WAI KE SAI YAUSHE ZA KI YI AURE NE?


*WAI KE SAI YAUSHE ZA KI YI AURE?!*
.

Kuskure ne ka yi wa budurwa irin wannan tambayar, da yawan Maza ko wasu matan auren sai ka ga da zarar sun ga wata wadda ta kai minzalin aure sai su dinga muzguna mata da tambayoyi irin wannan, gaskiya wannan abu yana matuqar yi masu zafi, kuma babu wani fa'ida sam-sam a cikin wannan tambayar, domin kodai ka cusa mata baqin ciki har ta fara zargin kanta sanadiyar rashin yin auren, ko kuma ta fara munanta zato ga Ubangiji wanda Shi ke qaddara komai, idan kuma qin yin auren daga ita ne, to fa maganarka ba za ta sa ta gyara ba. 

Ya kamata duk mai tunani ya gane, duk wata budurwa da ta kai matakin yin aure, to fa ta fi kowa son ta gan ta a gidan mijinta, amma ba ta da wani wayau ko dabara face abin da Allah Ya zartas mata, komai da lokacinsa, wani a gaggauta masa wani kuma a jinkirta masa, Allah Ya kan jinkirta wa mutum wani al'amari don za6a masa mafi alkhairinsa, shin ba ku da labarin waďanda za ku ga sun yi auren amma sun rasa samun farin ciki? Wasu kuma da zarar an yi auren sai ku ji an rabu? Shin ina amfanin hakan? Haqiqa duk wani abu da zai faru ga mutum an riga an rubuta masa shi, wasu mazan da matan Allah Ya kan jarabce su da jinkirin auren ne don hakan ya zama jarabawa a gare su, haqiqa duk wadda ta yi hakuri za ta gamu da babban rabo daga Ubangijinta duniya da lahira, Allah Zai wadata ta kuma Ya iya halarto mata da miji wanda ko a mafarkinta ba ta ta6a ganin irin shi ba, irin wanda tunaninta bai ta6a kai wa gare shi ba. Amma duk wadda ta bijire har ta kai ga ta fara zuwa wajen malaman zaure (bokaye) don su nema mata mafita, to haqiqa ta yi 6ata 6ata mai girma, kuma ta gaggauta tuba da neman gafarar Ubangijinta, haka kuma wajibi ne ta kame kanta daga dukkan ayyukan alfasha irin su zina, maďigo, istimna'i (masturbation) da sauransu.
.

Babban abin da ya dace ka furtawa mace budurwa shi ne ka yi mata addu'ar samun miji nagari, tare da yi mata nasiha da ta ji tsoron Allah ta kiyaye dokokinsa, kuma ta fita harkar samari waďanda za su zo wajenta ba da nufin aure ba sai don cin ma burinsu, kodai su 6ata mata lokaci ko kuma su gur6ata mata rayuwa, su zubar mata da kimarta da darajar iyayenta kuma su shafe mutuncin gidansu tare da barin abin gorantawa ga danginta. Ya Allah Ka qara shiryar da mu. 
.

Sannan su ma matan su ji tsoron Allah kada su biye wa soye-soyen zukatansu, 'yar uwa shi aure ibadah ne, don haka dole ne ki bi koyarwar addini a yayin za6en mijin aure, miji mai addini da kyawawan ďabi'u shi ne za6in da Allah da ManzonSa suka yi maki, kada ki biye wa kyale-kyalen duniya ko kyawun surar namiji, wannan duk yaudarar kai ne. 
.

Ki kasance mai kiyaye dokokin Allah, ki lizimci azumi da sadaqa, kuma ki zama mai tashi cikin dare don yin ibadah tare da kai kukanki ga Mahaliccinki, kasance mai neman shawara da addu'ar bayin Allah nagari, kada ki zartas da komai face sai kin yi istikhara don neman za6in Allah Gwanin ilimi da hikima, sannan a koda yaushe ki dinga burin cewa Allah Yana yi maki babban tanadi kuma Yana sane da halin da baiwarsa take ciki, babu wadda za ta yi haka face ta samu mafi alkhairin abin ta take so in shā Allah, amma kada mu mance da alqawarin da Allah Ya yi na zai jarabce mu da fitintinu kala-kala, haqiqa duk wadda ta yi hakuri ita ce mai rabo. 
.

Ki zama mace soliha mai tsoron Allah, sai Ubangiji Ya kawo maki irinki wanda zai kula da ke kuma ya kula da addininki, kuma ba zai wulaqanta ki ba, domin Allah Ya ce su mazan kwarai na matan kwarai ne. Amma duk wanda ya aure ki don kyawunki ko wani abin duniya, to fa za ki hadu da wulaqanci da qasqanci kala-kala. Bahaushe dai ya ce: In da kwaďayi da wulaqanci!
.

Sannan iyaye su ma su ji tsoron Allah su dinga aurar da yaransu idan sun kai lokaci, ku sani cewa duk laifin da yaranku suka yi, to fa ku kuma kuna da zunubi kwatankwacin nata. Allah Ya kiyaye. 
.

Allah muke roko Ya shiryar da mu Ya sa mu fi qarfin zukatanmu, kuma Ya haďa mu da masu son mu domin Sa. Allah Ya datar mu. 
.


*✍🏾Ayyub Musa Jebi Giwa.*
*(Abul Husnain).*

Daga Zauren 
*🕌Islamic Post WhatsApp.*

Ana iya turo da cikakken suna da address zuwa wannan number *+2348166650256* don shiga Zauren Islamic Post.
Post a Comment (0)