RASHIN KUNYA KO ƘARANCIN TAUHIDI?


RASHIN KUNYA KO KARANCIN TAUHIDI???

Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuhu, Barkan mu da warhaka ya 'yan uwa musulmai. Hakika Nazari yana daya daga cikin hanyoyin da akan bi domin samun ilimi kuma a isar dashi. 

A yau ina so ne in yi tsokaci akan wani al'amari wanda ya dade yana ci min tuwo a kwarya. A wannan zamani da muke ciki akwai abubuwa ko kuma ince dabi"u da dama wadanda ake yi da sam basu dace ace musulmai suna yinsu ba, amma kuma anayi, kuma sam ba'a maida hankali kansu ba. Daya daga cikin irin wadan nan dabi'u ne nake so inyi tsokaci akai. Ayau, mafi yawanci matasan mu idan zasu masallaci domin gabatar da Sallah basa tsaftace jikinsu yadda ya kamata, wasu ma basa tsayawa su yi al'walar yadda ya kamata, wani ma
da ya dawo daga wurin aiki dagaje dagaje kawai zai yi alwala bur-bur yaje ya shiga masallaci mutane suna kyamar hada sahu da shi. Wani ma sam baya kula da jikinsa da zaku hada sahu da shi, kai kadai zaka san me kaji saboda warin hammata, warin rana da makamantan su. Amma idan zaice wurin budurwarsa ne tadi ko hira ko zance. Sai kaga yayi wanka, yayi wanki yayi guga an fesa turare an ci gayu. To shin don Allah me ya sa muka fi baiwa 'yan matanmu muhimmanci ta fannin tsafta fiye da wurin ibadar ?? Shin ashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa sallam bai hore mu da yin tsafta a koda yaushe ba? Shin baka.tunanin zaka iya daukar alhakin wadan da zaka hada sahun sallar dasu?? shin kana nufin ita budurwar taka ta fi masallacin muhimman ci ne? Shin Rashin Kunya ne yasa bama tsaftace jikin mu yayin zuwa masallaci amma mun iya cancarewa yayin zuwa tadi ko kuma karancin imani ne? Ya Allah ka bamu ikon yi maka cikakkiyar biyayya ba tare da nuna gajiyawa ba. Ya Allah ka bamu ikon yiwa junan mu adalci. Ya Allah ka sa mu dace kuma ka azurta mu da kyakkyawar fahimta Ameen.


Post a Comment (0)