WASU MUGAYEN ƊABI'U DA YA KAMATA MATA SU KAUCE MUSU


Wasu Mugayen Dabi'un Da Ya Kamata Mata Su Kaucewa Yinsu:

Wani matsalar da akasarin mu mata muke fiskanta a lokuta da dama shine na rashin sanin yadda ya kamata mu zauna da mazajenmu, duk da yake wasu lokutan muna sane muke yin abunda muke domin cusgunawa mazajen namu.

Sau tari matan suka ingiza mazansu cikin kuncin da suke ciki a maimakon kokarin fiddasu. Haka kuma mata kanyi sanadiyar jawowa mazajensu matsala a wuraren aiyukansu kokuma a harkar kasuwancinsu.

Da akwai wasu lokuta mahimmai ga mata a wurin mazajensu da matan aure da damar gaske basu da masiyat mahimmancin wadannan lokutan a wajensu, don haka maimakon suyi amfani da wadannan lokatan wajen kwantarwa mazajensu hankula, sai kuma suyi abunda zai jawo bacin rai a garesu dama mazajen nasu.

Irin wadannan lokutan na tarairayan maza, mata sun maidasu ba a bakin komai suke ba, wasu matan ma basu san amfani ko kuma yadda zasu tafiyar da mazajensu a irin wadannan lokutan ba.

Da akwai lokutan da namiji baya bukatar yaji wani abu da zai tayar masa da hankali, da akwai lokacin da maigida yake bukatar jin labarin da zai farar ta masa rai, da kuma lokacin da yake son jin wata gulma daga gareki. Haka kuma maza suna da lokutan da suke bukatar jin mace tana musu hirar soyayya. Mata nawa ne sukasan irin wadannan lokutan kuma suke amfani da su yadda ya kamata?

Bari mu dauki lokacin da miji ya dawo gida bayan ya kammala kujuba-kujubansa na yau da kullum, a lokacin da ya dawo gida domin ya huta ko ya ci a binci. A irin wannan lokacin ya zamewa mace dole tayi la'akarin da wace irin siga mijin ya shigo gidan domin sanin yadda zaki tinkareshi da kuma irin hirar da ya kamata kiyi masa a wannan lokacin.

Kada ki sake ki baiwa mijinki labari mara dadi a lokacin daya sanya abnci a gaba zai ci, yin hakan zai iya hanashi cin abincin yadda ya kamata, bacin ran labarin kuma ya dantanta ne da kwatankwaci girman labarin, misali idan labari ne wanda ya shafi rashi rai kona dukiya labarine da zai iya sanya miji ya stame hannu daga abincin daya ke ci. Irin wannan halin na baiwa mazaje labari mara dadi a lokacin ma mai gida ya zauna cin abinci mu daukeshi tamkar wata ibada a garemu.
 http://sirinrikemiji.blogspot.com/2018/07/wasu-mugayen-dabi-da-ya-kamata-mata-su.html#.XkP0PcP1ud8.whatsapp
Post a Comment (0)