LABARIN NAN YANA ƊAUKE DA TAUSAYI SOSAI

Wani Labari mai ban tausayi

wasu iyalaine talakawa a wani kauye cikin pakistan sunada 'Da namiji Kwaya daya rak sun bashi ilimi na addini dana zamani ya zama shahararren ENGINEER yananan sai yasami wata attjira ya aura yananan a kauyen nasu tare da iyayensa sai nan take matarsa ta matsa masa tace ta gaji da zaman kauye, sai suka tattara nasu ya nasu suka koma birni ba da jimawa ba sai yaga wani talla ana neman Engineers a JEDDAH A SAUDI ARABIA kenan yaron kuwa yana da sa'a sosai sai yasamu aikin nan take ya koma can da aiki shekaru da dama yana turowa iyayensa kudi.


Gaba gaba dai kwata-kwata ya daina turo kudi kuma duk shekarar Allah sai yayi Hajj Ana haka sai ya fara mafarki a cikin baccinsa wani bawan Allah nace masa HajjINKA BA KARBABBIYA BACE.

sai abin ya dame shi yaje ya tambayi wani Malami wanda aka yadda dashi mai fassarar mafarki malamin yace masa yaje yaga iyayensa nan take ya hau jirgi sai pakistan da isarsa yaje kauyen nasu duk abubuwa sun canja masa, ba kamar yadda ya saniba. sai yaga wani yaro yayi masa kwatancin iyayensa sai yaro yace lalle akwai wata tsohuwa a gidan makanniyya wadda mijinta ya rasu bada jimawa ba (wato mahaifiyarsa harta makance akan zubar da hawaye kuma babu mai kula da ita).

kusan Allah mai karbar addu'ar iyayemmu ne ( waifa lokacin da yake mafarkin addua'a mahaifiyar ce Allah ya amsa mata kamar yadda zaku ji nan gaba).


yana shiga ya ganta a kwance tanata faman kadaici saboda shi kadai ke gare su balle ace tanada wasu jikoki kuma gashi babansa ya rasu sai yaji tana magana can ciki ciki saiya kawo kunnensa kusa da bakinta domin yaji abinda take fade.


kusan abinda yaji tana fada duk tsawom shekarun daya kwashe kamar baisan da suba a duniya, kusan iyayemmu ba kadan suke sommuba, abinda yaji tana fada shine ya Allah ka dawo mini da 'dana gida domin idan na rasu ya dinga yi mini addu'a ni kuma nayi masa fata na karshe.


inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. kunji fa ita duk bata tunanin guje masu da yayi amma sai faman nemar masa gafara takeyi. Ya Allah ka datar damu mu kyautatawa iyayenmu Allah kasa mu

Post a Comment (0)