MATSALOLIN CIWON SANYI GA MATA


ALAMOMIN CIWON SANYIN MARA NA MATA 

SANYIN MATA WANDA AKE YAÆŠAWA TA JIMA'I

 

WaÉ—ansu daga cikin alamomin ciwon sanyin mata da ake samu ta hanyar saduwa da namiji ko mace mai É—auke da ciwon : (STD/STI):

 

1. Fitar ruwa daga farji, ruwa mai kauri ko silili, kalar madara ko koren ruwa daga farji.

2. Kuraje masu É—urar ruwa da fashewa a farji , musamman wurinda pant ya rufe.

3. Feshin ƙananan ƙuraje a farji ko cikin farji

4. RaÉ—aÉ—in zafi a lokacin yin fitsari

5. Jin zafi cikin farji lokacin jima'i

6. Zubar jinin al'ada mai yawa ko zuwan jinin al'ada mai wasa, wato akan lokacinda ya saba zuwa ba

7. Ciwon mara

8. Zazzaɓi

9 . Ciwon kai

10. Murar maƙoshi/maƙogwaro

11. Kasala/raunin jiki

12. Zubar jini lokacin saduwa

13. Dakushewar sha'awa, ko rashin sha'awa ko É—aukewar ni'ima

14. Bushewar farji

15. Ƙaiƙayin farji

16. Warin farji (ɗoyi) mai ƙarfi

17. Kumburin farji da yin jawur

18. Gudawa

18. Ko rashin ganin wata alama daga cikin wadannan alamomin da muka bayyana a sama.

 

A can baya munyi bayanin ciwon sanyin mata na "toilet infection" (vaginitiies: Yeast infection & Bacterial vaginosis) wanda cutar sanyin mara ce wacce ba'a yaÉ—ata ta hanyar jima'i - wato sanyin mara wanda mace bazata iya harbin mijinta da cutar ba, wanda akafi samu daga "toilet" (bandaki/bayan gari). Duk da haka , munyi bayanin wata nau'in cutar sanyi guda 1 (Trichomoniasis) a cikin waÉ—ancan bayanan da suka gabata, wacce cuta ce da mace ka iya sakawa mijinta ciwon (STD). A wannan karon kuwa zamu yi bayani ne kaÉ—ai akan ciwon sanyin mata wanda akafi samunsa ko yaÉ—awa ta hanyar jima'i (STD/STI).

 

Ciwon sanyi cuta ce da akafi yaÉ—awa ta hanyar jima'i, wato ta hanyar saduwa da mai dauke da ciwon, shiyasa ake kiran dangin cututtukan da turanci da suna SEXUALLY TRANSMITTED DISEASES/ SEXUALLY INFECTIONS (STDs/STIs), wato CUTUTTUKAN DA AKE YAÆŠAWA TA HANYAR JIMA'I.

 

Ciwon sanyi anfi yaÉ—asa ne ta hanyar jima'i kuma maza na iya harbin mata da ciwon ko kuma su matan masu É—auke da ciwon su sakawa maza mararsa ciwon. Ciwon yafi yaÉ—uwa kuma anfi samunsa ga maza masu neman mata ko mata masu bin mazaje.

 

Haka kuma za'a iya samun cututtukan sanyi ta wata hanyar daba jima'i ba, kamar ta hanyar bada jini ga marar lafiya - jinin mai ɗauke da cutar sanyi daga wani mutum, ko haɗuwar jikin wani da wani - fata-da-fata ; wato idan fata mai ɗauke da cutar ta fashe zata iya harbin fatar wani mutum mai lafiya da cutar, ta jini ko ruwan jiki dake a jikin fatar mai cutar zuwa fatar wanda baya da cutar - wato idan akwai kafa buɗaɗɗiya komin ƙaƙantarta zuwa cikin hanyoyin jinin wanda baya da ciwon a fata zai iya samun cutar, misali ta hanyar sunbata (kissing) ko tsotsar al'aurar mai ciwon (oral sex), ko ta hanyar saka kayan sawar wata (pant) mai ɗauke da kwayar cutar mai rai, ko ta hanyar amfani da reza (razor blade) wanda wani yayi amfani da ita, rezar mai ɗauke da kwayar cutar mai rai, da kuma wasu hanyoyin na daban. Ataƙaice, ƙwayoyin halittun dake sanya cutar ana yaɗa sune daga wani mutum zuwa wani mutum, ta jini, maniyyi, ruwan farji ko ruwan jiki.

