MURNAR MUTUWA MURNAR BANZA


MURNAR MUTUWA MURNAR BANZA

BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

Assalamu Alaikum warahamatullah Wabarakatuhu.

A cikin 'yan kwanakin nan da mu ke ciki, musamman da ga jiya zuwa yau na fahimci cewa akwai wasu tsirarun mutane da su ke cikin wani irin hali na shauƙi, annashuwa da kuma jin daɗi saboda labari ya isar mu su cewa wasu manyan mutane sun kamu da wannan cuta ta COVID19.

A zahirin gaskiya, yana ɗaukar dabba mafi girman daraja a cikin dabbobi marasa hankali kafin ta yi wa 'yar uwarta dariyar murnar ta kamu da cutar da za ta iya zama ajalinta, ko kuma saboda ta shiga wani hali da zai iya kai ta zuwa ga hakan. Kenan hakan yana ɗaukar mafi girma daga cikin jahilan mutane kafin a ce ya ma bar irin wannan tunanin ya shige shi ballantana ma har ya kai ga bayyana shi a fili. Shin kai da kake murna ta kama waɗancan mutane, tsakani da Allah menene abun murnar? Shin kana tunanin ka fi ƙarfin ta kama ka ne? Ko kana ganin cewa in sun mutu kai za ka tsaya gadin duniyar ne? Shin ko ka san cewa kana iya mutuwa su su rayu? Ka sani ko Allah ya warkar da su kai kuma ya jarrabe ka da cutar?

Gaskiya ya kamata mutane mu shiga taityinmu fa, ace annoba irin wannan wacce ta girgiza duniya baki É—aya ta samu wani wanda ka sani ko kuma yake shugabanka kuma wai ka koma gefe kana dariya? Murnar mutuwa dai murnar banza ce tunda kowa sai ya tafi.

Ya Allah ka tsare mu daga wannan bala’i, ya Allah ka kawo mana sauÆ™in al'amarin, ya Allah kar ka kama mu da laifin wayayen cikin mu, ya Allah ka kawo mana Æ™arshen wannan musiba. Amin.

➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖
Subhanak Allahumma Wabi Hamdika Ash Hadu Anla Ila Ha Illah Anta Astagfiruka Wa Atubu Ilaika. 

•----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman
•----------•✬(✪)✬•----------

    +23481858191
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Twitter: @jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Instagram: Jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Facebook
https://m.facebook.com/JamiluWriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Tumblr: Jamiluwrite
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Bakandamiya: Jamilu Abdurrahman
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Telegram: https://t.me/Jamiluwrite
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
LinkedIn: https://www.linkedin.com/in/jamilu-abdurrahman-36b88211
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Haimanraees@gmail.co
──────⊹⊱✫⊰⊹──────m─8─r─ ─r─/:─ ─ ─76•  
Post a Comment (0)