MATSALAR RASHIN TSAFTAR MUHALLI GA MATA

*MATSALAR RASHIN TSABTAR MUHALLI GA MATA*

Mata da yawa na fama da wannan matsala ta
rashin tsabtace muhalli, musamman a wannan
lokaci da waya ta dauke hankalin mutane. Sai
ku ga mace ta tashi ba ta gyara ko inda ta
kwanta ba ta hau kan waya ko an je gaban allon talabijin
za ayi kallo wannan babbar matsala ce kuma asara ne ga
lokacin mu.

Mu sa ni gyara shine mace, ba kawai gyara jiki ba don
maigida ya gan ki cikin tsabta amma wurin zama na nan
da kazanta ba. Ya na da kyau in muna son amsa sunan
mace mai tsabta sai mun hada da tsabtar jiki, muhalli,
da na yara.

Mata da yawa kan bawa gyaran cikin gida rashin
muhimmanci wanda daga nan sai matsaloli su yi ta biyo
baya.

Matsalolin Da Rashin Tsabtar Muhalli Ke Jawowa :

Akwai matsaloli ma su tarin yawa da rashin tsabtar
muhalli ke haifarwa. Kadan daga cikinsu sun hada da :

1. Ya na jawo raini a wurin maigida.

2. Ya na jawo raini wurin makwabta, dangin miji, abokan
miji da duk wani wanda ke shigowa gidan.

3. Ya na haifar da cuttutuka da za su zama barazana ga
lafiyar wanda duk ke zaune cikin gidan, dama wanda zai
shigo.

4. Ya na jawowa miji yawan aure-aure.
5. Ya na haifar da mutuwar aure da sauransu.

Ina Mafita????

Mafita anan ita ce :

1. Mata su sa ni tsabtar muhalli na daga darajar mace.
2. Ya kan jawo mace ta zama abin koyi wurin al’umma.
3. Kafin mace ta shiga sabgar kallo ko chatting ya na da
kyau ta tabbatar ta gyara ko ina cikin gidan.
4. Mace in ta samu lokaci ta yi ta canda fasalin daki, falo
lokaci zuwa lokaci, hakan kansa maigida ya ji kamar
sabon aure yayi ya kasance cikin dokin matarsa a kullum.
5. Bayan an tsabtace wuraren sai kuma a bi da turaren
daki.
6. Haka bandaki (Toilet) mace ya kasance ta na wanke
shi a kullum tare da zuba sinadaran kashe ko hana
kwayoyin cuta yaduwa.
7. Idan bandakin na gargaji ne a tsabtace shi ta hanyar
sharewa kullum da wankewa sannan ayi ta zuba toka
(ash) a bakin shadda da kuma wurin da ake fitsari.
Hakan kan kashe kwayar cutar da ta samu zama a wurin.
8. Labule a dinga wanke su tare da candazu akai-a kai.
9. Kicin ya zama ana tsabtace shi a duk lokacin da za a
yi aiki a ciki da bayan an gama, yin hakan zai hana haifar
da kwarin da za su cutar da mu.
10. Maigida ya sani sakin mace ko karin aure don rashin
tsabtar matar gida ba shine mafita ba, idan yaga tanayin
ba daidai ba shi zai tsawatar har ta gyara. In kuma ya
tsaya ya karin yin aure ne ba mamaki wacce aka kawo
ita ma tabi sawun wacce ta samu.
Da sauransu.

SHAWARA :

Shawara ta ga mata anan ita ce, mu sa ni tsabta cikon
addini ne sannan yana kara dankon soyyaya ga
maaurata. Kar mu kyale a dalilin rashin gyara muhalli ya
zama sanadin kawo wata mace da sunan ta shigo ta yi
gyara, duk macen da ta ba da wannan kofar to kuwa
lallai ta zubar da ajinta ta kuma raina kanta a wurin miji
da duk wani wanda ya shafe shi. Mu kasance cikin
tsabtace muhalli ta wurin shara, nome kananun ciyayi,
kona shara, yashe kwatami, da amfani da turraruka na
garwashi, tsinke da na fesawa, yin hakan kansa ku
kasance kamar sabbin maaurata a koda yaushe.

Post a Comment (0)