LABARIN KYANWA DA BERA
Akwai wata itaciyar kuka a bayan wani gari. A gindin itaciyan nan akwai wani bera, a cikin kogonta kuma ashe akwai wani muzuru na kwana. Kukar kuwa cikin gonar wani mutum ta ke.
Kullum dare sai muzurun ya fito ya je ya yi ta wa mutumin nan barna. Da mutumin ya ga haka, sai ya samo wata raga ya yi tarko, don ya kama kome ke shiga ke yi masa barna. Allah ko ya ba shi sa’a. Da asalatu ran nan muzurun ya ga beran, ya zabura zai kashe, zai ya fada cikin tarkon, ya yi ya yi ya fita, ya kasa.
Bera kuwa da ya waiga ya ga tarko ya kame muzurun, sai ya yi rawa yana murna. Yana nan yana murna, ya duba haka cikin kara kusa da raminsa, sai ga wani maciji nan yana jira ya rabo da muzuru ya hadiye shi. Ya duba sama don ya hau, sai ya ga shirwa na kewaya, tana jira ya motsa ta fyauce shi.
Bera ya tsaya, ya rasa inda za shi. Abu ya zama masa gaba siyaki baya damisa. Yana nan sai ya tuna wata dabara, ya ce, “Na san dai da maciji da shirwa ba mai iya zuwa kusa da muzuru. Yanzu ba abin da ya fi sai in je wajen muzuru, in ce ya rantse ba zai sake cutata ba, ni ko in cinye igiyar ragan nan in sake shi.”
Sai ya tafi ya tambaye shi. Muzuru ya ce, “ina za a fara wannan aiki? Ka fid da ni daga halaka, sa’an nan in cuce ka? Ai ka kubutad da ni, mun zama abokai ke nan har abada.”
Bera ya ce, “Bari in jarraba alkawarin nan naka in gani, in gaskiya ne. Zan kurda tsakanin kafafunka in gani in ba ka cuce ni ba. Amma fa ka sani in ka halaka ni, ka halaka kanka ke nan.”
Muzuru ya ce, "Ai ni ba na magana in tayar."
Bera ya kurda ko'ina, muzuru bai motsa ba. Da maciji ya ga haka sai ya sulale, kada muzuru ya sami kubuta ya gama masa aiki. Shirwa ita kuma ta yi nata wuri, don tana tsoron muzuru.
Muzuru ya ce wa bera, “Aboki, yi maza ka cinye igiyoyin nan, ko na tsira. Ko yaushe na motsa sai in ji sun kara daure ni.”
Bera ya ce, “Yi hakuri dai kadan, igiyoyin ke da karfi.” Don wayo sai ya takarkare, kamar yana cin igiyar da karfi, amma sannu ya ke yi, yana cewa a ransa, “In na yi maza na kwance shi, ban yi tsammani zai bar ni ba. Amma in na ja aiki sannu sannu har mai gona ya zo, sa’an nan sai ya kama gabansa, ba zai nufe ni ba.”
Muzuru ya rika duban bera, yana cewa, “Don Allah yi maza, gari ya waye, yanzu mai gona ya zo ya ga abin da ya faru. Kasan ko, in ya same ni nan, na lalace.”
Bera ya ce, “Gabanka ya bar faduwa, iyakar kokarina na ke yi. Ban da ni ba beran da zai yarda da kai ya taimake ka.”Ya ci gaba da tauna sannu sannu, yana barin wadansu.
Can sai suka hangi mai noma tafe, yana sabe da bota. Muzuru ya ce wa bera, “Ga shi can tafe, ga shi can tafe, don Allah yi maza.” Bera ya kama aiki da karfi. Manomi ya kusa kawowa, ya tsunke raga duka. Muzuru ya gudu ya fada daji. Bera ya ruga ya shiga raminsa.
Manomi ya rika tafa hannu yana cewa, “Kash! Ya cinye ragar, amma bari, gobe na sake dabara.” Ya kwashe, ya koma gida.
