ZUWA GA 'YAR UWA TA


*Zuwa ga 'Yar uwata 🧕🏾*

Haqiqa Allah Maďaukakin Sarki Shi ne Mai azurta bayinsa a dukkan lokacin da Ya so, kuma idan Ya ga dama sai Ya amshi abin sa a dukkan lokacin da Ya so. 

◽Wasu an haife su a gida ko a dangi na talakawa, amma sai Allah Ya azurta su kuma Ya ďaukaka darajarsu. 

◽Wasu kuwa sun fito daga manyan gida, ko sun yi tashen dukiya da ababen duniya, amma lokaci guda Allah Ya amshi dukiyarsa su ka koma marasa komai kuma sunansu ya shuďe a tarihi. 
.

To 'yar uwa idan har kin yi imani cewa Allah Shi ke da arziki da talauci, to me zai sa ki damu kanki ko ki qaqaba wa zuciyarki cewa dole sai mai kuďi za ki aura?! Ba ki tunanin cewa koda kin samu mai kuďin Allah Zai iya talauta shi? Ba ki tunanin ki faďa hanun azzalumi mara addini da kyawawan halaye? 

Lallai dai yana da kyau ki zauna ki sake tunani, domin shi aure ibadah ne ba kasuwanci ba, idan mutum ya zo neman aurenki, to abin da ake so ki duba shi ne addininsa da kyawawan ďabi'unsa, kuma ya kasance yana da sana'a ko aikin yi wanda zai iya riqe ki. 

Mu cire son zuciya sai mu rabauta. Allah Ya sa mu dace. 
.


*✍🏾Ayyub Musa Jebi Giwa.*
*(Abul Husnain).*
*08166650256.*
Post a Comment (0)