ambata, suna nuna cewa Aljani ya zo kusa da kai, yana jira kayi bacci ya danneka.

 *ALAMOMIN DANNAU, LOAKCIN DA YA DANNEKA.* 

1- Farkawa daga bacci cikin mugun firgici da bugawar zuciya mai karfi.

2- Toshewar kofofin iska ta yadda mutum zai kasa magana da numfashi. Za ka ji kana so kay ihu ko addu'a amma ka kasa ko kuma kana ihun amma ba ya fita.

3- Daurewar jijiyoyin jiki. Wato mutum ya kasa motsa kowace ga6a ta jikinsa, kamar hannu ko kafa da dai sauransu.

4- Jin alamun hannuwan mutane ko wasu halittu suna daddanneka ko suna shaqeka. Wani lokacin ma mutum yana kallon Aljanun da suka danne shi ido da ido.

5- Ganin wani mutum ko wasu mutane sun shaqeka, suna dura maka wani abu a bakinka.

6- A lokacin da abun yake faruwa da kai, zaka ji kana jin dukkan abubuwan da mutanen gidanku suke yi. Kana jin maganganunsu kuma kana fahimta. Ma'ana hankalinka bai gushe ba, saidai kamar matacce kake jinka, don ba abinda kake iyawa.

Amma fa wannan yana faruwa ne a tsakanin bacci da ido biyu, ba mafarki ake ba. A zahiri yake faruwa da mutum.

 *ME YASA ALJANU SUKE DANNE MUTANE?* 

Ba kowanne Aljani ne Dannau ba, sai dai akwai irin Aljanun da suke danne mutane da kuma dalilai mabambanta da suke sawa suyi hakan.

Nau'in Aljanun da suka fi danne mutane su ne Jinnul Ashiq, Jinnul tayyar, Jinnul Qariyn, Jinnul Katfa, da kuma Jinnus sihr. 
Wadannan nau'in Aljanu, insha Allah zamuyi bayani akansu anan gaba. 

 *Daga cikin abubuwan da suke sa wa Aljanu su danne mutane.* 

1- Wasu Aljanun, musamman Jinnul Ashiq, suna danne mace ne in tana bacci don su samu damar saduwar jima'i da ita. A irin wannan hali ne mace zata ga gardi ya danneta, ya shaqe mata baki, yana saduwa da ita.

Kuma in ya gama ya tafi, sai taga jikinta ya 6aci da maniyyi.
Haka ma idan namiji ne, zai ji ko yaga wata mace ta danne shi, tana wasa da gabansa, kuma in ya farka zai ga ya 6ata jikinsa.

2- Aljani yakan danne mutum ne don ya samu damar zuba masa guba ajikinsa. Aljanu, musamman Jinnus Sihr, suna zuwa su zubawa mutum guba a bakinsa ko a al'aurarsa, to amma ba za su iya ba sai in mutum yana bacci sannan su zo, su dura masa ta karfin tsiya.

3- Akwai Aljanu masu danne mutum don su cire masa wani abu daga jikinsa. Ya fi faruwa da mata masu ciki. Sai mace taga wadansu sun danneta, sun caka hannu a gabanta ko a cikinta, sun ciro wani abu. Daga nan sai taga jini ya 6alle mata, ko ta tashi da ciwon mara mai tsanani, in kuma tana da ciki sai ya zube. Haka ma Aljanu mashaya jini. Sukan danna mutum su tsotsi jininsa ko ruwan jikinsa.

4- Wani Aljanin tsananin rashin lafiya ce take damunsa amma wannan ya fi faruwa lokacin sanyi. Wani Aljanin in tsananin rashin lafiya ta dame shi, ya san yadda zai yi ya juyewa dan-Adan ita, don shi ya samu sauki. Don haka sai ya danneka, yayi maka aman guba, yayi tafiyarsa.

5- Haka kuma idan Aljaninka ba ya so ka tashi da wuri don aikata wani aiki, to zai zo, ya danneka, ya shaqeka.

6- Wasu Aljanun, kamar Jinnul Katfah, ba su da kwarin kafafuwa. Don haka duk sa'adda suka ra6i mutum saidai su danne shi su abokance shi, don in suka bari ya tashi ya tafi ba za su iya binsa ba, kuma ba su da kwarin kafafuwa sannan ba sa jurewa tsayuwa.
Wannan a takaice kenan.

 *YADDA ZA KA GANE AL-JANI NE YA DANNEKA, BAYAN KA WATSTSAKE.* 

1- Za ka tashi kag Al'auranka a miqe, ma'ana Aljana ta biya bukatarta da kai, ta tafi.

2- Ko mace ko namiji, zaka tashi, kaga ka 6ata jikinka da maniyyi.

3- Idan gari ya waye, za ka ji wajenda suka danne maka yanayi maka ciwo. Sawa'un ciki ne ko kirji ko mara ko kuma akanka suka zauna.

4-Tashi da ciwon kai, musamman ta keya da kuma jin alamar baccin bai isheka ba.

5- Galibi mutum ya kan wuni gabansa yana faduwa.
Da dai sauransu.

