*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*
*🍉🍅JIKIN DAN ADAM // 03🍍🍊*
*(Fitowa ta Uku)*
*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*
Wasu masana wadan da ba su ma da alaqa da Muslunci sun ce: Azumi yana rage mummunar qibar ga dan adam, ya tsarkake fatarsa, ya yi maganin wani mummunan sinadari na jikin mutum wanda zai riqa yi masa barazana, ya gara tsarin jijiyoyin jiki, ya rage radadin jiki ko kumburi, ya qara wa mutum qarfin tabbatar da abubuwa, ya sauqaqa wa mutum damar gamsar da iyalinsa ta wajen ciyarwa, ya kuma sami isasshen lokacin zama da su, wata qila ma abu mafi girma shi ne mutum ya kyautata tsarin lafiyar jikinsa.
Wannan bincike na su kamar fassarar ayar Qur'ani ce da Allah SW yake cewa:
وَأَنْ تَصُومُوا خَيْرٌ لَكُمْ إِنْ كُنْتُمْ تَعْلَمُون.
In dã kun sani yin azumin shī ne ya fi muku.
Don duk abin da kake buqata na tsarkakewa azumi ya tattara shi, kamar ba da kariya ga ido, kunne, hanji, zuciya da qwaqwalwa, sannan ko yunwa da takan gallabi mutane sai da shari'a ta kwadaitar da a riqa yalwata wa juna, inda ta yi nuni da cewa Manzon Rahama ya fi yin kyauta a watan, sai mutane suka kama don yin koyi da shi.
Abubuwan da musulmi zai amfana da su ta wurin yin azumi bayan kiwon lafiyarsa akwai:
⚫Shiga Aljanna ta qofar da ake kira rayyan.
⚫Azumi dalili ne na samun rahamar Ubangiji.
⚫ Amsar addu'a da Ubangiji (SWT) yake yi a wa tan Ramadana.
⚫ Yakan matso da bawa kusa da Ubanginsa, masamman yadda tsoron Allan yakan yawaita a zuciyar mutane, su guji aikata haram, su halarci sallah.
Babu ko shakka sallah ita ce mafi girman ibadu, kuma Allah SW ya bayyana cewa takan hana zina da sauran ababan qi, to amma fa sai in an yi sallar kamar yadda shari'a ta ce mutum ya yi, don in ba haka ba to ba a karbe ta ba bare ta gyara sauran shika-shikan musluncin, azumi kuwa in dai za a yin, to da wahala ba ka ga ya tura mutum masallaci ba, ko mutum bai je wajen tafsiri ba za ka taras ya kunna a rediyon motarsa ko ta dakinsa.
⚫Azumi yakan zama ma mai ceto ga bayin Allah ranar qiyama.
Domin tsarkake mutum daga duk wasu munanan cututtuka na boye da na sarari, za ka iske cewa, rayuwar mutum duk gaba dayanta zagaye take da sabubban da za su sanya shi azumi domin tsarkake zuciyarsa da kuma sauran jikin nasa gaba daya, shi ya sa ma azumin ya karkasu zuwa gida-gida, akwai wanda ya zama dole a yi, shi ma din yakan kasu har zuwa gida uku:
(1) Azumin watan Ramadan wanda ya zama wajibi a kan duk wani musulmi, dole dai mutum a rayuwarsa ya kasance ya karkade zuciyarsa gaba dayanta daga munanan ayyuka, wadan da ake iya dauko su ta kunne ko ta sauran sassan jiki.
Ya kuma gyara alaqarsa da duk wani dan adam, yadda koda tsokanarsa aka yi zai iya cewa "Ni dai azumi nake yi" don dai kar a sami wata taqaddama wace za ta bata abin da ake qoqarin cimma wa, ya sami cikakken lafiya wanda zai fuskanci sauran ibadu da su, don watan azumi yakan kwatanta sauran shika-shikan musluncin ne, yadda kowa kan bazama zuwa ga Allahi shi kadai, ga yawaita sallah a cikin jam'i da rana, sai tarawihi wato tahajjudi da daddare, ga yawaita sadaqa da mutane ke yi a watan, wasu ma sun fi fitar da zakka in watan ya kama, ga haduwar duniya kakaf dinta kan yin ibada qwara daya a lokaci guda.
(2) Sai kuma azumin da ya wajabta amma bisa lalura ko wani dalili, kamar dai azumomin kaffara, mutum in ba wani zabin yake da shi ba azumin kan zama masa wajibi, yadda ruhinsa da zuciyarsa da jikinsa gaba daya za su koma ga mahalicci, har mutum ya tabbatar a cikin zuciyarsa cewa lallai ya yi kuskure a baya, jikinsa ko na ce cikinsa ya gaya masa, daga bisani sai ya dora azamar cewa ba zai koma zuwa ga kuskuren baya ba, ya kuma yi nadamar abin da ya aikata, daganan komai nasa zai tsarkaka.
(3) Sai kuma azumin da mutum ya wajabta wa kansa, kamar dai azumin alwashi, wadannan har da kasancewarsu wajibi, sai dai wani daka ciki sau daya kadai yake kasancewa a kan bawa, sauran kuwa sai in ta dauro, wani har ya gama rayuwarsa wata qaddara ba tilasta masa yin azumi ba, to amma da mutum zai yi azumin ba ko shakka zai amfana a zuciyarsa, ruhinsa, jikinsa, da kuma lahirarsa gaba daya, gami da kyautata alaqarsa da jama'a ta wajen guje wa duk wani abu da zai iya kawo tashin tashina, a nan YIN AZUMIN SHI NE YA FIYE WA DAN ADAM, ALLAH YA YI GASKIYA.
Zamu ci gaba insha Allah.
*Gabatarwa: Zauren Sunnah*
*Gamasu Sha'awar Bibiyar Karatukanmu Akan Shafukan Sada Zumunta Kamar WhatsApp da Facebook Zasu iya Bibiyarmu ta Wannan Hanyar*
*_Sai kuturo da Cikakkiyar Sallama. Da Cikakken Suna Tare da Adreshi ta Wadan nan Numbobin_*
_*WhatsApp Number*_
+2348039103800.
+2347065569254
_*Facebook @Zauren Sunnah*_
https://www.facebook.com/groups/552998655501583/
*اللهم لا تواخذنى بما نقولوا واجعلنى خيرا مما نظنون. فقلت ما قلت. إن تك حسنة فمن الله وإن تك سيئة فمن نفسك والشيطان. وسبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا اله إلا أنت. وأستغفر الله
لى ولكم ولسائر جميع المسلمين من كل ذنب و استغفر وه إنه هو البرو الوبركاته
*والسلام عليكم ورحمة الله وبركاته*