SHAWARWARI GA THREE KHANS OF BOLLYWOOD.
Ya ku Khans of Bollywood, ina yi muku sallama irin ta addinin musulunci, tare da fatan kuna lafiya. Allah ya sa haka, Aameen.
Duba da irin halin da kuke ciki a yanzu ne yasa na ce bari in ɗan jawo hankulanku ko hakan zai kawo sauyi ko da ba mai girma bane a cikin lamarin ku. Kun ga dai yadda Bollywood ta zama yau, kuna kuma ganin abubuwan da ke faruwa a cikin ta, don haka bana buƙatar sai na zayyano matsalolin ɗaya bayan ɗaya. Amma abinda nake so in yi magana akai shi ne;
1. Abinda ya haɗaku ya fi wanda ya raba ku yawa: in kuka lura da kyau za ku ga cewa maganata tana kan hanya, domin kuwa Addininku ɗaya, shekarunku kusan ɗaya, harshenku ɗaya, ƙasarku ɗaya, sana'arku ɗaya kuma kusan ƙwarewarku ɗaya.
2. Da ace kawunanku a haɗe suke, to da shiga tsakaninku zai zama aiki ne babba, amma saboda kun bari an raba kawunanku gashi nan yanzu ana yaƙarku a kaikaice.
3. Tabbas dole ne a samu 'yar matsala a nan da can a cikin kowace tafiya, amma ku sani cewa; gaɓar da kuke kai a yanzu gaɓa ce mai haɗarin gaske. Kuma ya kamata ku san abinda kuke ciki.
Kuna dai ganin yadda hatta daraktocin da ku kuka taimakawa kasuwancinsu yanzu wasunsu sun fara ja baya da ku. Kuna ganin yadda ake ƙoƙarin danne ku ta kowace fuska a masana'antar. Shin hakan ashe ba zai sa ku hankalta ba? Ka ga kai Aamir Khan, kana da masoya kuma kowa na yaba aikinka, ya kamata ka aje zafin kanka ka kuma kawar da tunanin ƙin yin wani abu daga gareka zai sa mutanen nan su canza daga yadda suke, ba ka da wannan matsayin da kimar a idonsu. Murna ma suke yi ka sauƙaƙa musu aiki, don haka ka aje wannan tunanin ka dinga shiga jama'a ya fi maka alheri, in ba haka ba sai a tashi wasan babu kai. In da Srk da sallu suka fi ka kenan, kuma kada ka manta masu iya magana sun ce "in ba za ka iya maganunsu ba, shiga cikinsu".
Kai kuma Srk, ya kamata ka yi wa kanka karatun ta nutsu, ka fi sauran shahara don haka an fi yi maka zagon ƙasa, amma saboda tunanin wai kai mutumin kirki ne bari ka ba su uzuri sai ka kasa fahimtar da ake ciki. Ya kamata tun daga kan abinda ya faru a kan shirin ka na FAN ka shiga taitayinka, amma sai ka ƙi. To ka sani cewa lokaci fa ya yi da ya kamata ka san me kake ciki, ehe. Kuma shawarata mafi girma a gareka ita ce ka ƙara kusantar mahaliccinka fiye da yadda kake a yanzu, in komai ya daidaita baɗi ka je ka sauke farali ka nemi zaɓinsa, sannan in ka dawo ka sake sabon tsari wa rayuwarka. Yanzu ba a yi wa kowa irin wannan kallon, in kuwa ka sake... To ga shi nan dai kana kallo ai.
To Salman saura kai, duba da cewa duk ka fi sauran shiga matsaloli a 'yan shekarun nan zan so ace ka yi aure in dai har ba wata babbar matsala bace ke da kai da za ta hana ka yin auren ko don saboda ka rufe bakin masu surutu. Kai kana nan kana abin arziki amma ana can ana maka zagon ƙasa, ba wai ina nufin ka daina taimakawa mutane ba ne, amma ka daina shiga cikin al'amuran da ka san cewa za su jawo maka zubewar mutunci ko yaya ne. Tun da ka riga ka san ga yadda abubuwan suke, to ka daina yarda da cewa ai akwai kyakkyawar alaƙa tsakaninka da wane ko su wane don haka ko da wani abu ya taso zasu goyi bayan ka, za ka sha mamaki ranar da za su juya maka baya.
A taƙaice dai, ba wai cewa nake yi ku zo ku yi fim tare ba, amma dai ku ajiye banbance-banbancen da ke tsakaninku, ku rungumi junanku kuma ku taimaki juna, in kuwa ba haka ba, to ina jiye muku tsoron maƙiya na gab da ɗaiɗaitar da ku.
Allah ya kiyashe mu da jin mummunan labari. Aameen.
Sai anjima.
©️✍🏻
Jamilu Abdurrahman
(Mr. Writer)
+2348185819176
Haimanraees@gmail.com