BUƊAƊƊIYAR WASIƘA GA KE DA SHI


*BUƊAƊƊIYAR WASIƘA GA KE DA SHI.*
.

Daga *Ayyub Musa Jebi*
*(Abul Husnain).*
.

Abin fa ya girmama, kowa na son nashi ya taso cikin nagarta, amma ba ya lura da lalacewar na wasu. 

'Ya'ya ni'imace ga dukkan wanda Allah Ya azurta shi da su, wannan ya sa dayawa ake kokari don ganin mutum ya togace 'ya'yansa daga fitintinun wannan qarni. 

Daga cikin fitinun wannan zamani akwai yawaitar ZINACE-ZINACE a cikin al'umma, wanda yanzu ya zama ruwan dare, tsakanin Malami da ďaliba, ďalibi da ďaliba, Tsoho da yarinya, saurayi da budurwa, kai har a tsakanin muharramai. Wal iyādzu bil Lāh.

Muna mance cewa; Mafi girman hanyar da za ka bi don tarbiyyar yaranka, shi ne ka kyautata quruciyarka, kuma ka auro masu uwa soliha. (Wannan shi ne abin da har yanzu muka kasa kiyayewa). 

Zina bashi ce, duk wanda ya ďauke shi dole sai ya biya. *Addini, al'ada* da abin da suka bayyana mana a zahiri sun tabbatar mana da cewa *zina* wata aba ce wadda take bin jini, kamar yadda yaro kan biyo mahaifinsa a tsawo, hasken fata ko gajarta, haka ita ma zina take bin mutum har cikin zuriyarsa. 

Yayin da ka yi zina da 'yar wani a 6oye, da yiyuwar wata rana a yi da taka a fili, idan ka yi amfani da kuďi wajen keta haddin 'yar wani, da yiyuwar wata rana taka a yi da ita a kyauta, idan ka ja wa iyaye zubar da cikin da ka yi wa 'yarsu, mai yiyuwa kai taka a gidanka za ta haife maka shi. Haka abubuwan ke faruwa, muna ji kuma muna gani. *Zina bashi ce!*

Dan uwa ba ka da wani wayau ko dabara da za ka iya yi don hana faruwar abin da Allah Ya zartas, don haka mafita kawai shi ne ka yi wa Allah da ManzonSa ďa'a, sai ka yi rayuwa cikin farin ciki. 

Zina qazanta ne, babu mai yin ta sai qazami, ta hanyar zina ana kamuwa da cututtuka masu wahalar magani, ta hanyar zina ne ake samun cikin shege, da yawan 'yan matan yanzu suna ganin cewa ba wani abu bane don sun yi zina domin akwai magungunan hana ďaukar ciki, sun mance cewa babu wanda ya isa ya hana faruwar abin da Allah Ya rubuta faruwarsa, bil Lāhi! Duk maniyyin da Allah Ya qadarta zai rayu, to babu wani hanya ko magani da za a sha don hana zuwansa duniya.

A binciken da wata jami'ar amurka (University of Seattle USA) ta fitar a shekarun da suka gabata, sun tabbatar da cewa a duk lokacin da mace ta sadu da wani namiji, daga lokacin da maniyyinsa ya shiga jikinta, to akwai waďansu kwayoyin ďabi'a da ake kira DNA (Deoxyribonucleic acid) daga jikin shi da za su zauna a jikinta din-din, domin a lokacin da kwayar maniyyi (sperm cell) ya bugi mahaifarta, shi kuma zai saje da tsokar jikinta ne, kuma dama shi DNA rayayye ne ba ya mutuwa, wannan ke tabbatar da cewa akwai yiyuwar mace ta kwashi ďabi'un wanda ta yi zina da shi, kuma waďannan ďabi'un za su iya gangaro wa har zuwa abin da za ta hayayyafa, shiyasa musulunci ya umarce mu da auren mace tagari, domin idan ka auro mara nagarta, to fa rashin nagartarta zai iya shafar yaranka, haka kema idan kika auri mara ďabi'u masu kyau, akwai yiyuwar ku yi ta haihuwan 'ya'ya marasa tarbiyya koda kuwa kuna kokarin ba su tarbiyya.  

Zina tana raunata jiki, mafi girman muninta shi ne tana jawo wa mutum fushin Ubangiji, babu wanda zai yi zina face sai an cire imani daga jikinsa, to ya kake tunani idan Allah Ya amshi rayuwarka a wannan hali, a tunaninka za ka rabauta idan ka tashi a lahira babu ďigon imani a tare da kai?

Don haka, mu ji tsoron Allah, mu kiyaye al'aurar mu. Allah Ta'āla Ya shiryar da mu. 

Wassalamu alaikum Warahmatullah. 
.

*🕌Islamic Post WhatsApp.*
*08166650256.*
.

https://m.facebook.com/ayyubmusa133/
Post a Comment (0)