MAZA MA'AURATA MASU ZAMA A RUMFAR MAI SHAYI


MAZA MA'AURATA MASU ZAMA A RUMFAR MAI SHAYI

Bissmillahir Rahmanir Raheem.

Assalamu Alaikum warahamatullah Wabarakatuhu. 


Sanannen abu ne cewa mazaje da yawa kan je rumfar mai shayi da safe ko da dare domin su rage zafi. Wasu daga cikin mazajen nan dai matasa ne waÉ—anda ba su damu da cin abincin gida ba, yayin da wasu kuma mazaje ne masu iyali. Haka kuma akan samu waÉ—anda ba a garinsu suke ba, don haka su ke zuwa rumfar domin cin abinci. 

Na sha tambayar kaina Shin menene dalilin da zai sa mutum yana da mata a gida kuma zai zo ya zauna a rumfar mai shayi da nufin cin abinci? Amma na kasa samun amsa gamsashiya. Hakan ya sa na fara tambayar sauran mutane domin jin ta bakinsu. Ta sanadin haka ne na fahimci cewa wasu daga cikin mazajen nan sukan je rumfar mai shayi ne kawai idan matan nasu ba sa nan ko in basu da lafiyar da za su iya girki ko kuma in ba a garin da suke da mata suke ba. Wasu mazajen kuma su kan je ne domin samun abokan hira yayin da su kuma matan an barsu a cikin gida su ji da kansu. Wasu mazajen kuma suna so ne su ci abinci mara nauyi saɓanin irin wanda suka bayar a dafa a gida. Hallau, a kwai wasu kuma da kawai suna zuwa ne saboda sun riga sun saba da zuwa tun suna matasa.

To a ƙarƙashin haka, sai kuma na gano cewa mata da yawa suna shiga cikin damuwa a sakamakon irin wannan ɗabi'a da mazajensu ke yi. Wasu ma har takan kai ga rabuwar auren. Dalili kuwa shi ne, matan suna ƙorafi da cewa irin waɗannan mazaje ba sa basu kulawa yadda ya kamata, irin waɗannan mazaje ba sa ciyar da su irin abinda ya kamata amma su suna iya ci a waje, ba sa basu isashen lokacin da ya dace amma sun iya ba wa wasu a waje da dai ƙorafi-ƙorafe makamantan waɗannan.

To, bincikena ya tabbatar min da cewa wasu daga cikin zarge-zargen matan nan gaskiya ne, yayin da wasu kuma ba haka suke ba. Don haka ni a nan ba wai zan zaɓi wani ɓangare bane in ɗibga musu laifi. Amma ku matan da kuke fuskantar haka, mai zai hana ku yi tunanin menene dalilin da yasa mazanku ke muku haka kuma ku gyara in kun gano kuna da laifi? In kuma ba ku da laifi mai zai hana ku ci gaba da yi musu addu'a kan Allaah ya maido muku da hankalinsu gida? Ku sani cewa ƙorafi da zarge-zarge ba za su yi maganin matsalar ba, amma addu'a za ta iya.

Ku kuma mazajen da kuke aikata irin hakan, me zai hana ku yi ƙoƙarin ganin kun gyara saboda a samu zaman lafiya mai ɗorewa a tsakaninku da iyalan naku? In ma matayen ne su ke tirsasaku fitowa, me zai hana ku ma ku ci gaba da bin su da nasiha da addu'ar Allaah ya ganar da su gaskiya su gyara halayen nasu? Tabbas fitowar ku waje ku zauna ba zai yi maganin matsalar ba, duka ko zagi ba za su iya ba, amma nasiha da addu'a za su iya in shaa Allaah.

Da fatan masu rumfunan siyar da shayi da maÆ™wabtansu masu siyar da nama ba za su É—auki wannan 'yar tunatarwa da zafi ba, domin kuwa har gobe matasa marasa aure sun fi masu aure yawa. 


Allaah ya azurta mu da kyakyawar fahimta tare da zaman lafiya mai É—orewa Aameen.

➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖
Subhanak Allahumma Wabi Hamdika Ash Hadu Anla Ila Ha Illah Anta Astagfiruka Wa Atubu Ilaika. 

Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuhu. 

<••••••••••••••••••••••••••••>
      Haiman Raees 
<••••••••••••••••••••••••••••>

        08185819176

Twitter: @HaimanRaees 

Instagram: Haimanraees 

Haimanraees@gmail.com 

Miyan Bhai Ki Daring
Post a Comment (0)