BAYANIN AURE DA SAKI DA BIKO DA ZIHARI DA LI'ANI DA KHUL'I SHAYARWA.
Fitowa ta 011 Kuma na Karshe. A Babin Aure.
Ci gaba da Bayani daga inda muka tsaya:KHUL'I, shi khul'i Saki ne wanda babu kome a cikin sa, sai bayan wani auren da Matar za ta yi da yardarta bawai shiryawa akayi ta yi ba,
Mace Baiwa da aka 'yanta tana hannun Bawa, wato tana Matarsa, toh sai a ba ta Zabi ko dai ta ci gaba da zama da shi ko kuma ta rabu da shi, Wanda duk ya sayi Matarsa Auren ya warware. Sakin Bawa Saki biyu ne kadai, haka nan iddar Baiwa Haila biyu ce kadai zata yi, kaffarar Bawa kamar ta 'Da' take, wato babu wani bambanci.
Amma ban da haddodi da Saki, a nan akwai bambanci, duk abin da ya shiga cikin Yaro na Nono a cikin shekara biyu (2) na shayarwa,
Toh ya tabbatar da Haramci ko da na tsotsa daya yayi, amma abin da ya sha na Nono bayan wucewar shekara biyun bai tabbatar da Haramci ba, sai dai idan ya kusa da cikar sa shekara biyun, kamar da wata daya ko biyu, a wani zancen an ce idan aka yaye yaro kafin cikar sa shekara biyu, ya Saba da cin abinci ya manta da Nono toh duk abinda aka shayar da shi na Nonon Mace a wannan Lokacin ba zai tabbatar da haramci a kansa ba, Haramcin yana tabbata ta hanyar 'dura wa yaro Nono ta Hanci ko ta Kunne, duk Matar da ta shayar da wani yaro Nono, toh 'ya'yan wannan Matar da 'ya'yan Mijinta gaba daya na farko da na baya duk 'yan'uwan su ne, Babu Aure a tsakanin su gaba dayan su, amma ya halatta ga dan'uwansa ya Auri 'ya'yanta.
Daga Zauren Muslim Women Mata Zallah
WhatsApp Group.
MUHAMMAD TUKUR JALINGO
Domin Shiga Wannan Group Zaki Iya Turo Da Cikakken Sunan Ki Da Jihar Ku Ta WhatsApp Number Namu Kamar Haka
08164223447.
This Group Is Only For Women Please.