YARO MAI ƘARFIN IMANI

    💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

     DARUSSAN RAYUWA


  ࿐​ ​PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION࿐​

༄༄ PWA ༄༄

 ➖➖➖➖➖➖➖➖➖
                ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
     ʂɬơrყ/wrıɬɛɛŋ     
            ɮʏ✍🏻:
👉🏻© ɧãımãŋ Řâééʂ ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
 ➖➖➖➖➖➖➖➖➖

                    Fitowa ta 03 
   
     YARO MAI ƘARFIN IMANI



Shaykh Fath al-Mowsily Ya ruwaito cewa; Watarana na haɗu da wani yaro yana tafiya shi kaɗai a cikin daji. Da Alamu yana tafiya yana magana ne shi kaɗai. Sai nayi mishi Sallama shi ma kuma ya amsa min kamar yadda ya kamata. Sai na tambaye shi da cewa "Ina zaka ne haka samari?' sai ya bani amsa da Cewa; 'zan je ɗakin Allaah ne (Makkah)'. Sai na sake tambayar sa da cewa; 'To me kake faɗa ne? Sai ya ce min QUR'AN nake karantawa. Sai na ce mishi, “Ai kai yaro ne ba lallai bane akan ka sai kayi karatun QUR'AN a koda yaushe' 

Sai yace dani, “na ga mutuwa ta ɗauki mutanen da basu kai ni yawan shekaru ba, saboda haka ne nake mata tanaji domin tana iya zuwa ta ƙwanƙwasa min ƙofa a kowane lokaci'. Da Mamaki a fuskata sai na ƙara ce masa, gashi takun ka ƙarami ne kuma inda zaka yana da nisa, sai yace dani "Aikina shi ne inyi takun (tafiya) amma samun damar kaiwa inda Zani wannan hukuncin Allaah ne'. Sai na sake tambayar sa da cewa, 'To ina Kayan tafiyar ka Kuma ina Abin hawan ka?' sai ya bani amsa da cewa; 'Imani na shi ne kayan tafiya ta ƙafata ita ce abin hawa na". Sai nace mishi ina nufin gurasa ne da ruwa",

Sai ya bani amsa da tambaya yana mai cewa; “ya kai wannan shehi, shin idan mutum ya gayyace ka gidansa kana ganin ya dace ka tafi da abincin ka zuwa wannan gida? Sai na bashi amsa da a'a, sai ya ci gaba da cewa; "to nima haka, Ubangijina ya Gayyaci Bawan Sa izuwa Ɗakin Sa, ƙarancin Imani ne kawai ke sa mu ɗebi guzuri. Duk da haka kana Tunanin ubangiji na Zai barni na tagayyara ne? 

 “Har abada Ba Zai bari ba” na bashi amsa. Daga nan sai ya tafi. Watarana sai muka haɗu da shi a garin Makkah, sai ya gabato gare ni yace dani; "Ya shaikh shin har yanzu kana da raunin imani? 

Na Tsakuro wannan labari ne daga cikin Littafin Stories of the Pious Na Shaikh Ahmad Ali

Haƙiƙa wannan labari darasi ne babba amma ga masu hankali da tunani. Allaah Ya Azurta Mu da kyakkyawar fahimta Aameen. 

<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring 


Post a Comment (0)