Diddigin Isar Hausawa Gwanja da Kurmi
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
08060869978
Da Bukar Mada
08021218337
Cinikayyar Goro wata abar tunawa ce a tarihin k'asar Hausa. Domin kuwa abisa al'ada, kowacce al'umma tana ware wani abu muhimmi mai daraja domin yin musanyar cinikayya a matsayin Haja tun kafin a samar da kudade.
Tarihi ya nuna cewa ba'a bar kasar hausa a baya ba a wannan fage, domin kuwa al'ummatan zamanin daya gabace mu sun yi riko da Bayi, Gishiri, Wuri, Azurfa, Zinare da Goro duk a bisa irin wancan matsayi na musaya a fannin cinikayya da sigar mallakar abubuwa.
Watakila, wannan ne yasa hausawa na wancan lokacin suka bazama neman wadancan abubuwa masu daraja. Tarihi ya nuna an samu garuruwa da dama da suka kafu saboda zuwan mutane hak'ar zinare a yankunan, haka kuma labarin yadda hausawa ke tafiya fataucin bayi, gishiri duk sananne ne izuwa duk inda suka san zasu samu kayayyakin. A irin haka muke kyautata tsammanin bahaushe ya fara riskar yankunan da ake noman goro domin fataucinsa a nasa yankin.
Duk da kasancewar babu takaimaimen lokacin da bahaushe ya fara zuwa wancan wuri, ko kuma sunan bahaushen daya fara dillancin goro, amma dai sanannen abu ne cewa turbar kasuwanci ta kafu a wuraren k'arni na takwas tsakanin garin Gwanja inda ake noman goro izuwa hamshak'iyar masarautar Kanem dake Borno.
Marubucin littafin Kitab Al-buldan mai suna Al'yaqubi bayan yawace-yawacen sa dayayi a kusa da wannan yankin, ya ruwaito a shekarar 872-873 cewa "akwai wata masarauta awani wuri dake tsakanin masarautar kanem da tafkin kwara (dai-dai da ko kuma kusa da inda kano take a yanzu), mai suna 'HBSH'. Sunan mai mulkinta 'MRH' sunan birnin ta 'ThBYR'. zuwa yanzu, da yawan masana sunfi gaskata cewar hausawa Al-Yakubi yake nufi a matsayin mazauna yankin.
Shi kuwa Goro, cinsa akeyi.
Kasancewar sa abu mai daraja na wancan lokacin, an jiyo canfe-canfe da dama akansa. Wasu ma na ganin cewar mahalicci ya zabe shi ne sama da sauran 'ya'yan itaciya, don haka...