DUK MATAR DA TA SHA AZUMI A RANAR "JAJIBERIN SALLAH" WAI DOMIN AIKACE-AIKACEN GIDA TANA GUDAN WAHALA, TOH ZAKIYI KAFFARA "AZUMI 61" A JERE,



DUK MATAR DA TA SHA AZUMI A RANAR "JAJIBERIN SALLAH" WAI DOMIN AIKACE-AIKACEN GIDA TANA GUDAN WAHALA, TOH ZAKIYI KAFFARA "AZUMI 61" A JERE, MATA WALLAHI KU JI TSORON ALLAH WALLAHI

TAMBAYA 

Assalamu Alaikum malam akwai wata neighbour na ita kullum cewa take ran jajiberi zatasha azumi wai saboda akwai aiki sosai gashi wai maybe zata shiga kasuwa don haka ba zata iya wahala ba ita kam zata sha azumi nace mata ai bai kai hujja ba da zai hanata yin azumi tunda shigar ta kasuwa ba dole bane a addini mijin ta ne yakamata yayo shefenen sallah ba, itama in yace taje ta ce tana gudun wahala ya je ko ya tura kannen sa tunda kullum su suke shefenen Amma takasa fahimta kuma na gaya mata wannan baikai hujjar da zaisa Tasha azumi, kuma ta ce ai ita tana Shayarwa don haka zata ajiye Azumin, kuma malam tun Farkon Azumi tace ita ba zata ajiye Azumin ta domin Shayarwa ba domin tana ganin zata iya yin Azumin, kuma tunda aka fara Azumin bata sha ba, domin idan ma ruwan Nonon ne akwai shi yaron ta watan sa 6, ta san Cewa bata ma daga Cikin waɗanda za su jikkata har su ajiye Azumin domin Shayarwa Shiyasa tace ba za ta Ajiye ba, amma yanzu tana Cewa ai Ranar Jajiberi Zata sha, don zatayi Aikin Sallah kuma ga Shayarwan. don Allah me Hukuncin ta? Sannan don Allah kuyi faɗakarwa akan hakan domin wasu suna Kuskure.

           
*AMSA*👇


Wa Alaikis Salaam:-

Toh Ƴar Uwa ki tabbatar mata da Cewa idan ta Kuskura ta Sha Azumin ta akan Abunda kika yi Bayani, Shakka Babu ki gaya mata zata yi Kaffarar Azumi 61 a Jare, idan ko ba ta yi su anan Duniya ba, za ta je Ranar Alkiyama ta tarar da Azabar Ubangijin ta wanda yafi wanda zata ji shi a Ranar da zata yi Aikace-aikacen cikin gidan. 

Ba hujja ba ce cewa zata Wahala sannan ai tana Shayarwa wai kuma Ace har zata yi Tunanin Cewa zata ajiye Azumin ta wai domin Ayyukan cikin gidan ta, wani Aiki ne ma zata yi wanda har zata wahala? Wallahi a Cikin Aikace-aikacen cikin gida da zata yi a Cikin Kaso 10% daker ne zata iya ɗaukar kaso 2% na wata Matar, idan an bata aikin wata tayi koda ba Shayarwa take yi ba wallahi ba zata iya yin sa ba, amma Wannan itama bata ce zata ajiye Azumin ta ba sai ita, sannan itama tana Shayarwar kuma yaron ta bai wuce wata 2 ko 3 ba, amma bata taɓa tunanin cewa ga Ranar da wai zata Ajiye Azumin ta ba, wai sai ita sannan kina gaya mata cewa ga Hukuncin Allah tana cewa A'a sai tayi ita, toh ki sanar da ita Cewa idan ta sha zatayi Kaffara Azumi 61.

Inda ace Yau tun Farkon Azumin ta bata samun tayi Azumi Kullum shan Azumi take yi dalilin tana Shayarwa, idan ta ci gaba da yin Azumin ta Lallai ne Yaron ta zai sha Wahala domin ba zai samu Abincin sa ba wato Nono, sai tun farkon Azumi tana Shan Azumi har zuwa ranar JAJIBERIN Sallah ba ta Samu Yin Azumin ba, nan ne zata Samu Rangwame, amma tana yin Azumin ta tunda aka Kama wata tana yi har mata tafi wata wanda bata Shayarwar, amma wai har take tunanin cewa zata Ajiye Azumin ta a Ranar JAJIBERIN Sallah, to Zata yi Kaffarar Azumi 61 a Jere idan ta Kuskura ta ajiye Azumin, idan kuma batayi su anan Duniya ba, zata je Ranar Alkiyama ta karɓi ta sha Azabar da ya wuce Wahalar da zata sha a Ranar JAJIBERIN Sallah ɗin.

Wannan Matar ma ai Jahila Ce. Duk Wanda Allah ya haɗa shi zama da Jahili Akwai aiki babba a kansa wallahi. 

Saboda haka Tinda Kin gaya mata ba ta Fahimta ba. Sai ki kyaleta idan ko zaki sake gaya mata ta chanja halin ta Shikenan.

