NASIHOHIN LOKACIN SANYI 02

NASIHOHI A LOKACIN SANYI (fitowa ta biyu)
MU KYAUTATA ALWALA A LOKACIN SANYI
Idan sanyi ya tsananta mutane da yawa sukan tauye alwalar su, saboda kyamar amfani da ruwan sanyi, sai kaga wani ya kasa wanke gabar sa dukkanta, ko ya rika barin lum’a a jikin sa.
عن أبي هريرة، أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «ألا أدلكم على ما يمحو الله به الخطايا، ويرفع به الدرجات؟» قالوا بلى يا رسول الله قال: «إسباغ الوضوء على المكاره، وكثرة الخطا إلى المساجد، وانتظار الصلاة بعد الصلاة، فذلكم الرباط".
An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara masa yarda, lallai manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yace: “ku saurara! Shin kuna so in nuna maku (ayukka) wanda Allah yake goge zunubbai saboda shi? kuma yake daukaka darajoji saboda shi? Suka ce: e ya Manzon Allah, yace: “kyautata Alwala a lokacin kyama (kamar lokacin sanyi) da yawan taku zuwa Masallaci, da jiran sallah bayan sallah, wadannan sune masu katangewa (daga sabon Allah).  
Muslim (251) ya ruwaito shi.
عن عبد الله بن عمرو، قال: رجعنا مع رسول الله صلى الله عليه وسلم من مكة إلى المدينة حتى إذا كنا بماء بالطريق تعجل قوم عند العصر، فتوضئوا وهم عجال فانتهينا إليهم وأعقابهم تلوح لم يمسها الماء فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «ويل للأعقاب من النار أسبغوا الوضوء".
An karbo daga Abdullahi bin Amru yace: mun dawo tare da Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam daga Makka zuwa Madina, har muka kawo wajen wani ruwa a kan hanya, sai wasu mutane sukayi gaggawa a wajen (sallar) La’asar, sai sukayi alwala suna masu gaggawa, sai muka same su, dugadugan su suna bushe, ruwa bai shafe su ba, sai Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yace: “bone ya tabbata ga dugadugai daga wuta, ku kyauata alwala”.
Muslim ne ya ruwaito shi.

Post a Comment (0)