LALATA DA ƊALIBAI MATA A JAMI'O'I


LALATA DA DALIBAI MATA A JAMI'O'I

Idan Bera Da Sata...

Daga Maje El-Hajeej Hotoro

LAKCARA ba Mala'ika ba ne ba kuma Annabi ba ne da Allah Ya tsare shi daga dukkan sabo. 

Lakcara mutum kamar kowa da kwayoyin halittar SHA'AWA suke gudana a cikin jinin jikinsa.

Ba zai iyu ki sa fitinannun Tufafi masu farautar zuciya ki tashi nonuwa kamar kwan Kurciya. Ki baje duwawu kamar dutsen Dala da Goron dutse, ki shiga ofishin Lakcara kina kwarkwasa da iya shege don ki ci jarabawa ba. 

Kin ki karatu daga yawon banza da na wofi sai chatting da sa Hotunan TSIRAICI a Instagram, sannan a zo ana zagin lakcarori sun lalata ki ba. Dama can ke shegiyar kanki ce wacce taje Jami'a don ta bayar a ba ta.

Mu yakin mu akan matan kirki ne masu MUTUNCI da suka je Jami'a don Su yi karatu su ci jarabawa su zama abin alfahari gan al'umma. Wadanda BUNSURAYEN lakcarori ke yi musu barazana don yin lalata da su ta dole ko su kayar da su jarabawa.

Amma ke da kika dauki Jami'a a matsayin dandalin WAL BA NI WAL BA KA ba dake mu ke ba.

'Ya'yan Albarka a ci gaba da karatu a dage da addu'a gami da bin IYAYE. Idan matan aure ne a bi MIJI a kyautata shiga ta MUTUNCI a guji hulda da marasa MUTUNCI.

Allah Ya tsare mana IMANIN MU.
Post a Comment (0)