LUWAƊI A AL'UMMAR MUSULMI


*Luwadi a al’ummar musulmi.*😢😢


Luwadi a wannan zamanin ya zama kamar ruwan dare a tsakanin Matasa. Sun biye ma sha'awa irin ta shaidan wacce ta mamaye zukatansu, Sun afka cikin mafi munin Qazantar laifin da aka taba aikatawa adoron Qasa.

Ina gujewa masu irin wannan dabi’ar domin zasu fuskanci tashin hankali a duniya, a lahira kuma za’ayi musu azaba linki biyu. Yanzu har akwai wata sha’awa tsakanin namiji da namiji? Haba mutane, ina zamu tafi da wannan masifar? 

Hakika duk a cikin nau'o'in zina da danginta, Luwadi shine mafi Muni, kuma mafi Qazanta. Kamar yadda Allah yake gaya mana acikin Alqur'ani, sutaul-ankabut aya ta 27

وَلُوۡطًا اِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهٖۤ اِنَّكُمۡ لَـتَاۡتُوۡنَ الۡفَاحِشَةَ مَا سَبَـقَكُمۡ بِهَا مِنۡ اَحَدٍ مِّنَ الۡعٰلَمِيۡنَ‏

Ma’ana; “ka tuna Annabi lut (As) lokacin da yace wa mutanensa "me yasa kuke yin irin wannan alfashar? Babu wani wanda ya rigaku aikata irin wannan alfasha daga cikin talikai (HALITTU BAKI DAYA)".

Kuma acikin suratu An-naml aya ta 55, Allah yace; 

ﺍَـﺌِﻨَّﻜُﻢۡ ﻟَـﺘَﺎۡﺗُﻮۡﻥَ ﺍﻟﺮِّﺟَﺎﻝَ ﺷَﻬۡﻮَﺓً ﻣِّﻦۡ ﺩُﻭۡﻥِ ﺍﻟﻨِّﺴَﺎٓﺀِ​ؕ ﺑَﻞۡ ﺍَﻧۡـﺘُﻢۡ ﻗَﻮۡﻡٌ ﺗَﺠۡﻬَﻠُﻮۡﻥَ 

Ma’ana “ku kuna zuwa ma mazaje ta fannin sha’awarku maimakon mata, bari dai ku mutane ne wadanda suka kasance jahilai".

Acikin irin wannan halin ne, Annabin Allah yayi baki a gidansa, daga nan sai mutanen nasa suka zo suna masu gaggawa, akan sai sunyi luwadi da wadannan bakin kamar yadda acikin suratu-huud aya ta 78 Allah yake cewa; 

ﻭَﺟَﺎٓﺀَﻩٗ ﻗَﻮۡﻣُﻪٗ ﻳُﻬۡﺮَﻋُﻮۡﻥَ ﺍِﻟَﻴۡﻪِ ؕ ﻭَﻣِﻦۡ ﻗَﺒۡﻞُ َﺎﻧُﻮۡﺍ ﻳَﻌۡﻤَﻠُﻮۡﻥَ ﺍﻟﺴَّﻴِّﺎٰﺕِ ؕ​ ﻗَﺎﻝَ ﻳٰﻘَﻮۡﻡِ ﻫٰٓﺆُﻟَﺎۤﺀِ ﺑَﻨٰﺘِﻰۡ ﻫُﻦَّ ﺍَﻃۡﻬَﺮُ ﻟَـﻜُﻢۡ​ ۚ ﻓَﺎﺗَّﻘُﻮۡﺍ ﺍﻟﻠّٰﻪَ ﻭَﻟَﺎ ﺗُﺨۡﺰُﻭۡﻥِ ﻓِﻰۡ ﺿَﻴۡﻔِﻰۡ ؕ ﺍَﻟَﻴۡﺲَ ﻣِﻨۡﻜُﻢۡ ﺭَﺟُﻞٌ ﺭَّﺷِﻴۡﺪٌ .

Ma’ana; da mutanensa suka je masa suna gaggawa zuwa gare shi, kuma a gabani, sun kasancence suna aikata munanan ayyuka. Yace “ya mutane na, wadannan ‘ya’yana ne sune mafiya tsarki a gareku. Kuji tsoron Allah kar ku wulakantani a cikin baqi na. Shin babu wani namiji shiryayye daga gare ku?”.

Kunga anan har ‘ya’yansa mata yayi musu tayi, amma suka ce basu yadda ba. Kamar yadda wasu malamai sukace, ya gabatar da ‘ya’yansa mata ga wadannan mutanen domin ya fanshi bakin sa. Amma mutanen suka ki amince wa.

Acikin suratu-hijr aya ta 70 ya kara ce musu;

قَالَ هٰٓؤُلَاۤءِ بَنٰتِىۡۤ اِنۡ كُنۡـتُمۡ فٰعِلِيۡنَؕ‏

Ma’ana; “idan kun dage akan sai kunyi, toh ga ‘ya’ya na nan.

Amma duk da haka suka ki, daga karshe Allah yayi musu azabar da bai taba yiwa wata al’umma kafinsu ba. Allah ya aiko da Mala'iku suka ciccibe garin zuwa sama, suka watsa narkon azaba sannan suka Kifar dasu.

Acikin Suratu Huud (as) Allah yace:

ﻓَﺠَﻌَﻠۡﻨَﺎ ﻋَﺎﻟِﻴـَﻬَﺎ ﺳَﺎﻓِﻠَﻬَﺎ ﻭَ ﺍَﻣۡﻄَﺮۡﻧَﺎ ﻋَﻠَﻴۡﻬِﻢۡ ﺣِﺠَﺎﺭَﺓً ﻣِّﻦۡ ﺳِﺠِّﻴۡ

Ma’ana "Yayin da al’amarinmu yazo, sai muka sanya saman birnin ya zama kasanta(kamar juyin waina) sannan mukayi musu ruwan duwatsun wuta na sijjeel".

Allah ya azabtar dasu abisa zunubansu, kuma duk wanda yake aikata irin wannan mummunar alfashar toh ya sani shima irin wancen hukuncin ne dashi, domin kaima an aiko maka da annabi kamar yadda aka aikowa da su ma wadancen mutanen.

LUWADI Mummunar Annoba ce wacce ta kauce wa hanyar da Allah ya halicci dukkan halittunsa akai. Don koda dabbobi ba zaka tarar suna yin irin wannan abun ba.

Allah ya tsare mana imaninmu😭😭
Abdulhadi Dankama
Post a Comment (0)