 

Alamomin ciwon sanyi ga mata sun sha banban tsakanin mata wanda ciwon ya harba. Hakan ya danganta ne da nau'in ƙwayar halittar cutar wacce ta haddasa ciwon da kuma matakin da cutar ta takai a jikin mace - ma'ana, alamomi ko matakin farko da kamuwar cutar ko alamomi na gaba bayan ta soma jimawa a jikin marar lafiyar. Haka kuma, suma yanayin alamomin sunsha banban ta fuskar tsanani ko sauƙinsu, koma rashin ganin alama ko ɗaya duk da cewa kau akwai cutar a jikin mace. A taƙaice dai, alamomin ciwon sanyin zasu iya ɓuya amma gwaji a asibiti zai iya nuna akwai cutar ko akasin haka.

 

Alamomin ciwon sanyi na " toilet infection " na iya kama da alamomin cutar sanyi da ake samu ta jima'i (STD/STI). Saidai banbancin shine hanyoyin samun cututtukan , kuma cutar sanyin "toilet infection" tafi saukin magancewa; ita kuwa cutar sanyin da ake yaÉ—awa ta jima'i (STD) nada wuyar magani da naci, musamman saboda wasu na'uin cutar daga kwayar cutar "virus" ne (kamar "syphillis" da "genital herpes"). Gwaji a asibiti shine zai iya nuna na'uin cutar da maganin da ya dace, imma "toilet infection" ko kuma cutar sanyin jima'i wacce tafi muni da wuyar magani.

 

MATSALOLIN DA CIWON SANYIN ZAI IYA HADDASAWA MACE:

 

a) RASHIN SAMUN JUNA-BIYU/ HAIHUWA: Cutar sanyi mai suna "Gonorrhea" (Gonoriya) , ƙwayar cuta ce daga halittar "bacteria" kuma zata iya laɓewa a cikin jiki ba tare da wasu alamomi ba. Itace mafi tsohuwar cutar sanyin da akafi sani. Gonoriya bata cika nuna alamun taba a jikin mace, musamman a matakin farko na shigarta cikin jiki, ba kamar ga maza ba wanda alamomin kan bayyana gare su . Mata da yawa basu san ma suna dauke da cutar ba a jikinsu. Duk da haka, tana iya zuwa da alamomi kamar fitar ruwa daga farji ko ɗan koren ruwa, mai kalar madara daga farkon cutar, yin fitsari da zafi da yawan yin fitsari, yawan zubar jinin al'adah, murar maƙoshi/maƙogwaro, jin zafi a farji yayin jima'i, da sauransu. Idan ba'a lura da cutar da wuri ba kuma aka magance ta, zata iya sanya rashin haifuwa ga mace ko namji. Tana shafar wani hangaren mahaifa da yi masa dameji, sai mace ta kasa samun juna-biyu.

 

Haka kuma itama cutar "Chlamydia" (kilamidiya), wacce kwayar halittar "bacteria" ke haddasata , na daga cikin game garin cutar sanyi wacce ke hana mace ɗaukar ciki. Hakan yafi faruwa idan mace nada cutar na tsawon lokaci ko kuma ta samu cutar wasu lokutta na rayuwarta da dama. Idan an gano cutar kuma an magance ta da wuri zai rage illa ga mahaifar mace a gaba. Cutar "Chlamydia" maɓannaciya ce da take illa a ɓoye kuma mafi yawanci bata nuna wata alama a zahiri ga mai ɗauke da cutar. Ana samunta bainar mata da yawa fiye da maza. Mafi yawanci bata nuna wata alama sai haddasa rashin haihuwa.

 

b) RASHIN JIN DADIN JIMA'I , ÆŠAUKEWAR NI'IMA , KO DAKUSHEWAR SHA'AWA KOMA RASHINTA

Sanyin gaba mai zuwa da 'yan 'kananan kuraje cikin farji , na sanya mace taji zafi wajen jima'i yayinda zakari ke kai-kawo cikin farji, wanda sau da yawa masu kurajen basu ma san suna da kurajen ba cikin al'aura, saidai suce suna jin zafi lokacin saduwa. Kurajen suna fashewa saboda da gugar zakari, sai wurin ya zama rauni. Hakan nasa mata tsoron jima'i da ganinsa abin azabtarwa gare su mai maimakon abin jin dadi. Sau tari basu san abinda ya haddasa zafin ba, wanda kuma mai yiwuwa ciwon sanyi. Ciwon sanyi na iya dakushe sha'awar mace ko namiji. Ciwon sanyi na iya haddasa bushewar gaba (vaginal dryness) wanda alamunsa shine daukewar ni'ima da 'kaikayin gaba. Idan gaba ya bushe zaiyi wahala mace da miji suji dadin jima'i in banda zafi.

