MU LEƘA JAMI'A

Arewa student orientation Forum

Ahamdu Bello University Zaria chapter


✔️MU LEQA JAMI'A✔️

Yau zamu kalatomaku Lambobin karramawa(Certificate award) da jami'o'in kasarnar ke karramawa ga dalibai bayan kammala karatun Jami'a fannoni daban-daban

Sanin kowa ne bayan Dalibi ya kammala karatunsa a fannin da yake nazarta,jami'iarsa zata karramasa da wata lambar shedar kammala karatun

Me ka sani akan B.sc B.ed B.A M.sc ........

KASHE-KASHEN LAMBOBIN KARRMAWA DA JAMI'O'I KE BAYARWA BAYAN KAMMALA KARATU

1. B.Ed ( Bachelor of Education)

Wannan wata lambar karramawa ce da ake bawa daliban da suke nazarin fannin koyar da Ilimi zallah (Faculty of Education) 
Misali B.Ed Islamic studies ko kuma B.Ed Hausa da sauran su.

2. B.sc (Bachelor of Science)
Wannan lambar karramawa ce da ake karrama daliban dake nazarin kimiyya wato (Science)
Misali:
B.sc Chemistry ko B.sc Biology da sauransu.

3. B.sc Ed (Bachelor of Science Education) wato wannan Lambobin karramawa ce da ake kira (Double award) wadda ana karrama daliban da suka yi nazarin kimiyyar ilimi mai cakude da Dabarun koyarwa.
misali B.sc ed chemistry d.s 

4. B.A. (Bachelor Of Art ) wannan ma lamabar karramawa ce da ake karrama dalibai masu Nazarin sashen ilimin zube, ba tare da sarrafashi da dabarun koyarwa ba.
Misali 
B.A Hausa,B.A English B.A Arabic B.A History d.s 

5.B.eng. Wannan fanni ne ga Daliban da suka Yi nazari bangaren Injiniyanci(Engineer)
6 M.sc (wannan lamba ce da ake karrama dalibai masu karatun Digiri ta biyu a fannin Kimiyya zallah
Misali 
M.sc chemistry d.s 

7. M.sc ed (Master's in science Education) wannan lambar karramawa ce da ake karrama dalibai masu digiri ta biyu kan Nazarin kimiyya tare da dabarun koyarwa 
Misali 
M.sc ed chemistry d.s 

8. M.ed (Master's in Education) wannan lamabar karramawa ce da ake karrama dalibai masu digiri ta biyu kan Nazarin sashen dabarun koyarwa.
Misali
M.ed Islamic M.ed Adult Education, d.s
9. LLB wannan ita ma lambar karramawa ce da ake karrama dalibai masu nazari a fannin shari'a wato (LAW)
10. MBBS wannan lambar karramawa ce da ake karrama dalibai masu nazari a fannin kiyon lafiya.
Misali. Medicine

11. P.hd (Phylosophy of Doctoring Degree) wannan lambar karramawa ce da ake karrama dalibai masu digirin digirgir wato digiri ta ukku

Muna godiya da kulawarku 


Ku kasance da 
Arewa student's orientation Forum


Comr. Rufai Abdullahi Dole 
08162852416
@ASOF2020 Whatsapp 08038485677


Post a Comment (0)