 Ina ma ruwan Allah da wata jajiberan din sallahn ta ko kuma yiwa gidan ta Aiki? Zata je ta same shi kuma wallahi Azabar da zata sha sai yafi wanda zata ji a Ranar JAJIBERIN Sallah ɗin, Zata je ta ga yadda Mala'ikun Allah za suyi da ita.

Bata daga Cikin Jerin waɗanda za su ajiye Azumin su,

Saboda haka baya halalta ace a musulunce mutum yayi wata dabara domin sauke wani hukuncin Shari'a kanshi, kuma hakan haramun ne, kamar yadda Allah ya jirkita halittar wasu Yahudawa zuwa birrai yayin da suka yi kokarin yin wayon sun kifi. Don Haka itama idan tace bari ta nuna wayon ta ga Allah bari ta Ajiye Azumin ta Sakamakon kina gudun Wahala toh za ki faɗa Cikin Wahalar da yafi wanda za ki ji Shi a Ranar da kike son Ajiye Wannan Azumin naki.

Wahalar da take sanyawa Azumi ya faɗi a kan Mutum wahalace da ta fita daga Al'ada, wato wahalar da zata iya haifar da rashin lafiya ko salwantar rai ko wacce zata galabaitar da mai Azumi ya fita daga hayyacin sa, kamar Mara lafiya ko mai shayarwa ko tsoho Matafiyi ko yaro duka wadannan an huwace musu da su sha ruwa. Amma ke kin yi Azumi Sama da 18 ko hutu bakiyi ba tunda kina Shayarwan, amma wai sai a Ranar JAJIBERIN Sallah wai kina jin tsoron kada ki Wahala wai bari ki sha Azumi domin Zakiyi Aikace-aikacen cikin gidan ki, toh zakiyi Azumin 61, ai wannan ma isgili da wasa da ibadar Allah, kuma Hukuncin Masu isgili da ibadar Allah makomar su Wuta ne Wutar ma yana Karkashin Wutar Kafirai. Don ki Ɗauki Azumin tukuna idan Kin Suma ko ya Jikkata ki nan ne zaki fara tunanin ki ajiye amma saɓanin haka kina Lafiya Qlau kina yin Azumin ki garau amam wai Ranar JAJIBERIN Sallah kak zaki huta, toh Akwai Azumi 61 zakiyi su.

Wai zakiyi wayon shan ruwa da wannan dalili, wannan ba abu ne karbabbe ba kina Sha toh kina Cewa Haramun ne zaki Aikita, kuma ga Sakamakon ki idan kin yi hakan.

Sannan ya kamata mata wallahi ji tsoron Allah, akan Azumin kwana ɗaya wahalar shi bata kai wahalar sauran kwanakin ba, sannan ki sani Azabar sa idan kin Ajiye sa, Azabar da Allah zai miki a Kiyama sai yafi wanda Zai same ki a Ranar JAJIBERIN Sallah ɗin. Wallahi Ku ji tsoron Allah Ku ɗena sanya Son Zuciyar ku wajen Ibadar Allah akwai Ranar da Kowacce daga Cikin ku zatayi Nadamar Abunda ta aikata a Lokacin da Wannan Nadamar naki ba zai taɓa tsanani miki komai ba sai Faɗawa cikin Azabar Ubangijin ki. 

Sannan Maza, Wallahi ku Sani Cewa duk Namijin da ya sake ya Bar Matar sa ta Sha Azumi a Wannan Ranar domin tayi maka Aikace-aikacen cikin gidan ka, toh Wallahi ka shiryawa Kanka Amsar da zaka bawa Ubangijin ka, domin Annabi yace Kawo An bashi Kiwo ne, kuma Ranar Alkiyama sai An tambaye ka kan Wannan, idan ka bar ta ta sha Azumi a dalilin haka kaima ka shirya karɓar Azabar Allah na wasa da ibadar sa da isgili da kuka yi da shi. Don Haka ku Ji Tsoron Allah wallahi. 

Ba wani hujjar da Mace zata Kawo Cewa ai tana Shayarwa ne don haka a Ranar JAJIBERIN Sallah zaki ajiye Azumin ki Wannan ba hujja ba ce, inda zai zama Hujja shine ace an samu tun farkon Azumin ki ai ba ki iya yin Azumi Kullum kina Shan Ruwa dalilin Shayarwa da kike, amma Kullum kina yin Azumin kuma kina Shayarwa kuma Lafiyar ki qlau har na kin fi wata, amma wai don a Ranar JAJIBERIN Sallah Zaki wahala don haka bari ki ajiye Azumin ki, toh zakiyi Kaffara Azumi 61 a Jere. Mata nawa Ne Suke Aiki tukura fiye a naki kuma suna Shayarwa Wannan tunanin ma bai taɓa zuwa musu ba, sai ke? Haba Ɓaiwar Allah!! Wannan wacce irin Rayuwar ce haka na tunanin saɓawa Allah? Don haka duk matar da ma take da Niyyar Ajiye Azumin ta a Wannan Ranar tou ki ji tsoron haɗuwa da Azabar Allah da yafi wanda zaki ji a Ranar da kika ajiye Azumin ki domin kiyi aiki Cikin Sauki a Ranar JAJIBERIN Sallah. Allah ya tsare ya shirya Ameen. 

Wallahu A'alamu.
Post a Comment (0)