Da gari ya waye kashegari muzuru ya zo bakin ramin bera, ya ce, “Abokina, abokina, fito mu yi tadin abota.”
Bera ya yi dariya da ya ji wannan zance na muzuru, ya ce, “Wane aboki? Ai muddin kana nan ba ka ganina na leko. Da ma kaddara ta sa mu aminci, ba wata abota ce mai dorewa ba, ta fatar baki ce, tun daga jiya kuwa muka babe. Yadda ruwa ke abokin gabar wuta, haka na ke abokin gabarka. Da ma ka dangana. Wannan hadari mun haye shi, sai wata rana.”
Da muzuru ya ji haka sai ya tsuguna nan, ya yi ta rantse-trantse, ya kalallame shi da baki, yana cewa, “Fito, mu sami wurin zama, ni ba zan cuce ka ba. Kuma da ya ke ni na fi ka karfi, ko wane abu na ga zai cuce ka na yi kokarin in tsare maka shi.”
Ya dai sami dan beran nan, har ya yarda da maganarsa, ya fito. Ya kewaya, bai ga ya yi masa kome ba, sai ya ce, “I, ashe dai gaskiyarka, ko cikin kyanwoyi akwai ‘yan halas da yawa.”
Muzuru ya ce ya kwashe kayayyakinsa da ya tara, su koma cikin kogon kuka inda ya ke, don can ya fi yalwa. Bera ya yi ta kwaso kayayyaki masu yawa wadanda ya ke tarawa, domin lokacin dari ya yi kwanciyarsa cikin rami, ba ya fitowa, balle ya sha dari.
Da muzuru ya ga kayan da bera ya tara, ga su daddawa, ga mai, ga nama, ga fura, ga cuku, ga kayayyaki barkatai, sai kunya ta kama shi, don ba shi da wani abu gidansa.
Ya tambayi bera inda ya samo wadannan kaya cikin daji. Bera ya ce, “Wajen mai gonan nan da ya kama ka. Kullum matarsa ta kawo masa a nan gona, kafin ya kai kunyar da ya fara ya zo ya ci, ni ko sai in yi ta diba, ina kawowa gida da gudu, ina komawa. Wadansu ko ma ta wajen ubana na gaje su.”
Muzuru ya ce, “Sai haka.” Shi kuma ya shiga nasa kokari, bera kuma ya sake ta da himma, suka kara bisa ga abin da ya zo da shi.
Da suka tara, sai suka tsaya shawarar inda za su boye. Muzuru ya ce, “Ba inda ya fi masallacin can na bakin kofa.” Suka dauki kaya, suka sami wani wuri can suka boye suka komo gida suka shiga hidimar ci da kawunansu kullum.
Suna nan zuane, ran nan muzuru ya ji kasala ta kama shi, ga shi kuwa yana jin yunwa, dari kuwa bai kama ba, balle, a duba ajiya. Sai ya tafi wurin bera, ya ce, “An aiko mini daga cikin gari wai wata kanwata ta haihu, yau kuwa ne suna. Ina so in tafi yanzu, kai sai ka zauna ka share gida, don ba za mu tare ba, bama halin ‘yan Adam ba iri daya ba ne. Abin da wani ya gani ya kyale, in wani ya gani, ba ya kyalewa.”
Bera ya ce, “Hakanan ne, amma fa kada ka manta da ni cikin kayan suna.”
Muzuru ya ce, “Haba, in na manta da kai, in tuna da wa?” Ya nufi gari. Da ma karya ya ke yi, ba wanda ya gayyace shi suna, wajen ajiyarsu ya ke so ya je ya ci. Da ya ci ya koshi, sai ya sami wuri ya kwanta yana lasar gashi, yana gurnani. Can da rana ta yi, sai ya komo gida.
Ko da bera ya hango shi, sai ya tarye shi da murna, yana tsammani ya rago masa wani abu, ya fara cewa, “Me aka samu?” Muzuru ya ce, “Namiji.”