 *YADDA ZAKA GANE AL-JANI YA DANNE WANDA YAKE KUSA DA KAI.* 

1- Akwainwani Bawan Allah da ya ta6a gaya min cewa, sha'awar matarsa ta dauke, kwata-kwata ba ta sha'awar mijinta ko gamsuwa da yayin jima'i. To amma in tana bacci sai yaga tana wasu abubuwa kamar ana saduwa da ita. In ya tasheta daga baccin ya tambayeta meke faruwa?!, sai ta ce masa ai wani ne yake saduwa da ita, kuma tana jin dadi.

Don haka daga cikin alamomin da zaka gane Aljani ya danne na kusa da kai, akwai ganin yana wasu abubuwa kamar mai yin jima'i, a yayin da yake bacci.

2- Ganin idon mutum yana jujjuyawa lokacin da yake bacci. Wannan dai ita kadai ce babbar alama, domin ba wata ga6a ta jikin mutum da take iya motsi. Saidai a wasu lokutan wani har bige-bige yana iya yi, tare da ihu

 *BAMBANCIN MAFARKI DA DANNAU* .

Shi mafarki kwata-kwata mutum bai san abinda yake faruwa a kusa da shi ba kuma mutum zai iya ganin an dauke shi zuwa wani waje daban. 

Mafarki acikin bacci ake yinsa, ba a ido biyu ba.
Yayinda shi kuma Dannau hankalin mutum ba ya gushewa, saidai ya kasa sarrafa ga6o6in jikinsa, kuma mutum ba zai ga an kai shi wani waje daban ba.
Don haka Dannau a hakika yake faruwa, ba tunani bane kuma ba mafarki bane.

 *ME YAKE JANYOWA MUTANE MATSALAR DANNAU?* 

Kamar yadda mukayi bayani a farko, mafi yawan masu fama da matsalar Dannau matasa ne, domin kashi talatin bisa dari 30% na matasan duniya suna fama da wannan matsala.
Yanzu ga wasu dalilan da suke janyowa Aljani ya zo ya danne mutum.

1- Rashin kwanciya da tsarki ko alwala.

2- Rashin yin addu'ar kwanciya bacci.

3-Kwanciya Rub-da-ciki, ko rigingine ko kwanciya a 6arin hagu.

4- Kasancewar mutum dama can yana da matsalar Aljanu.

5- Asiri. Idan aka aiko Aljani don ya zuba maka wani abu ajiki.

6- Bude tsaraici yayin kwanciya bacci, na iya sawa Aljani ko Aljana suyi sha'awar kwanciya da mutum.

7- Shaye-shayen kayan maye. In mutum yana shaye-shaye, hakan yana janyo Aljanu `yan shaye-shaye `yan uwansa su dinga zuwa suyi maye akansa.

8- Kaiwa tsakar dare ana yin abinda Aljanu suke so. Wato mutum ya raba dare yana jin kida da waka, ko kallon bidiyo da makamantansu.

19- Kwanciya a mazaunin Aljanu ko kwanciya akan `ya`yan Aljanu. 
 
 *ME MATSALAR DANNAU ZATA IYA JANYOWA MUTUM?* 

Idan mutum yana yawan samun matsalar Dannau, za ta iya kai shi ga:

1- Rashin samun bacci. Wanda shi kuma zai haifar masa da matsaloli masu yawa.

2- Yawan ciwon kai.

3- Yawan bugawar zuciya, wanda shi ma zai iya janyo masa matsaloli da yawa.

4- Makuwa. Abinda ake nufi da makuwa shi ne, lokacin da mutum yake cikin tafiya, sai kwai yaga ya daina gane hanya, koda kuwa a unguwarsu ne ko wajen da ya sani. Mutum zai ga kamar bai san wajen ba, saidai ya tambaya ko kuma a kai shi gida. Saidai wannan ta fi faruwa da tsofaffi da yara.

5- Matsalar Dannau tana shafar kwakwalwa kai tsaye. Wanda hakan zai iya haifar da matsaloli masu yawan gaske.

YADDA ZA A MAGANCE MATSALAR DANNAU

1- Yin tsarki da alwala kafin kwanciya bacci.

2- Tsaftace wajen kwanciya da nisantar guraren zaman Aljanu.

3- Yin addu'a kafin kwanciya bacci.

4- Fara kwanciya a 6arin dama da kuma rufe kunne da hannun hagu. Wato in mutum ya kwanta, sai yasa hannunsa ya rufe kunnensa.

5- Inda hali, ka dena kwanciya a daki kai kadai. Sai da wani a kusa da kai.
Duk wanda yake samun matsalar Dannau har sau biyu a shekara daya, to yana cikin wadanda matsalar, saboda bai fiye faruwa akai-akai ba, sai da wata babbar matsala.
Yana da kyau ka ziyarci mai Ruqiyyah, ya bincika kanka, don gano wadanne irin Aljanu ne suke danneka da kuma abinda suke yi da jikinka ko kuma abinda suke zuba maka.

والله تعالى أعلم.
Dan uwanku a Musulunci
Ahmad Muhammad Nata'ala
(Abu Fu'ad)
CEO: Daru As'habun- Nabiy Islamic chemist Kaduna.
08069823502, 08075049989, 08083335561.
Post a Comment (0)