SHARHIN FIM ƊIN BUNNY
Bunny fim ɗin faɗa ne da aka fitar a India cikin harshen Telugu a shekara ta 2005. Shirin, wanda shi ne fim na uku da jarumi Allu Arjun ya yi bayan Gangotri da Arya ya samu karɓuwa matuƙa.
An fassara wannan shiri da harshen Oriya inda aka sa masa suna Dharmayuddha, da yaren Hindi kuma Bunny The Hero, da Malayalam kuma aka bar shi da sunan shi. Da aka maimaita shi da harshen Bengali kuma sai aka sa masa suna Challenge. Hakanan kuma an fassara wannan shiri zuwa harshen Hausa in da aka sa masa suna Cinnaka, kuma wannan shi ne fim na biyu da na fara ɗaura muryata domin yin fassara. Kuma daga wannan fim ne jarumi Allu Arjun ya samu laƙabin Bunny.
Umurni: V. V. Vinayak
Ɗaukar Nauyi: M. Satyanarayana Reddy
Rubutawa: V. V. Vinayak
Sauti: Devi Sri Prasad
Mai horaswa: Chota K. Naidu
Tacewa: Gowtham Raju
Ranar fita: 6 April 2005
Tsawon Shiri: Mintuna 139
Harshe: Telugu
Kasafi: ₹15 crore (US$2.1 million)
Kasuwanci: ₹35.5 crore (US$5.0 million)(Share) 100 Days.
LABARIN SHIRIN
Somaraju hamshaƙin ɗan kasuwa ne da ke zaune a Visakhapatnam, yana da wani ɗan uwa mai suna Mysamma wanda shi ne ya ke jagorantar harkokin kasuwancin sa a Hyderabad. Somaraju yana da wata kyakkyawar 'ya da yake matuƙar so mai suna Mahalakshmi.
Bunny wanda aka fi sani da Raja ya samu damar shiga kwalejin da da Mahalakshmi ta ke karatu in da ya samu nasarar burge ta tun a ranar farko. A hankali dai har ta faɗa kogin soyayyarsa. Somaraju bai so hakan ba, amma da ga ƙarshe dai ya amince da auren su. Kasancewar a al'adar su mata ne ke biyan sadaki, sai Raja ya ce shi dukiyar Somaraju ya ke so gaba ɗaya a matsayin sadakin. Da ga nan ne fa sai aka fara bayyanawa mai kallo dalilin da ya sa Raja ya ke so ya amshe wa Somaraju dukiya.
Mahaifin Raja wani mutum ne mai suna Ranga Rao Bhupathi Raja kuma ɗan uwan Somaraju ne ta ɓangaren uwa, a taƙaice ma dai kawun Mahalakshmi ne. Bhupathi Raja babban mutum ne da yake da filaye masu yawa da kadarori, bugu da ƙari yana da mutane sosai kuma yana da ƙafa a gwamnati. Yayin da a ka haifi Mahalakshmi, sai mahaifiyarta ta buƙaci Bhupathi da ya zo domin ya raɗa wa yarinyar suna da sauran al'adun da akan yi a biki irin wannan. A hanyarsa ta zuwa taron ne Somaraju da wasu 'yan daba su ka kai masa farmaki su ka raunata shi har kowa ya yi tsammanin ya mutu. Amma Bhupathi bai mutu ba har sai da ya raɗa wa yarinyar da aka haifa suna Mahalakshmi, ba a jima ba da yin hakan ya faɗi ya mutu ba tare da ya faɗa wa kowa abinda ke faruwa ba.
Raja sai ya fahimci hakan da ga baya bayan mariƙinsa wato Rangaswamy ya bayyana masa cewa ba shi bane mahaifinsa na gaskiya. A ƙoƙarin ceton Raja ne ma suka sadaukar da ɗan su domin shi ya rayu. A ƙarshe dai, domin ƙwato haƙƙinsa, Raja ya gwabza da Mysamma kuma ya auri yarinyar.
JARUMAN SHIRIN DA MATSAYIN SU
Allu Arjun - Bunny/Raja
Gowri Munjal - Mahalakshmi
Prakash Raj - Somaraju
Sarath Kumar - Ranga Rao Bhupathi Raja
Mukesh Rishi - Mysamma
Raghu Babu -
Sharat Saxena - Rangaswamy
Sudha - Matar Rangaswamy
Seetha -
Ahuti Prasad - DCP Venkhayya
Rajan P. Dev - Chief Minister Gudumba Chatti
Chalapathi Rao -
M.S. Narayana Daiva Sahayam
Venu Madhav -
Fish Venkat -
Jenny - Lecturer
L. B. Sriram - Doctor
Chitram Seenu - Abokin Bunny
Dil Ramesh -
Sravan - Tarun
WAƘOƘIN SHIRIN
1. "Maro Maro"
2. "Jabilammavo"
3. "Va Va Vareva"
4. "Mayilu Mayilu"
5. "Kana Padaleda"
6. "Bunny Bunny"
<••••••••••••••••••••••••••••>
Haiman Raees
<••••••••••••••••••••••••••••>
08185819176
Twitter: @HaimanRaees
Instagram: Haimanraees
Facebook: Haiman Raees
Haimanraees@gmail.com
Miyan Bhai Ki Daring