ZAMA DA MUGUN MIJI

*TAMBAYA TA 147*

ZAMAN DA MIJI MAI MUGUN HALI:

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah.

Wai ta yi kusan shekaru ashirin da aure, amma a kullum ba ta cikin kwanciyar hankali saboda:-
Mijinta mai munanan halaye ne: Ga dai duka, ga yawan zargi, ga ƙaryar tsiya, ga ƙulla sharri, ga kuma neman mata!
Ko Islamiyya ya hana ta zuwa saboda zargin cewa, wai malaman suna neman matan auren jama’a!
Har da mahaifinta ma ya zarge ta, haka da sauran maƙawabta, sannan kuma da ɗanta na-cikinta mai shekaru sha-shida!
Ta kai shi ƙara wurin iyayensa amma sai suka goya masa baya! Da ta kai wurin iyayenta kuma sai ya yi musu sharri wai sun tozarta shi, don haka ba ya ganin girmansu!
Daga baya da ta ce za ta bar gidansa sai ya yi ta ba ta haÆ™uri, tare da alÆ™awarin cewa idan ya sake zargin ta, to daga ranar ya yarda ta bar gidansa. 
Daga baya kuma ya sake yi har sau biyu! A nan ne ya yi alƙawarin cewa: Idan ya sake to a bakin aurensa. Kuma ya sake yi ɗin!!
Da ta kai ƙara wurin manya, shi ne aka tabbatar masa cewa igiyoyin aurensa guda biyu sun tsunke, yanzu saura guda ɗaya, don haka ya kula kar ya sake maimaitawa. Amma kuma ya sake maimaitawa har sau ba iyaka!
Tambayarta: Wai yaya matsayin aurensu? Kuma wace shawara za a ba ta? 

AMSA A147:

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Abin da na lura da shi dai, kamar tun farko ba su bi umurnin da Shari’a ta yi ba ne na yin kyakkyawan bincike tun kafin su fara nema, kuma har a Æ™ulla auren. Wannan kuwa yana daga cikin manyan musabbabin dukkan matsaloli da yawancin gidajen aure suke fama da su a yau. Amma dai wannan nata ya yi tsanani matuÆ™a. 

Shawarar da zan iya ba ta a nan ita ce: Ta tafi wurin wani alƙalin musulunci mai adalci, ko wata ƙungiyar musulunci mai ƙarfi kamar ta hisbah, ta kai musu wannan bayanin. Su za su iya gayyatan wannan mijin, su bincike shi har su tabbatar da gaskiyar waɗannan bayanan, daga nan kuma sai su ɗauki matakan da suka dace.

Har matsayin auren nasu ma za ta samu bayanai gamsassu daga wurinsu, idan dai aka zauna da malamai masana, kuma masu tsoron Allaah.

Allaah Ta’aala ya samar mata da mafita, kuma ya sa a dace.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
30/09/2019
12: 08am.

Majlisin sunnah
08164363661


Post a Comment (0)