Bera ya ce, “Me aka sa masa?”
Muzuru ya ce, “Wuyar-aiki-ba-a-fara-ba.”
Bera ya ce, “Wuyar-aiki-ba-a-fara-ba? Ai ko wannan suna yana da ban mamaki. Haka sunayen zuriyarku su ke?”
Muzuru ya ce, “Mene ne abin mamaki ciki, ku da ku ke sa wa naku ‘ya’yan Damburuntu fa?”
Bera da ya ga kamar ya yi fushi, sai ya kyale. Da aka kwana biyu kuma, muzuru ya ce an sake haihuwa a gidansu, za shi wajen suna. Bera ya ce, “To, amma don Allah yau kada ka manta da ni, ka san ran nan ba ka rago mini kome ba.”
Muzuru ya ce, “Yawa aka yi a wurin, amma yau na yi kokari in samo maka ko da ‘yar tsokar nama biyar.” Ya fita, bai zame ba sai masallaci, ya shige, ya sami ajiyar ya ci ya koshi, ya komo waje ya kwanta. Da rana ta yi, ya tashi ya koma.
Bera ya tambaye shi ya ce, “Ina tawa ragowar dina, ko kuma yau an yi yawa ne?” Muzuru ya yi biris da shi. Sai kuma ya bar wannan tambaya, ya ce, “Ina sunan da aka sa wa jarinin kuma yau?”
Muzuru ya ce, “Yau-da-gobe-ba-ta-bar- kome-ba.”
Bera ya ce, “Yau-da-gobe-ba-ta-bar-kome-ba?” Mts, wadannan irin sunaye naku ban taba jinsu cikin littattafammu ba.” Muzuru bai sake ce masa ci kanka ba.
Ran nan kuma ya ce an gayyace shi, ya tafi ya cinye sauran ajiyar da ta rage, ya dawo. Bera ya tambaye shi sunan yaro, ya ce, “Ta-faru-ta-kare.” Don gudun zuciyar muzuru, bera bai ce kome ba, sai suka shiga sha’aninsu. Daga ran nan ba a sake kiran muzuru zuwa wajen sun ba, ‘yan’uwansa suka rabu da haihuwa.
A kwana a tashi dari ya tsananta, sai bera ya ce wa muzuru, “lokacin duba ajiya fa ya yi.”
Muzuru ya ce, “Tun kwanan baya na so in gaya maka na yi gudun kada ka ga karayata.”
Suka tashi suka nufi masallaci, muzuru na tafe na yi wa bera gwalo a kaikaice. Da suka isa, bera ya duba, bai ga ko burbudi ba. Ya yi shiru, ya dubi mzuru, ya ce, “To, haka ka yi mini? Na dai gane abin da ya faru. Ashe nan ka ke zuwa, kana cewa wai wani an gayyace ka gun suna. Ran da ka fara ci ka ce wai sunan yaro ‘Wuyar-aiki-ba-a-fara-ba.’ Da ka koma ka ce, “Yau-da-
gobe-ba-ta-bar-kome-ba.’ Da ka zo na karshe ka cinye saura ka ce wai sunan jariri…”
Muzuru ya fusata, ya ce, “Ka rufe baki tun da girma! In na sake jin ka ce M, nan yanzu ina gama maka aiki.”
Dam beran nan na shiri ya ce, “Ta faru ta kare,” muzuru ya kwabe shi. Saboda haka kafin ya yi shiru sai ga ‘T’, ta fita ta bakinsa. Ko da muzuru ya ji ‘T’, bai tsaya jiran wani abu ba, sai ya fada wa bera ya lakwame shi.
Allah ya ba ka nasara, ka ji cutar shigege. Abin da zan kare ka da shi, in kai basarake ne, kome za ka yi nemi Sarakuna, malami ya nemi maluma, talaka ya nemi talakawa. Kowa ya ki bin abin nan da na fadi, in ya daka ta wadansu, shi ko ya rasa turmin daka tasa.