NASIHOHINMU ZUWA GA SOJOJINMU 01
An karbo hadisi daga Sayyidna Abu musal-ash-ariy [R.a] yace:
سئل رسول الله -صلى الله عليه وسلم- عن الرجل يقاتل شجاعة، ويقاتل حمية، ويقاتل رياء، أي ذلك في سبيل الله؟ فقال رسول الله -صلى الله عليه وسلم-: من قاتل لتكون كلمة الله هي العليا فهو في سبيل الله.
(البخاري ٢٨١٠ و مسلم ١٩٠٤)
“An tambayi Annabi (s.a.w) dangane da mutumen da yake yaki dan ya nuna jarumtaka, da kuma Wanda yake yaki dan kabilanci, da kuma Wanda yake yaki dan riya, waye a cikinsu Wanda yake yaki Na Fisabilillahi (Dan Allah)? Sai Annabi (s.a.w) yace: «WANDA YAKE YAKI DAN KALMAR ALLAH TA KASANCE ITACE A SAMA TO SHINE YAKE YAKI DAN ALLAH»”
A cikin wanna hadisi Annabi (s.a.w) ya karantar da cewa Duk Wanda zaiyi yaki da wata manufa wadda ba daukaka Kalmar Allah (s.w.t) bace to ba Dan Allah yake yakin ba,
Dan haka abinda ya kamata shine duk wani musulmin Soja ko Dan Sanda dasauran jami'an tsaro da masu gwagwarmaya da kai komo Dan Al'umma, suyi kokarin kudurce yi Dan Allah da daukaka Kalmar Allah a Zukatansu, idan sukayi haka zasu samu Lada da La'ada, Zasu samu Lada a wajen Ubangijinsu Allah (s.w.t) da kuma La'ada a wajen Gwamnatin da ta daukesu aiki.
Abin nufi dai su kudurce yi Dan Allah a zukatansu sai Allah ya duba kyakkyawar Niyyarsu ya taimakesu.
Dan haka: Kai dan uwa musulmi Soja ko Dan sanda ko Dan gwagwarmaya...: Kada kayi Yaki Dan Kawai Nuna Jarumta, Ko Dan kawai Kare Kasarka/Kabilarka, ko Dan kawai Samu matsayi ko Nuna matsayinka...!
Allamah Ibnu Uthaimeen [Rh] yace:
فقد سئل الرسول صلى الله عليه وسلم عن الذي يقاتل على أحد الوجوه الثلاثة، شجاعة، وحمية، وليرا مكانه.
أما الذي يقاتل شجاعة: فمعناه أنه رجل شجاع، يحب القتال، لأن الرجل الشجاع متصف بالشجاعة، والشجاعة لابد لها من ميدان تظهر فيه، فتجد الشجاع يحب أن الله ييسر له قتالا ويظهر شجاعته، فهو يقاتل لأنه شجاع يحب القتال.
الثاني: يقاتل حمية، حمية على قوميته، حمية على قبيلته، حمية على وطنه، حمية لأي عصبية كانت.
الثالث: يقاتل ليرا مكانه، أي ليراه الناس ويعرفوا أنه شجاع، فعدل النبي صلى الله عليه وسلم عن ذلك، وقال كلمة موجزة ميزانا للقتال فقال: «من قاتل لتكون كلمة الله هي العليا فهو في سبيل الله»
(شرح رياض الصالحين ١/ ٦٤-٦٥)
“Hakika an tambayi manzo (s.a.s) dangane da Wanda yake yaki Dan dayan ababe uku:
1-Nuna Jarumta.
2-Dan Kabilanci.
3-Dan Nuna matsayinshi.
Wanda yake yaki Dan Nuna Jarumta ma'anarshi shine: Dan ace shi mutum ne jarumi da yake son yaki, domin jarumin mutum ya siffantu da Jarumta, ita kuma Jarumta dole ne a samu filin da za'a bayyanata, Sai kaga Jarumi yana son Allah ya hore masa yaki Dan ya Bayyana Jarumtarshi kawai, Sai yayi yaki Dan kawai shi jarumi ne yana son yaki.
WANI KUMA: Yana yaki ne Dan Kabilanci, Kabilancin Mutanenshi, ko Kabilancin Zaurensu/yarensu, ko Kabilancin kasarshi, ko wani nau'in Kabilancin daban.
WANI KUMA: Yana yaki ne Dan aga matsayinshi (a Jarumta da iya yaki) Dan mutane du ganshi su San cewa shifa Jarumi ne.
Sai Annabi (s.a.w) yayi Adalci a dangane da hakan ya fadi kalma takaitacciya da zata kasance ma'aunin yaki yace: «DUK WANDA YAYI YAKI DAN KALMAR ALLAH TA KASANCE ITACE A SAMA TO SHINE YAKE YAKI DAN ALLAH».
Allah yayi mana muwafaqa.
✍Abubakar Ibrahim Assalafy.