SHIN ZAN IYA TSARKI DA RUWAN ZAMZAM?


SHIN ZAN IYA YIN TSARKI DA RUWAN ZAMZAM ?
*Tambaya
Assalamu alaikum Malam wani ya tambaye ni, shin zai iya yin tsarki da ruwan zamzam, saboda ya ji an ce yana kara karfin mazakuta, to gaskiya malam ban sani ba, shi ne na ce bari na tambayi Fukaha'u ?
*Amsa
Wa alaikum assalam To dan'uwa ruwan zamzam ruwa ne mai albarka, kamar yadda ya zo a hadisi cewa : Waraka ne ga cututtuka, Suyudi ya kyautata shi a Jami'ussagir, duba Faidhu Alkadeer 3/489.
Saidai duk da haka ya halatta ayi tsarki da shi a zance mafi inganci , saboda ba'a samu dalilin da ya hana hakan ba, ga shi kuma daga cikin ka'idojin malamai duk abin da ba'a samu nassin hani akansa ba a cikin mu'amalolin mutane, to ya halatta.
Sannan sahabbai sun yi tsarki da ruwan da ya bubbugo daga hannun Annabi s.a.w. , ruwan zamzam kuma ba zai fi wannan ruwan daraja ba.
Don neman Karin bayani duba : Hashiyatu Ibnu-abiidin 1\180 da kuma Insaf 1\27.
Allah ne mafi sani
*Amsawa*
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
18\9\2015.
Post a Comment (0)