NASIHOHI ZUWA GA SOJOJINMU 02


NASIHOHINMU ZUWA GA SOJOJINMU 02

Kai dan uwa musulmin soja ko Dan sanda ko wani jami'in tsaro ko mai gwagwarmaya Dan Al'umma... Wanda Allah yasa ka kasance a kasar musulmai, kayi yaki da gwagwarmayarka Dan Allah da daukaka Kalmar Allah sai Allah ya taimakeka a cikin al'amuranka, kada kayi yaki ko gwagwarmaya Dan kawai kare kasarka ko kare yan kasarka, A'a bayan haka anason ka cakuda Niyyarka ta yin yaki da Niyyar kare Addinin Allah (s.w.t) da mabiya Addinin Dan Daukaka Kalmar Allah (s.w.t).

Shaikh Muhammad Ibnu Sãlih al-Uthaimeen [Rh] yana magana akan yadda ya kamata mayaki (soja ko waninshi) musuli da yake a kasar musulmai ya kasance sai yace:

"...يجاهد أعداء الله لتكون كلمة الله هي العليا، لا لأجل أن يدفعوا عن الوطن من حيث إنه وطن، لأن الدفاع عن الوطن من حيث هو وطن يكون من المؤمن والكافر، حتى الكفار يدافعون عن أوطانهم، لكن المسلم يدافع عن دين الله، فيدافع عن وطنه لا لأنه وطنه مثلا، ولكن لأنه بلد إسلامي، فيدافع عنه حماية للإسلام الذي حل في هذه البلد.

“...Musulmai zasu yaki makiya Allah dan Kalmar Allah ta kasance itace a sama, ba wai dan kawai su kare kasa dan tana kasa ba, domin tsantsar kare kasa dan kasancewarta kasa ana samun hakan daga mumini da kafiri, hatta kafirai suna kare kasashensu, amma shi musumi -anason ya kasance- yana kare Addinin Allah ne, Misali ya kasance yana kare kasarshi ne amma ba dan kawai kasar tana kasarshi ba, A'a sai dan kasancewar kasar kasar musulunci ce, Dan haka sai ya bawa kasar kariya dan kare musuluncin da yake cikin kasar.”

KUMA YACE:
يجب على طلبة العلم أن يبينوا للناس أن القتال للوطن ليس قتالا صحيحا، وإنما يقاتل لتكون كلمة الله هي العليا، وأقاتل عن وطني لأنه وطن إسلامي، فأحميه من أعدائه وأعداء الإسلام، فبهذه النية تكون النية صحيحة، والله الموفق.
(شرح رياض الصالحين ١/ ٣٥)

“Ya zama wajibi akan daliban ilmi su bayyana wa mutane cewa yaki dan kasa ba ingantaccen yaki bane, kawai ana yin yaki ne dan Kalmar Allah ta kasance itace a sama, Zan yiwa kasata yaki ne dan kasancewarta kasar musulunci, dan in kare kasata daga makiyanta da makiyan musulunci, DA WANNAN NIYYAR NE NIYYA ZATA KASANCE INGANTACCIYA, Allah ne mai datarwa.

✍Abubakar Ibrahim Assalafy.
Post a Comment (0)