SHIN MUSULMI ZAI IYA YIN SALLAH A COCI?


MUSULMI ZAI IYA SALLAH A COCI ! ! *Tambaya:* Assalamu alaikum, Malam Shin ya halatta musulmai su yi sallah a coci kamar ranar juma'a ? *Amsa:* Wa alaikum assalam, da yawa daga malamai sun tafi akan haramcin hakan ko kuma karhanci saboda coci ba ta rabuwa da hotuna, kuma mala'iku ba sa shiga dakin da yake akwai hotuna ko kare a ciki, kamar yadda ya zo a Sahihil Bukhari. Ibnu Khudaamah ya rawaito halaccin sallah a coci mutukar tana da tsafta daga Umar dan Abdulaziz da Auza'i, da wasu jiga-jigan magabata, ya Kafa hujja da cewa: Annabi s.a.w. ya yi umarni da mutum ya yi sallah duk inda ta riske shi, kamar yadda ya yi bayanin hakan a Al-Mugni 1/407. Zance mafi inganci, In har akwai lalura ta rashin wurin sallah ya halatta musulmi ya yi sallah a coci kamar su rasa inda za su yi jumaa, kamar yadda Abu Musa Al-ash'ary ya yi sallah a wata Coci mai suna Nahya a Damashka, hakan ya zo a Musannaf a hadisi mai lamba ta: 4871, in babu kuma to haramun ne. Allah ne mafi sani. *Amsawa:* 16/10/2016 *DR Jamilu Zarewa*

Post a Comment (0)