Wasu daga cikin cututtukan sanyin da ake samu ta jima'i da ƙwayoyin halittu wanda ke haddasa su (a yaren turanci):

 

a) CHANCROID (bacteria) , cuta ce wacce ke zuwa da yanayin gyambo wani lokacin tare da ƙululu a hantsa.

b) CRABS (parasite), 'yan ƙananan halittu sosai , yanayin kwalkwata, masu cizo da tsotsar jini mai sanya mugun ƙaiƙayi. Ana samunsu daga gashin mara inda suka maida gidansu, ana kuma iya ɗaukarsu daga gashin gaban wani mutum zuwa na wani lokacin jima'i. Ana kuma iya samunsu ta kayan sawa, gado da sauransu.

c) GENITAL HERPES (virus) , cuta wacce take zuwa da ƙuraje masu ɗurar ruwa a baki ko kan zakari, ƙurajen masu kama dana zazzaɓin dare (fever blisters). Idan ƙurajen suka fashe sai su zama gyambo. Haka kuma za'a iya samun ƙurajen a ɗuwawu, cinyoyi, ko a dubura. Ciwon kai ko baya, ko mura (flu) mai ɗauke da zazzaɓi, ko kaluluwa da raunin jiki/kasala.

 

d) SYPHILIS (bacteria), anfi samunta wajen 'yan luwaɗi. Tana da matakai bayan shigarta a jiki. Misali, matakin farko (1): fitowar wani irin gyambo (chancre), wannan gyambon shine wajenda cutar ta shiga jikin mutum. Gyambon mai tauri, mai zagaye marar zafi. Wani lokacin abuɗe yake kuma da lema, ko zurfi musamman a hular zakari, wanda zaka ga wurin ya lotsa. Ana samunsa a zakari ko dubura ko leɓe (a baki). Ana kuma iya samun gyambon a ɓoye wani wajen cikin jiki. Mataki na biyu (2): ƙuraje a tafin hannu ko ƙarkashin tafin ƙafa ko wani sashen na jiki. 'Yar mura, zubar gashi, zazzabi marar tsanani, kasala, murar maƙoshi, ciwon kai ko ciwon naman jiki da sauransu. Mataki na gaba: mataki na gaba ko ƙarshe shine wanda cutar zata iya ɓoyewa a jiki, 'buya idan ba'a magance taba, kuma zata iya sanya ƙululun kansa/ciwon daji (tumour), makanta, mutuwar sashen jiki, matsalar ƙwalwa, kurumta, ciwon mantuwa mai tsanani (dimentia). Ana iya magance cutar cikin sauki da idan an lura da ita, da wuri, da yardar Allah.

 

e) TRICHOMONIASIS (parasitic organism) , cutar sanyi maisa warin farji, mace zata iya harbin mijinta da cutar ko mijin ga matar. Idan ya kasance miji nada wata mata ko yana neman matan waje masu cutar ko kuma macen ta taba saduwa da wani mutum mai cutar daya samo cutar daga wata mace, to akwai yiwuwar ma'aurata su samu cutar. Mazaje ba kaso suke sanin suna da cutar ba kasancewar alamomin cutar basu cika bayyana ga maza ba. Yawanci sai idan ciwon ya kama matan su suna cikin neman magani a asibiti suke gano suna da cutar. Wasu daga cikin alamomin cutar ga mata: zubar ruwa mai launin kore-da-dorawa - mai kumfa da wari, zafi wajen yin fitsari, rashin jin dadi wajen jima'i. Wannan cuta tana da hadari ga mace mai juna-biyu da abinda ke cikinta

 

f) DA SAURANSU, suna da yawa kuma alamomin wani ciwon na kama da na wani ciwon wani lokacin. Don haka bincike a asibiti shine zai nuna nau'in ciwon.

Ciwon sanyi anfi yaÉ—asa ne ta hanyar jima'i kuma maza na iya harbin mata da ciwon ko kuma su matan masu É—auke da ciwon su sakawa maza mararsa ciwon. Ciwon yafi yaÉ—uwa kuma anfi samunsa ga maza masu neman mata ko mata masu bin mazaje. Haka kuma mutum zaya iya kamuwa da ciwon ta wasu hanyoyin na daban daba jima'i ba. Kuma lallai ciwon nada wuyar magani , musamman idan mutum bai samu magani ingantacce ba. Zai iya yin wuyar magancewa saboda rashin samun sahihin magani ko daÉ—ewarsa cikin jiki ba'a magance ba. Sau da yawa zaka ga cewa mutane sukan sha magunguna domin kaiwa ciwon hari da sukar alluran likita amma hakan bai razana ciwon ba sai kaga yana wa mutane jeka-ka-dawo tsawon watanni koma shekaru da dama ba'a samu waraka ba.
Post a Comment (0)